Ruwa Ya Yi Gyara: Gidaje Sama da 70 Sun Yi Fata Fata a Filato
- Mazauna jihar Filato sun shiga tsaka mai wuya bayan an samu mamakon ruwa da iska da ya ɗaiɗaita gidaje sama da 70
- Lamarin, wanda ya afku a karamar hukumar Langtang ta Kudu ya jefa jama'a a a cikin ruɗani yayin da kwanon gidaje suka rika ɗaye wa
- Nanbol Nanzing, mazaunin ɗaya daga cikin yankunan da abin ya shafa, ya nemi gwamnatin jihar ta duba halin da su ka shiga
- Shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Nanfa Nbin, ya tabbatar da cewa kwamiti na kula da gaggawa ya ziyarci iyalan da iftila'in ya shafa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Plateau – Aƙalla gidaje da rumbunan abinci sama da 70 sun lalace sakamakon mamakin ruwan sama a jihar Filato.

Kara karanta wannan
A karon farko, gwamna Fubara ya fadi halin da ya shiga bayan dokar ta baci a Ribas
Rahotanni sun ce guguwar ruwan saman ta afkawa wasu yankuna a ƙaramar hukumar Langtang ta Kudu da ke Jihar Plateau.

Asali: Twitter
The Nation ta ruwaito cewa guguwar, wacce ta biyo bayan ruwan sama a ranar Laraba, 2 ga watan Afrilu, 2025, ta kiɗima jama'a.
Rahoton ya ci gaba da cewa iskar ta yi sanadiyyar ruɗani da gagarumar asarar dukiyoyin mutane da dama a yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gine-gine sun fadi a jihar Filato
Daily Post ta wallafa cewa guguwar ya tare da ruwan sama sun lalata gidaje da dama, inda sama da 70 na su suka rasa rufin su, kuma wasu gine-gine sun fadi. Nanbol Nanzing, wani mazaunin ƙauyen, da iftila'in ya aikawa ya nemi gwamnatin jihar ta tallafa, yana mai cewa al’ummomin da lamarin ya shafa suna cikin mawuyacin hali. Shugaban ƙaramar hukumar Langtang South, Hon. Nanfa Nbin, ya tabbatar da aukuwar lamarin a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara, Mr. Iliya Bako, ya fitar.
Ana kula da iftila'in Filato
Hon. Nanfa Nbin ya kuma bayyana cewa, kwamiti na musamman na ƙaramar hukumar ya ziyarci yankunan da guguwar ta shafa don tallafa wa jama'a.

Asali: Facebook
A cewar sanarwar, kungiyar kula da gaggawa ta gudanar da aikin ba da taimako ga iyalan da aka shafa, tare da ba su shawarwari da kuma hanyoyin samun tallafi daga hukumomin jin kai.
Yadda ake samun ambaliya a Filato
Yankin Langtang ya saba fuskantar iftila'in ambaliya, domin ko a damunar da ta gabata, akalla gidaje 80 ne suka lalace sakamakon ambaliyar ruwa a yankin .
Ambaliyar ruwan ta biyo bayan mamakon ruwan sama da aka sha a yankin na tsawon kwanaki uku daga Juma'a zuwa Lahadi, wanda ya haifar da barna mai yawa.
Filato: An kashe jama'a a kauye
A baya, kun ji cewa yan bindiga sun kai hari garin Ruwi da ke ƙaramar hukumar Bokkos a jihar Filato, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 10 da jikkatar wasu uku.
Wani mazaunin yankin da bai so a ambaci sunansa ya ce, 'yan bindigar sun bude wuta kan mutanen da ke gudanar da taron makoki, wanda ya jawo asarar rayuka.
Asali: Legit.ng