Ba a Gama Rigimar Sarautar Kano ba, Gwamna Radda Ya Sha Alwashi kan Masarautun Katsina

Ba a Gama Rigimar Sarautar Kano ba, Gwamna Radda Ya Sha Alwashi kan Masarautun Katsina

  • Mai girma gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, ya nuna muhimmanci da tarihin da masarautun jihar suke da su
  • Gwamnan ya nuna aniyar gwamnatinsa ta kare al'adu da mutuncin masarautun Katsina waɗanda suke da daɗaɗɗen tarihi
  • Dikko Radda ya bayyana hakan ne a wajen Hawan Magajiya da aka gudanar a masarautar Daura da ya samu halartar manyan baƙi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya yi magana kan masarautun jihar masu daɗaɗɗen tarihi.

Gwamna Radda ya addada aniyar gwamnatinsa na kare al’adu da mutuncin masarautun jihar.

Gwamna Dikko Umaru Radda
Gwamna Radda ya sha alwashin kare mutuncin masarautun Katsina Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin sanarwar da sakataren yaɗa labaransa, Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce gwamnan ya yi wannan jawabin a lokacin bikin nuna al'adun gargajiya na Hawan Magajiya da aka gudanar a Masarautar Daura.

Kara karanta wannan

Iyalai da abokan mafarautan da aka kashe a Edo sun yi maganar daukar fansa

Gwamna Radda zai kare mutuncin masarautu

A cikin jawabinsa, Gwamna Radda ya bayyana mahimmancin tarihin Daura a matsayin tsohuwar masarauta mafi daɗewa a Najeriya da kuma zamanta wani muhimmin ɓangare na al’adun ƙasar nan.

“Labarin Daura shi ne labarin Najeriya. Katangunta masu tarihi, bukukuwanta masu armashi, da hikimar mutanenta suna tunatar da mu su waye mu."
"Yayin da muka taru don Hawan Magajiya, mu tuna cewa al’ada ita ce ruhin ci gaba."

- Gwamna Dikko Radda

Gwamna Radda ya yi alƙawarin ci gaba da ƙoƙari don kare waɗannan al'adu na gado.

Ya kuma buƙaci haɗin kai da mutunta juna a tsakanin shugabanni da jama'ar da suke jagoranta.

"Za mu kare darajar masarautunmu, mu kula da al’adarmu, kuma mu tabbatar da cewa ci gaban da muka samu ya ɗore. Ba za mu ja da baya ba. Za mu ƙara karfi, tare.”
"Zaman lafiya ba ya zuwa haka kawai. Yana zuwa ne idan shugabanni sun yi shugabanci da adalci, kuma idan jama’a sun tsaya tsayin daka tare da shugabanninsu.

Kara karanta wannan

Ta tabbata Atiku Abubakar ya fice daga jam'iyyar PDP? An samu bayanai

Don haka, ina roƙonku, mutanena, ku tallafawa shugabanninku."

- Gwamna Dikko Radda

Jakadun ƙasashen wajen sun yaba da bikin sallah

A yayin bikin, jakadiyar ƙasar Finland a Najeriya, Sandra Selin, ta bayyana wannan bikin a matsayin abin burgewa wanda ya samu tsari mai kyau.

Gwamna Dikko Radda
Gwamna Radda tare da manyan baki a wajen Hawan Magajiya a Daura Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

Ta kuma godewa Gwamna Radda saboda kyakkyawan tarbar da suka samu da kuma damar da ta samu don koyon al’adun jihar kai tsaye.

Haka kuma, jakadan ƙasar Bulgaria a Najeriya, Yanko Yornadov, ya bayyana cewa:

"Muna da kyakkyawan ra’ayi matuƙa kan jihar Katsina. Na yi farin ciki matula ganin cewa abokan aikina da dama sun zo tare da ni domin ganin bikin al’adar Daura, wani gagarumim bikin tunawa da al'adun gado na wannan yanki."

Ƙuduri ne mai kyau

Ibrahim Kabir ya shaidawa Legit Hausa cewa niyyar gwamnan kan masarautun Katsina abun a yaba ne.

"Tabbas wannan abu ne mai kyau domin masarautunmu abubuwan alfahari ne a wajenmu."

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito fili: Dalilin Shugaba Tinubu na korar Mele Kyari daga NNPCL

"Yana da kyau a kare martabarsu da darajarsu. Muna goyon bayansa kan wannan kyakkyawan ƙudurin da yake da shi."

- Ibrahim Kabir

Gwamna Radda ya raba tallafi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Mai girma gwamnan atsina, Dikko Umaru Radda, ya raba tallafi ga zawarawa a faɗin jihar.

Gwamna Dikko Radda ya raba tallafin ne na kuɗi da kayan abinci ga zawarawa da matasa marasa galihu domin rage musu radaɗin da ake fama da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng