Ana cikin Dambarwar Natasha, Tsohon Sanata Ya Yi Sababbin Zarge Zarge kan Akpabio

Ana cikin Dambarwar Natasha, Tsohon Sanata Ya Yi Sababbin Zarge Zarge kan Akpabio

  • Elisha Abbo ya fito ya yi magana kan yadda Godswill Akpabio ya ƙullace shi saboda ya ƙi goya masa baya ya zama shugaban majalisar dattawa
  • Tsohon sanatan mai wakiltar Adamawa ta Arewa ya zargi Akpabio da hana a biya shi albashinsa na ƙarshe bayan an kore shi daga majalisa
  • Ya nuna cewa Akpabio ya sanar masa da cewa za a kori sanatoci biyar daga majalisa, kuma dukkaninsu sai da aka raba su da kujerunsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon sanatan Adamawa ta Arewa, Sanata Elisha Abbo, ya yi magana kan yadda Godswill Akpabio ya takura masa saboda bai goyi bayansa ba.

Sanata Elisha Abbo ya bayyana cewa Akpabio ya nemi ya goya masa baya domin zama shugaban majalisar dattawa, amma sai ya nuna masa yana tare da Abdul'aziz Yari.

Kara karanta wannan

Sanata: "Akpabio ya buɗe kofar kashe Natasha, kuma ba za a iya cire ta a majalisa ba"

Elisha Abbo ya zargi Akpabio
Elisha Abbo ya ce Akpabio ya takura masa Hoto: Senator Elisha Abbo, Godswill Obot Akpabio
Asali: Facebook

Sanata Elisha Abbo ya zargi Akpabio

Sanata Elisha Abbo ya bayyana hakan ne yayin wata hira da tashar Arise News a shirinsu na Prime Time.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon sanatan ya bayyana cewa shugaban majalisar dattawan ya sanar masa da cewa za a kori sanatoci biyar daga majalisa.

Ya ƙara da cewa kuma wannan maganar da Akpabio ya yi sai da ta tabbata domin dukkan sanatocin sai da suka bar majalisa, ciki har da shi.

Sanata Abbo ya bayyana cewa Akpabio ya ƙullace shi a zuciya saboda ya ƙi goya masa baya, wanda hakan ya sanya ya muzguna masa a majalisa.

Elisha Abbo ya ce Akpabio ya takura masa

Ya yi zargin cewa ya taɓa wakiltar majalisar dattawa wajen wani taro a Kenya, ya yi amfani da kuɗinsa, amma da ya buƙaci a biya shi, sai Akpabio ya hana.

Ya ƙara da cewa motocinsa na hawa da aka siyawa dukkanin sanatoci Akpabio ya ƙi mayar masa da su bayan an kore shi daga majalisa.

Kara karanta wannan

Yadda ɗan Sokoto ya yi ridda ya sake dawowa Musulunci bayan Sanata ya tsoma baki

Sanata Elisha Abbo
Sanata Elisha Abbo ya yi zarge-zarge kan Akpabio Hoto: Senator Elisha Abbo
Asali: Twitter

Tsohon sanatan ya nuna cewa har albashinsa na ƙarshe Akpabio bai bari an biya shi ba bayan kotu ta kore shi daga majalisa.

"Albashina na wannan watan, an cire ni a ranar 19 ga wata, bisa ga dokar gwamnatin tarayya indai mutum ya kai 15 ga wata za a biya shi albashinsa. Ba a biya ni albashi na ba na wannan watan bisa ga umarnin Akpabio."
"Bari na gaya maka wani mummunan abu da ya yi, akwai sanatoci 109, an kori biyar daga cikinmu, biyu sun tafi domin zama ministoci, Umahi da Geidam, wanda hakan ya sanya sanatoci bakwai suka bar majalisa."
"Daga cikin sanatoci bakwai da suka bar majalisa, Akpabio ya aika musu da motocinsu har gida. Daga cikin sanatoci huɗu da aka kora, duk sun samu motocinsu, Sanata Abbo ne kawai aka hana."
"Sun ƙi bani nawa motocin saboda na ƙalubalanci Akpabio."

-.Sanata Elisha Abbo

Natasha ta sake nuna yatsa ga Akpabio

Kara karanta wannan

Gwamnan Edo ya gana da Barau kan kisan Hausawa, ya fadi shirinsa kan iyalan mamatan

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan ta zargi shugaban majalisar dattawa da hannu a shirin yi mata kiranye.

Sanata Natasha ta zargi Godswill Akpabio da haɗa baki da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello,.domin ganin an raba ta da kujerarta a majalisa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel