Bankin CBN Ya Kirkiro Sababbin Takardun Kudi na N5,000 da N10,000? An Samu Bayani

Bankin CBN Ya Kirkiro Sababbin Takardun Kudi na N5,000 da N10,000? An Samu Bayani

  • Babban banki ƙasa watau CBN ya musanta jita-jitar da ake yaɗawa cewa yana shirin ƙirƙiro takardun N5,000 da N10,000
  • CBN ya bayyana cewa wannan rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta ƙatya ne, ba shi da tushe ballantana makama
  • Ana ta yaɗa cewa Najeriya za ta fara amfani da sababbin takardun kuɗi na N5,000 da N10,000, lamarin da CBN ya ce kanzon kurege ne

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Babban Bankin Najeriya (CBN) ya karyata rahoton da ake yaɗawa cewa ya na shirin ƙirƙiro sababbin takardun kuɗi na N5,000 da N10,000.

Rahoton da ke yawo a kafafen aadarwa ya nuna cewa CBN zai samar da ƙarin takardun kuɗin ne domin saukaka hada-hadar kuɗi a ƙasar nan.

Bankin CBN.
CBN ya karyata jita-jitar fitar da sababbin takardun kuɗi na N5,000 da N10,000 Hoto: @CentBank
Asali: Facebook

Amma a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba, bankin ya ƙaryata wannan raɗe-raɗi da ya kira mara tuahe balle makama.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya caccaki Tinubu, ya fadi sauyin da zai kawo da shi ne shugaban kasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da gaske CBN zai kirkiro N5,000 da N10,000?

CBN ya bayyana labarin a matsayin ƙarya tare da bukatar ‘yan Najeriya su yi watsi da shi gaba ɗaya.

“Wannan bayani ba daga Babban Bankin Najeriya ya fito ba. Muna tunatar da al'umma cewa shafin yanar gizo na CBN shi ne cbn.gov.ng,” in ji sanarwar.

A wani karin bayani daga sashen hulɗa da jama’a na bankin, an sake nanata cewa CBN ba ya fitar da sanarwa a ko ina sai sahihan shafinsa na kafafen sada zumunta da na yanar gizo.

“Kafofin da muke fitar da sanarwa daga CBN su ne shafin yanar gizo ko kuma bayanai daga sashen mu na hulɗa da jama'a. Babu wani mataimakin gwamnan CBN mai suna Ibrahim Tahir Jr.”

Raɗe-raɗin da ake yaɗawa kan takardun kudi

Rahoton ya yi ikirarin cewa an fitar da sababbin N5,000 da N10,000 ne domin rage fama da takardun kudi da samar da hanya mai sauƙi ga ‘yan Najeriya wajen yin manyan cinikai.

Kara karanta wannan

"Hantar Tinubu ta kaɗa": An faɗi wanda ya dace Atiku, Obi da El Rufai su marawa baya a 2027

Har ila yau, jita-jitar ta ce sababbin takardun za su ƙunshi hoton Cif Obafemi Awolowo a kan N5,000 da Dr. Nnamdi Azikiwe a kan N10,000 don girmama rawar da suka taka wajen ci gaban Najeriya.

Na'urar cire kudi.
CBN ya karyata batun kirkiro sababbin takardun Naira na N5,000 da N10,000 Hoto: Getty Image
Asali: Getty Images

Kazalika, an ce sababbin takardun kuɗin za su zo da tsarin tsaro kamar launin tawada mai canzawa da fasahar da ke hana jabun takardu.

Jita-jitar ta kara da cewa za a buga sababbin takardun kuɗin su fara shiga hannin ƴan Najeriya daga ranar 1 ga Mayu, 2025.

Bankin CBN ya fito ya yi bayani

Bugu da ƙari, an ce bankunan kasuwanci za su fara bayar da su ta na'urar ATM da kuma kan kanta a farkon watan Mayu.

Bankin CBN ya nanata cewa wannan bayani ba gaskiya ba ne, kuma yana binciken tushen labarin don daukar matakan da suka dace.

CBN ya naɗa sababbin daraktoci 16

A baya, kun ji cewa bankin CBN ya naɗa sababbin daraktoci 16 domin su ja ragamar ayyukansa a ɓangarori daban-daban.

Sababbin darektocin da aka nada sun hada da Jide-Samuel Avbasowamen a matsayin darektan sashen fasahar bayanai da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262