Sanusi II Ya Jawo Matsala da Ya Yi Hawan Sallah a Kano, Ƴan Sanda Sun Shiga Bincike
- Rundunar ƴan sanda ta aika saƙon gayyata ga Shamakin masarautar Kano, Alhaji Wada Isyaku domin ya amsa tambayoyi kan hawan Sallah
- Tun farko, mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya fito hawan Nasarawa duk da ƴan sandan sun hana bikin a shekarar bana
- Wannan ya sa rundunar ƴan sanda suka kudiri aniyar gudanar da bincike kan lamarin domin doka ta yi aiki kan duk wanda ya mata hawan ƙawara
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Rundunar ƴan sanda reshen jihar Kano ta bukaci Shamakin Kano, Alhaji Wada Isyaku, da ya bayyana a gabanta domin amsa tambayoyi.
Ƴan sanda sun gayyaci basaraken ne kan zargin da ake masa na karya umarnin ƴan sanda na hana gudanar da Hawan Sallah a fadin jihar Kano.

Asali: Twitter
Wannan mataki na kunshe a wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a shafin Facebook
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya jaddada cewa rundunar na nan kan bakarta na hana Hawan Sallah, tare da gargadin cewa duk wanda ya karya wannan umarni zai fuskanci hukunci mai tsanani.
Ɗalilin hana hawan sallah a Kano
A kwanakin baya, rundunar ƴan sandan ta sanar da hana Hawan Sallah a Kano, saboda wasu dalilai da suka danganci taaro.
Kiyawa ya ce suna da ingantattun bayanai na sirri da ke nuna cewa wasu gungun bata-gari sun shirya haddasa hargitsi da rikici a yayin gudanar da bikin Hawan Sallah.
Saboda haka, ƴan sanda suka dauki matakin hana taron don kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Haka nan, Abdulahi Kiyawa ya ce kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya kafa kwamitin bincike mai mambobi takwas domin gudanar da bincike kan rikicin da ya barke a ranar Sallah.
Hatsaniyar ta faru ne a lokacin da tawagar Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ke komawa fadarsa bayan kammala sallar Idi.
A wannan tashin hankali, an kashe wani jami’in tsaro tare da jikkata wani mai kula da tsaron tawagar sarkin.

Asali: Facebook
Bisa la’akari da hakan, rundunar ƴan sandan ta bayyana cewa bincike yana ci gaba da gudana kuma duk wanda aka samu da hannu a rikicin zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.
A halin da ake ciki, ana sa ran Shamakin Kano, Alhaji Wada Isyaku, zai bayar da cikakken bayani kan rawar da ya taka a batun Hawan Sallah, da kuma ko yana da wata alaka da sabawa dokar da aka kafa.
Rundunar ƴan sandan ta bukaci jama’a da su kwantar da hankulansu tare da bin doka da oda domin tabbatar da zaman lafiya a Kano.
Sanusi II ya yabawa Gwamna Abba
A wani labarin, kun ji cewa sarki na 16, Muhammadu Sanusi ya yaba wa Gwmana Abba kabir Yusuf bisa ayyukan ci gaban da yake gudanarwa a Kano.
Sanusi ya kuma yaba wa Majalisar Dokokin Kano bisa rawar da ta taka wajen dawo da martabar Masarautar Kano.
Asali: Legit.ng