Uromi: Barau Ya Yi Alkawari bayan Ziyartar Iyalan Hausawan da aka Kashe a Edo
- Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya ziyarci iyalan matafiyan da suka rasa rayukansu a jihar Edo
- Ya ziyarci iyalan mamatan a karamar hukumar Bunkure, a Kano tare da daukar alkawarin cewa za a tabbatar an yi adalci ga wadanda suka rasa rayukansu
- Sanata Barau ya tabbatar da cewa a lokacin da ya samu labarin kisan, ya shiga tashin hankali, tare da bibiyar hukumomi domin jin inda aka kwana
- Ya kara da cewa yanzu haka jami'an tsaro sun kamo wasu daga cikin mutanen da ake zargin sun kone matafiyan bayan sun yi musu kisan gilla
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya ziyarci karamar hukumar Bunkure a jihar Kano don ta'aziyyar matafiyan da aka kashe a garin Uromi, jihar Edo.
Sanata Barau ya hadu da iyalan mamatan, waɗanda suka fito daga kananan hukumomin Bunkure, Kibiya, Rano da Garko, a masallacin At-Taqwa da ke Sabon Fegi, Bunkure LGA.

Asali: Twitter
Wannan na kunshe a cikin mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Ismail Mudashir ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tare da Sanata Barau, akwai karamin Ministan gidaje da raya birane, Yusuf Abdullahi Ata, da Manajan Daraktan Hukumar Raya Arewa maso Yamma (NWDC), Farfesa Abdullahi Shehu Ma’aji da sauransu.
'Za a yi wa Hausawanmu adalci,' Barau
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ya tabbatar wa iyalan mamatan cewa hukumomi za su tabbatar da cewa waɗanda suka aikata wannan aika-aika sun fuskanci hukunci.

Asali: Facebook
Baya ga mutane 14 da aka kama a baya, ya ce jami’an tsaro sun sake cafke wasu mutane biyu da ake zargin su na da hannu a kisan.
Kisan Uromi: Barau ya tallafawa iyalan mamatan
Sanata Barau ya sanar da bayar da tallafin N1m ga kowane daga cikin iyalan matafiyan 16 da aka kashe, wanda ya kama N16m baki daya.
Haka kuma ya tabbatar wa iyalan da cewa zai gabatar da kudirin da zai yi magana kan lamarin a gaban majalisar dattawa bayan da ta dawo daga hutun wannan wata.
Sanata Barau ya bayyana cewa:
"Na zo nan domin jajanta maku game da wannan mummunan al’amari da ya haddasa mutuwar ‘yan uwanmu 16 a makon da ya gabata. Allah ya jikansu da rahama, ya kuma ba wa wadanda suka jikkata lafiya."
"Lokacin da na samu labarin abin da ya faru, hankalina ya tashi. Na gaggauta kiran gwamnan jihar, hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki. Sun dauki mataki, kuma har yanzu ana ci gaba da bincike. Yanzu haka, ban da mutane 14 da aka kama a baya, an sake kama wasu mutane biyu da ake zargi."
Ya ce gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo ya ba shi tabbacin ba za a bar wadanda su ka aikata wannan mummunan aiki su tafi a banza ba.
Edo: An jibge jami'an tsaro a Uromi
A baya, mun kawo labarin cewa , jami’an ‘yan sanda, sojoji, da sauran jami’an tsaro sun mamaye manyan hanyoyi a garin Uromi, Karamar Hukumar Esan ta Arewa maso Gabas a Edo.
Matakin ya biyo bayan kisan gilla da aka yi wa matafiya 16 daga Arewacin Najeriya a ranar Alhamis da ta gabata, wanda ya haifar da fushi da Allah wadai daga al’ummar Arewacin kasar.
Asali: Legit.ng