Bayan Bijirewa Gwamnati, Sanata Natasha Ta Sake Dura kan Akpabio da Tsohon Gwamna

Bayan Bijirewa Gwamnati, Sanata Natasha Ta Sake Dura kan Akpabio da Tsohon Gwamna

  • Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan na ci gaba da yin zarge-zarge kan yunƙurin yi mata kiranye daga majalisar dattawa
  • Natasha ta zargi Sanata Godswill Akpabio da tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello da hannu a shirin raba ta da kujerarta
  • Sanatar Kogi ta Tsakiya ta buƙaci Yahaya Bello da ya maida hankali kan zargin karkatar da kuɗaden da EFCC ke yi masa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kogi - Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta yi sabon zargi kan shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.

Sanata Natasha Akpoti ta yi zargin cewa Akpabio da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ne suke kitsa shirin yi mata kiranye daga majalisar dattawa.

Natasha ta zargi Akpabip
Natasha ta zargi Akpabio da hannu a shirin yi mata kiranye Hoto: Natasha H Akpoti, Nigerian Senate
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sanata Natasha ta fitar a ranar Laraba, 2 ga watan Afirilun 2025, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

Zargin kitsa Kashe Natasha: Akpabio da gwamna Ododo sun yi magana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Natasha ta yi wa all'umma godiya

Sanata Natasha ta godewa jama'arta da ɗaukacin ƴan Najeriya da suka fito ƙwansu da ƙwarƙwatarsu domin tarbar ta duk da irin barazanar da aka yi musu.

A ranar Talata, magoya bayanta daga ƙananan hukumomi biyar na Kogi ta Tsakiya sun taru tun da sassafe a Ihima, ƙaramar hukumar Okehi, domin tarbar ta.

Duk da haramcin da gwamnatin jihar Kogi ta sanya kan tarurruka, Natasha ta samu tarba mai ƙayatarwa daga magoya bayanta.

Natasha ta nuna yatsa ga Akpabio

Sanatar ta nuna takaicin yadda Akpabio zai zubar da girmansa ta hanyar haɗa kai da ɗaya daga cikin 'mutanen da EFCC ke nema ruwa a jallo' domin ya ci mutuncin Sanata mai ci saboda dalilai na ƙashin kansa.

Natasha ta ƙalubalanci tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, da ya bayyanawa duniya inda ya samo sunayen mutanen bogi da ke neman a koro ta daga majalisa.

Kara karanta wannan

Duk da kwararan matakai a Kogi, masoyan Natasha sun yi mata tarbar girma a jirgi

A cewarta, dukkan shaidun da ake da su sun nuna kai tsaye cewa Yahaya Bello ne ke jagorantar yunƙurin raba ta da kujerar ta daga majalisar dattawa.

Natasha ta ambaci irin munanan ayyukan da Yahaya Bello ya aikata kafin da kuma yayin babban zaɓen 2023, lokacin da aka zarge shi da ɗaukar nauyin hare-hare da dama a kanta lokacin da take takarar kujerar sanata.

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan
Natasha na ci gaba da zarge-zarge kan Akpabio Hoto: Natasha H Akpoti
Asali: Facebook

Sanarwar ta bayyana yunƙurin yi mata kiranye daga majalisa a matsayin ci gaba da ramuwar gayya da tsohon gwamnan ke yi mata a siyasa.

"Ina ba tsohon gwamnan shawara da ya fi mayar da hankali wajen kare kansa kan zarge-zargen karkatar da Naira biliyan 89.2, maimakon ƙoƙarin rusa amanar da al’ummar Kogi ta Tsakiya suka ba ni."
"Akwai zarge-zargen cin hanci da rashawa kan tsohon gwamnan, amma har yanzu yana ƙoƙarin hana jama'a cin moriyar zaɓin da suka yi."
"Muna sane da ayyukansa kafin da yayin babban zaɓen da ya gabata, inda ya ɗauki nauyin munanan hare-hare a kaina."

Kara karanta wannan

Kiranye: Natasha ta nuna yatsa ga INEC bayan sanar da ita shirin koro ta daga majalisa

"Wannan yunƙuri na yi min kiranye daga majalisa ba komai ba ne face wani sabon yunƙuri na tauye abin da jama’a suke so."

- Natasha Natasha Akpoti-Uduaghan

Sanata Natasha ta soki hukumar INEC

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sha suka daga wajen Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

Natasha ta zargi hukumar zaɓen da ba masu neman yi mata kiranye fifiko bayan sun yi kuskure a shirinsu na ganin ta baro majalisar dattawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel