Kisan 'Yan Arewa a Edo: Jami'an DSS Sun Cafke Manyan Wadanda Ake Zargi
- Gwamnatin jihar Edo na ci gaba da ba da bayanai a yunƙurin da ake yi na cafke masu hannu kan kisan gillar da aka yi wa ƴan Arewa
- A wata sanarwa a ranar Talata, gwamnatin ta bayyana cewa jami'an DSS sun cafke wasu daga cikin manyan waɗanda ake zargi kan kisan
- Ta bayyana cewa an cafke mutanen ne bayan an samu sahihan bayanan sirri a ƙauyen Uromi a ƙaramar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Edo - Gwamnatin Edo ta bayyana cewa jami’an hukumar tsaro ta DSS sun cafke wasu daga cikin manyan masu hannu kan zargin kisan ƴan Arewa a jihar.
Gwamnatin ta bayyana cewa jami'an na DSS sun kama manyan mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan mafarauta 16 ƴan asalin Arewacin Najeriya a Uromi, ƙaramar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas.

Kara karanta wannan
"Mutane sun yi takansu": Halin da ake ciki a garin da aka kashe ƴan Arewa 16 a Edo

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa sakataren yaɗa labaran gwamnan Edo, Fred Itua ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Talata, 1 ga watan Afirilun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kashe mafarauta ƴan Arewa a Edo
Mutanen da aka kashe mafarauta ne da ke tafiya daga Port Harcourt jihar Rivers, zuwa Kano domin bukukuwan Sallah a ranar 28 ga Maris 2025.
Jami’an sa-kai na yankin sun tare su, inda suka zarge su a matsayin masu garkuwa da mutane, sannan suka kashe su.
Kisan gillar da aka yi wa mafarautan ya jawo Allah wadai daga sassa daban-daban na ƙasar nan, inda aka buƙaci hukumomi su tabbatar an ƙwato musu haƙƙinsu.
A ina jami'an DSS suka cafke waɗanda ake zargin?
A cikin sanarwar Fred Itua, ya tabbatar da cewa an kama wadanda ake zargin ne a Uromi bayan samun sahihan bayanan sirri, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.
Ya ƙara da cewa hukumomin tsaro na ci gaba da farautar sauran manyan waɗanda ake zargi da hannu a wannan mummunan lamari.

Kara karanta wannan
Gwamnan Edo ya gana da Barau kan kisan Hausawa, ya fadi shirinsa kan iyalan mamatan
Ya bayyana cewa an tura waɗanda aka kama zuwa Abuja domin ci gaba da bincike da gurfanar da su a gaban hukuma.
An cafke wasu mutum 14 da ake zargi
A ranar Litinin, gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya kai ziyarar ta’aziyya zuwa jihar Kano, inda ya bayyana cewa tuni an kama mutane 14 da ake zargi da hannu a kisan, kuma za a tura su Abuja domin ci gaba da bincike.

Source: Twitter
Gwamna Okpebholo, wanda ya kai ziyarar ta’aziyya ga gwamnati da iyalan mamatan, ya yi alƙawarin cewa za a tabbatar da adalci, kuma duk waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki za su fuskanci hukunci.
Hakazalika, gwamnan ya tabbatarwa iyalan mamatan cewa za a biya su diyyar kisan gillar da aka yi wa mutanen.
Yadda aka kai ga kamen
Jami’an tsaro sun yi amfani da sahihan bayanan sirri don kama wadanda ake zargi, inda suka yi amfani da dabarun leƙen asiri da suka haɗa da bibiyar hanyoyin sadarwa da kuma bayanan da aka tattara daga shaidu a yankin.
An ce jami’an DSS sun bi diddikin wasu muhimman saƙonni da suka gano a wayoyin wasu daga cikin wadanda ake zargi kafin su kai farmaki a Uromi.
Wata majiyar tsaro ta bayyana cewa, wadanda ake zargin sun yi yunƙurin tserewa kafin a kama su, amma jami’an sun yi nasarar dakile yunƙurin nasu ba tare da wani tashin hankali ba.
Har yanzu dai ana ci gaba da bayyana Allah-wadai kan wannan mummunan lamari da ya auku a jihar Edo, inda 'yan siyasa ke ci gaba da karbar kiraye-kiraye daga 'yan kasa kan cewa ya kamata a dauki matakin da ya dace.
Ana sa ran gwamnatin Najeriya ta gurfanar da wadanda aka kama tare da yi masu hukuncin da ya dace da su daidai da tanadin dokar kasa.
Gwamnan Edo ya ziyarci Sanata Barau
A wani labarin kuma, kuma kun ji gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya ziyarci mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, kan kisan da aka yi wa ƴan Arewa.
Gwamnan ya yi wa Sanata Barau ta'aziyya tare da ba shi tabbacin cewa gwamnatinsa za ta biya diyya ga iyalan mamatan.
Salisu Ibrahim ya fadada labarin nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
