Sarki Sanusi II Ya Yi Babban Rashi, Galadiman Kano, Abbas Sanusi Ya Rasu

Sarki Sanusi II Ya Yi Babban Rashi, Galadiman Kano, Abbas Sanusi Ya Rasu

  • Rahotanni na nuni da cewa Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi, ya rasu ya na da shekaru 92 a duniya
  • Masarautar Kano ta bayyana cewa ya rasu ne a daren Talata 1 ga Afrilu, 2025, bayan wata jinya mai tsawo
  • An sanar da za a yi jana’izarsa a Fadar Sarkin Kano da ke Kofar Kudu da misalin karfe 10:00 na safe a ranar Laraba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Allah ya yi wa Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi, rasuwa ya na da shekaru 92 a duniya.

Mamacin, wanda shi ne mafi girma a cikin majalisar sarakunan Kano, ya rasu ne a daren Talata, 1 ga Afrilu, 2025, bayan wata jinya mai tsawo.

Galadiman Kano
Galadiman Kano, Abbas Sanusi ya rasu. Hoto: Masarautar Kano
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan rasuwar Galadiman Kano ne a cikin wani sako da masarautar Kano ta wallafa a shafinta na X.

Kara karanta wannan

'Maza sun ƙare a Kano': An shiga jimami da Galadiman Kano, Abbas Sanusi ya rasu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayin yana daya daga cikin manyan dattawan masarautar Kano, wanda ya rike mukamai da dama tun daga zamanin mahaifinsa, Marigayi Sarkin Kano Sanusi I.

Za a gudanar da sallar jana’izarsa a Fadar Sarkin Kano da ke Kofar Kudu, da misalin karfe 10 na safe a ranar Laraba, 2 ga Afrilu, 2025.

Tarihin rayuwar Galadiman Kano

An haifi marigayi Galadiman Kano Abbas Sanusi a shekarar 1933 a garin Bichi kuma ya fara karatunsa a Kofar Kudu Elementary School a shekarar 1944.

Jaridar Daily Nigerian ta wallafa cewa daga bisani ya ci gaba a Kano Middle School, wacce a yanzu ake kira Rumfa College, a shekarar 1948.

A shekarar 1959, mahaifinsa, Sarkin Kano Sanusi I, ya naɗa shi a matsayin Sarkin Dawakin Tsakar Gida da Hakimin Ungogo.

Bayan rasuwar mahaifinsa da kuma zuwan sabon Sarki, Muhammadu Inuwa, an naɗa shi Dan Iyan Kano a shekarar 1962.

Kara karanta wannan

Abubuwa 3 da ba ku sani ba game da marigayi Galadiman Kano

Ado Bayero
Marigayi sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero. Hoto: Masarautar Kano
Asali: Facebook

An ruwaito cewa daga baya, a zamanin Sarkin Kano Ado Bayero, an sake naɗa shi a matsayin Wamban Kano.

A lokacin mulkin Sarki Muhammadu Sanusi II, an naɗa shi Galadiman Kano, matsayin da ya fi girma a cikin majalisar masarautar Kano.

Daga cikin ‘ya’yan Galadiman Kano

An ruwaito cewa Galadiman Kano ya rasu ya bar 'ya'ya da jikoki da dama wanda daga cikin su akwai fitattun mutane.

Daya daga cikin ‘ya’yan marigayin shi ne Abdullahi Abbas, wanda shi ne shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano a halin yanzu.

Alhinin rashin Galadiman Kano

Ana ganin rasuwar Abbas Sanusi babban rashi ne ga masarautar Kano da daukacin al’ummar jihar.

Ya kasance dattijo mai kishin masarauta, wanda ya shafe sama da shekaru 60 yana hidimtawa masarautar Kano a mukamai daban-daban.

Manyan mutane da masarautun gargajiya na kasar nan na ci gaba da aika sakon ta’aziyya ga iyalansa da daukacin al’ummar Kano.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Sarkin Kano, Sanusi II ya ture umarnin 'yan sanda, ya yi Hawan Nasarawa

An karrama Aminu Ado Bayero

A wani rahoton, kun ji cewa wata kungiya mai zaman kanta ta karrama sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ana daf da bikin karamar sallah.

Legit ta rahoto cewa kungiyar ta ba Alhaji Aminu Ado Bayero lambar karrama wa ne a kan zaman lafiya kwanaki bayan janye hawan sallah da ya yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng