Tinubu Ya Sauke Mele Kyari da Manyan Shugabannin Kamfanin NNPCL

Tinubu Ya Sauke Mele Kyari da Manyan Shugabannin Kamfanin NNPCL

  • Shugaba Bola Tinubu ya sauke shugaban kwamitin gudanarwar NNPCL, Pius Akinyelure, da shugaban gudanarwa, Mele Kyari
  • Bola Tinubu ya nada sababbin shugabanni, inda Bashir Bayo Ojulari ya zama sabon shugaban gudanarwan kamfanin man
  • Ana sa ran sababbin shugabannin za su inganta NNPCL, farfado da masana’antar mai, da habaka harkar kasuwanci da zuba jari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince da sauya kwamitin gudanarwan kamfanin mai na kasa, NNPCL.

Bola Tinubu ya sauke tsohon shugaban kwamitin, Chief Pius Akinyelure, da kuma shugaban gudanarwar kamfanin, Malam Mele Kyari.

Tinubu
Tinubu ya yi saye sauye a NNPCL. Hoto: Bayo Onanuga|NNPCL
Asali: Getty Images

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya fitar da sanarwar a yau Laraba a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Abin da 'yan Najeriya ke cewa bayan Tinubu ya cire Mele Kyari daga shugabancin NNPCL

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sauke Mele Kyari da shugabannin NNPCL

Bayan sauke Mele Kyari, shugaba Tinubu ya tsige dukkan sauran mambobin kwamitin da aka nada tare da Akinyelure da Kyari a watan Nuwamban 2023.

Biyo bayan haka, jaridar The Cable ta wallafa cewa Bola Tinubu ya kafa sabon kwamitin da zai jagoranci kamfanin.

Sabon kwamitin yana da mutane 11, tare da Injiniya Bashir Bayo Ojulari a matsayin sabon shugaban gudanarwa da Ahmadu Musa Kida a matsayin sabon shugaban kwamitin gudanarwa.

A cewar sanarwar, Shugaba Tinubu ya nada sababbin mambobin kwamitin daga shiyyoyin ƙasar nan. Wadanda aka nada sun hada da:

  • Bello Rabiu (Arewa maso Yamma)
  • Yusuf Usman (Arewa maso Gabas)
  • Babs Omotowa (Arewa ta Tsakiya)
  • Austin Avuru (Kudu maso Kudu)
  • David Ige (Kudu maso Yamma)
  • Henry Obih (Kudu maso Gabas)

Haka nan, Lydia Shehu Jafiya daga Ma’aikatar Kudi da Aminu Said Ahmed daga Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur za su wakilci hukumominsu a kwamitin.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi martani ga Amurka kan zargin kashe kiristoci karkashin Tinubu

Fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa dukkan waɗannan nade-nade sun fara aiki ne daga yau Laraba, 2 ga Afrilu, 2025.

Dalilin sauye sauye a kamfanin NNPCL

Tinubu ya ce sauyin da aka yi a kwamitin NNPCL na da nufin inganta ayyukan kamfanin, dawo da kwarin gwiwar masu zuba jari, da kuma karfafa samar da iskar gas da albarkatun mai.

Ya bukaci shugabannin su yi cikakken bincike kan kadarorin da NNPC ke kula da su da hadin gwiwarsu da sauran kamfanoni, don tabbatar da ana tafiyar da su bisa tsari.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa tun daga shekarar 2023, gwamnatinsa ta kaddamar da sauye-sauye a harkar mai don jawo hankalin masu zuba jari.

Gwamnatin na fatan kara yawan hakar mai zuwa ganga miliyan 2 a rana nan da 2027, sannan ta kai ganga miliyan 3 a rana nan da 2030.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun cafke mataimakin shugaban ƙasa, sabon yaƙi na shirin ɓarkewa a Sudan

NNPCL
Tinubu ya sauke Mele Kyari. Hoto: NNPC Limited
Asali: Facebook

Bayani kan sababbin shugabannin NNPCL

Sabon shugaban kwamitin NNPCL, Ahmadu Musa Kida dan asalin jihar Borno ne kuma ya yi karatu a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

A daya bangaren, sabon shugaban gudanarwan NNPCL, Bashir Bayo Ojulari ma ya yi karatu a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Tinubu ya godewa tsohon kwamitin NNPCL

Shugaban ƙasa ya gode wa tsofaffin mambobin kwamitin bisa kokarinsu wajen farfado da matatun mai na Port Harcourt da Warri.

Ya yi musu fatan alheri a rayuwa, yayin da sababbin shugabannin suke shirinkarbi ragamar tafiyar da NNPCL.

An kara kudin mai a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan kasuwa sun kara kudin litar fetur a Najeriya sakamakon tashin farashin danyen mai a duniya.

An samu karin kudin ne yayin da gwamnatin Najeriya ta tsayar da sayar da danyen mai wa matatar Dangote da Naira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng