Sheikh Jingir Ya Yi wa Dan Bello Raddi Mai Zafi, Ya Kare Abdullahi Bala Lau

Sheikh Jingir Ya Yi wa Dan Bello Raddi Mai Zafi, Ya Kare Abdullahi Bala Lau

  • Sheikh Sani Jingir ya ce Sheikh Bala Lau ba barawo ba ne yayin da ya yi watsi da zargin da Dan Bello ke yi masa
  • Jingir ya bukaci Bala Lau da ya kai masu zargin shi kotu, yana mai cewa ba laifi ba ne malamai su karɓi kwangila
  • Sheikh Baban Gwale ya goyi bayan Sheikh Jingir, ya na mai cewa malaman Musulunci garkuwar addini ne

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Filato - Shugaban Ƙungiyar Izala mai hedkwata a Jos, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya mayar da martani kan zargin da Dan Bello, ke yi wa Sheikh Abdullahi Bala Lau.

Sheikh Jingir ya nuna cewa babu wata hujja da ke tabbatar da Bala Lau ya karkatar da kudin wata kwangila, ya na mai cewa ba laifi ba ne idan malami ya karɓi kwangila daga gwamnati.

Kara karanta wannan

'Magagin faduwa zabe bai sake shi ba,' Fadar shugaban kasa ta tankawa Peter Obi

Dan Bello
Sheikh Jingir ya kare Bala Lau daga zargin Dan Bello. Hoto: Jibwis Nigeria|Hamza Muhammad Sani|Dan Bello
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanan da Sheikh Jingir ya yi ne a cikin wani bidiyo da Hamza Muhammad Sani ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Bala Lau ba barawo ba ne' – Sheikh Jingir

A cikin jawabin da ya yi, Sheikh Jingir ya ce ba za su yarda a bata sunan malamai ba, ya na mai cewa zargin da Dan Bello ke yi ba shi da tushe.

“Ni a wurina, Bala Lau ba barawo ba ne. Mu ba barayi ba ne, mu ba ‘yan damfara ba ne,”

In ji Sheikh Jingir

Malamin ya kara da cewa idan ana ba waɗanda ba musulmi kwangila, to me zai hana musulmi su ma a ba su?

Baya ga haka, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya kuma zargi Dan Bello da yin amfani da makarantarsu a kan karya.

Malamin ya bayyana cewa Dan Bello yana son ya ci mutuncinsu ne amma sai ya fara zagaye zagaye ya na bata sunan Bala Lau.

Kara karanta wannan

'Ka saurare mu': Malamin Musulunci ya gargadi Ɗan Bello, ya shawarci ƴan Najeriya

Jingir ya bukaci Bala Lau shigar da kara

A cikin jawabin nasa, Sheikh Jingir ya bukaci Sheikh Bala Lau da kada ya ji tsoron kowa, ya maka wadanda ke zargisa a gaban kotu.

"Allah ya sa Bala Lau ya kai su kotu. Kada ya ji tsoro,"

- Sheikh Jingir

Malamin ya bukaci Bala Lau da ya guji mutanen da ke neman bata masa suna, tare da yin addu’ar Allah ya kare shi daga duk wani sharrin da ake yi masa.

Sheikh Baban Gwale ya yaba wa Jingir

Wani malamin addini a jihar Kano, Sheikh Abubakar Abdulsalam Baban Gwale, ya nuna goyon bayansa ga Sheikh Jingir bisa irin raddin da ya yi wa Dan Bello.

A cewarsa, malamai ne garkuwar addini, don haka ya zama dole a kare su daga duk wani sharrin da ake ƙullawa a kansu.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Izala za ta maka Dan Bello a kotu kan zargin Sheikh Bala Lau

Sheikh Baban Gwale
Sheikh Baban Gwale ya yaba wa Jingir kan raddin da ya yi wa Dan Bello Hoto: Sheikh Abubakar Abdussalam Baban Gwale
Asali: Facebook

Sheikh Baban Gwale ya wallafa a Facebook cewa:

"Allah ya saka wa Sheikh Jingir, ya kare mana malamanmu, ya kuma kunyata azzalumai,"

Ya kuma yi kira ga Dan Bello da ya tuba ya nemi gafarar Allah da bayin Allah, ya na mai cewa duniya ba za ta amfane shi ba idan bai gyara ba.

Legit ta tattauna da malamin addini

Wani malamin addini a jihar Bauchi, Ustaz Hussaini Magaji ya zantawa Legit cewa akwai bukatar Dan Bello ya gabatar da gamsassun hujjoji a kan zargin da yake yi.

Malami Hussaini ya ce:

"Kamar yadda gaskiya ta ke biyo wa ta kan kowa, idan malami ya yi kuskure ko laifi za a iya fada masa.
"Amma dai dole ya zama bisa hujjoji ba kawai zargi ba. Saboda haka idan Dan Bello yana so a gaskata shi, sai ya amsa tambayoyin da aka yi masa"

Kara karanta wannan

Hafsan tsaro ya tsoma baki kan kisan ƴan Arewa a Edo, ya fadi shirinsu kan lamarin

Hukuncin rama sallar Idi a Musulunci

A wani rahoton, kun ji cewa fitaccen malamin addini da aka yi a Najeriya, marigayi Dr Ahmad Bamba ya taba magana kan rama sallar Idi.

Sheikh Bamba ya bayyana cewa ya halasta mutum ya rama sallar Idi idan ya makara ranar sallah, kuma za a iya rama ta a gida ko masallaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng