Ana tsaka da Shagulgulan Sallah, Gwamna Ya Yi Barazanar Tsige Sarakuna 3 daga Mulki

Ana tsaka da Shagulgulan Sallah, Gwamna Ya Yi Barazanar Tsige Sarakuna 3 daga Mulki

  • Gwamna Ademola Adeleke ya gargaɗi sarakuna kan wasu rahotanni da aka samu cewa ana shirin tayar da rikici a yankunansu
  • Mai girma Adeleke ya yi barazanar cewa zai tuɓe masu rawani matuƙar suka gaza tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali
  • Ya gargaɗi mazauna yankunan cewa gwamnatinsa ta sassauta dokar hana fita ne ba don mutane su ci gaba da faɗa ba, ya yi haka ne saboda jin ƙai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Osun - Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya gargaɗi sarakunan gargajiya na Ifon, Erin Osun da Ilobu kan rigingimun da ke faruwa a tsakaninsu.

Gwamnan ya yi wa sarakunan barazanar cewa gwamnatinsa za ta ɗauki mataki mai tsauri a kansu idan suka kasa tabbatar da zaman lafiya a yankunansu.

Gwamna Adeleke.
Gwamna Adeleke ya gargaɗi sarakunan Ifon, Erin Osun da Ilobu kan tayar da zaune tsaye Hoto: Ademola Adeleke
Asali: Twitter

Adeleke ya fitar da wannan gargaɗi ne biyo bayan rahotannin da ke yawo a kafafen sadarwa cewa ana shirin sake ta da yamutsi a garuruwan biyu uku, in ji Channels tv.

Kara karanta wannan

"Mutane sun yi takansu": Halin da ake ciki a garin da aka kashe ƴan Arewa 16 a Edo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna ya yi barazanar tsige sarakuna 3

Ya ce zai iya tuɓe rawanin sarakunan idan ta kama matukar suka zuba ido suka bari wani sabon rikici ya ɓarke a garuruwansu.

An tattaro cewa wasu gungun mutane da ba a san su ba na shirin tayar da rikici a yankunan da aka jima ana fama da faɗace-faɗace tsakanin al'ummomi.

"A yayin shagulgulan Sallah, na samu rahotanni cewa wasu mutane na shirin tayar da rikici a Ifon, Ilobu da Erin Osun. Jami’an tsaro sun ƙara tsaurara matakan tsaro don hana kai hare-hare
"Jami’an tsaro sun fara binciken manyan shugabanni da mutanen da ake zargi da hannu a rikicin. Ina so in tunatar da manyan shugabannin yankunan cewa yarjejeniyar zaman lafiya da suka rattabawa hannu ba abin wasa ba ce.

Dalilin gwamna na sassauta dokar kulle

Gwamma Adeleke ya kara da cewa ya sassauta dokar hana fita domin mutane su samu damar ci gaba da harkokinsu na yau da kullum, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Gwamnan Edo ya gana da Barau kan kisan Hausawa, ya fadi shirinsa kan iyalan mamatan

"Dalilin sassauta dokar hana fita shi ne saboda jin ƙai. A matsayina na gwamna mai tausayi, na fahimci cewa da dama daga cikin mutanen da ke fama da wahala a yankunan rikicin ba su da hannu a cikin wannan fitina.
"Idan mutane suka yi ƙoƙarin amfani da sassaucin dokar don wajen tayar da rikici, za mu mayar da dokar hana fita na sa’o’i 24.
"Kari kan haka, zan tube rawanin duk wani sarki da rikici ya sake ɓarkewa a garinsa, wannan mataki yana nan daram. Ya zama dole sarakuna su ja kunnen mutanensu. Zan ɗauki mataki mai tsauri. Ya isa haka!"

- In ji Adeleke.

Gwamna Adeleke.
Gwamnan Osun ya gargaɗi sarakunan garuruwa 3 su gujewa tashin-tashina a yankunansu Hoto: Ademola Adeleke
Asali: Twitter

An nemi Tinubu ya sa dokar ta ɓaci a Osun

A wani labarin, kun ji cewa tsohon ministan harkokin ‘yan sanda, Oyewale Adesiyan, ya bukaci a ayyana dokar ta-baci a jihar Osun saboda tashin tashinar da ake samu.

Ya zargi Gwamna Ademola Adeleke da nuna rashin biyayya ga hukuncin kotu, wanda ya ce hakan ne ya haddasa rikicin da ya kai ga salwantar rayukan mutane.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng