"Mutane Sun Yi Takansu": Halin da Ake ciki a Garin da Aka Kashe Ƴan Arewa 16 a Edo
- Mutanen Uromi sun fara guduwa suna barin gidajensu saboda fargaba bayan kisan gillar da aka yi wa Hausawa a jihar Edo
- Rahotanni sun nuna cewa mazauna garin sun fara ƙorafin ana kama marasa laifi domin waɗanda suka aikata kisa sun gudu tuntuni
- Wannan dai na zuwa ne bayan jami'an tsaro sun fara cafke waɗanda ake zargi da hannu a aikata wannan aika-aika
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Edo - Mutanen da ke zaune a titin Old Ilushi, Opere, da Good Will Junction a Uromi, Jihar Edo, sun kaurace wa gidajensu saboda fargabar ramuwar gayya da kamen jami'an tsaro.
Mutane sun fara guduwa suna barin gidajensu a Uromi ne biyo bayan kisan gillar da aka yi wa mafarauta 16 ƴan Arewa a makon da ya shige.

Asali: Original
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa hakan na zuwa ne bayan Gwamna Monday Okpebholo na Edo ya ziyarci Kano a jiya inda ya ce za a tabbatar da adalci ga wadanda aka kashe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutane sun fara tserewa daga Uromi
Rahotanni sun bayyana cewa mazauna Uromi da kewaye sun daina zuwa gonakinsu, da yawa daga ciki sun gudu sun nemi mafaka a wasu garuruwa na makwabta.
Wani mazaunin yankin da ya bayyana sunansa a matsayin Monday, ya ce:
“Kungiyar ‘yan banga ta samu bayanai daga wasu wuraren da ke kan hanyar Old Ilushi cewa matafiyan na dauke da makamai a motarsu.
"Da suka iso Uromi, ‘yan bangar suka bukaci su fito daga mota, amma suka ki, wanda hakan ya haddasa husuma. Daya daga cikinsu ya fito da wuka, hakan ya sa ‘yan bangar suka ɗaga murya suna zargin ‘yan fashi ne.
“Kowa ya san cewa abin da aka yi ba daidai bane. Duk da haka, wadanda suka aikata wannan danyen aiki sun tsere, yayin da jami'an tsaro kuma sun fara kama waɗanda basu da laifi.
Ana zargin kama waɗanda ba su da laifi
Monday ya ƙara da cewa ƴan sanda sun kama wani matashi ɗan acaɓa ranar Asabar duk da ya gaya masu bai ma san abin da ya faru ba.
"Yanzu dai yankin ya kasance babu yawan mutane, sai ‘yan tsiraru da ke wucewa a kan babura. A ranar Litinin da misalin karfe 12 na rana, ‘yan sanda sun sake dawowa domin kama wasu da ake zargi," in ji shi.

Asali: Facebook
Wani mazaunin yankin na daban da ya bayyana sunansa a matsayin Akhere, ya ce:
"Duk da cewa ba mu goyon bayan kisan gilla, amma wadannan mutane ba masu farauta ba ne kamar yadda ake fada, domin mun san yadda mafarauta ke tafiya da karnuka.
"Yan banga sun dade suna bibiyar wadannan ‘yan bindiga da ake zargi da garkuwa da mutane. Abin ya daure wa mutane kai, don haka ranar da abin ya faru, an gansu a kusa da Ubiaja.
"An ce an ga sun dakatar da wata motar dakon kaya, suka shiga tare da makamai da wasu kayan su da ake zargin kudi ne a ciki.
“Ina ganin kuskuren da ‘yan bangar suka yi shi ne kin mika su ga ‘yan sanda, maimakon daukar doka a hannunsu.
Gwamnan Edo ya yi alƙawarin biyan diyya
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Edo ya yi alkawarin biyan diyya ga iyalan mafarauta 16 da wasu 'yan jiharsa suka yi wa kisan gilla.
Monday Okpebholo ya yabawa al’ummar jihar Kano saboda jajircewarsu tare da gujewa daukar doka a hannu, duk da munin al’amarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng