Alkawarin Gwamnan Edo ga Iyalan Mafarautan Kano da aka Kashe a Jiharsa

Alkawarin Gwamnan Edo ga Iyalan Mafarautan Kano da aka Kashe a Jiharsa

  • Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya bayyana takaicinsa kan yadda wasu daga cikin mutanensa suka yi wa wasu mafarauta, kisan gilla
  • A makon da ya gabata, wasu ‘yan bijilanti da 'yan gari sun tare motar Dangote da mafarautan ke ciki, tare da kashe 16 daga cikinsu
  • A ziyarar da ya kai Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya raka Okpebholo har garin wasu daga cikin mamatan domin yi wa iyalansu ta'aziyya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya yi alkawarin biyan diyya ga iyalan mafarauta 16 da wasu 'yan jiharsa suka yi wa kisan gilla.

Rahotanni sun nuna cewa kungiya ta sa-kai ta jihar ce ta jagoranci kashw bayin Allah a Uromi, yayin da suke kan hanyarsu daga Fatakwal zuwa Kano don yin bikin Sallah tare da iyalansu.

Kara karanta wannan

Bidiyon Abba Kabir ya jagoranci Okpebholo zuwa ga iyalan wadanda suka mutu a Edo

Kanawa
Gwamna Monday Okpebholo ya ya isa Kano kan kisan mafarauta Hoto: Sunusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Mista Okpebholo ya yi alkawarin biyan diyyar ne a lokacin da ya ziyarci iyalan mamatan a Torankawa, jihar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ne ya yi masa jagora har zuwa garin mafarautan domin yi masu ta'aziyyar mummunan kisan da aka yi wa yan uwansu

Gwamnan Edo ya yabi mutanen Kano

Daily Post ta wallafa cewa Mista Okpebholo ya yabawa al’ummar jihar Kano saboda jajircewarsu tare da gujewa daukar doka a hannu, duk da munin al’amarin.

Ya ce:

“Ina kuma yabawa mutanen Kano da daukacin Arewacin Najeriya saboda rashin daukar doka a hannunsu da kuma kin daukar fansa.”
“Mun zo nan domin jajantawa iyalan mamatan. Muna tabbatar muku cewa za a hukunta duk masu hannu a wannan aika-aika. Allahu ya gafarta musu, ya sanya su a Aljanna."

"An fara kame," Gwamnan Edo kan kisan Kanawa

Gwamnan jihar Edo ya bayyana cewa an fara kama wasu da ake zargin suna da hannu a kisan gilla da aka yi wa mafarautan Kano.

Kara karanta wannan

Gwamnan Edo ya gana da Barau kan kisan Hausawa, ya fadi shirinsa kan iyalan mamatan

Kanawa
Jama'ar da su ka tarbi gwamna Abba Kabir Yusuf da takwaransa na Edo, Monday Okpebholo Hoto: Sunusi Bature D Tofa
Asali: Facebook

Monday Okpebholo ya ce:

“An kama kimanin mutane 14 da ake zargi da hannu a wannan kisan. Za mu ci gaba da bin wannan batu har sai an kai ga hukunta duk masu hannu a ciki.” Muna kuma shirin biyan diyya ga duk iyalan da abin ya shafa."

Alkawarin Gwamnan Kano ga iyalan mafarauta

A jawabinsa tun da fari, Gwamna Abba ya yi addu’a ga rayukan mamatan, tare da bayyana cewa ana daukar matakan ganin cewa an yi adalci.

Abba Kabir Yusuf ya ce:

“Muna aiki tare da Gwamna Okpebholo domin tabbatar da cewa duk wanda aka kama za a gurfanar da su a gaban shari’a.”
“Muna kuma kokarin biyan diyya ga duk iyalan mamatan. Na yi alkawarin ba su tallafin kudi da kayan abinci.”

Ya kara da cewa za a biya diyyar mamatan, kuma gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an yi adalci ga wadanda aka kashe.

Kara karanta wannan

Gwamnan Sokoto ya yi magana da babbar murya kan kisan 'yan Arewa a Edo

Gwamnatin Kano da fusata kan kisan 'yan Arewa

A baya, mun wallafa cewa gwamnatin Kano ta bayyana matuƙar kaduwarta kan yadda wasu 'yan bijilanti da jama'ar gari su ka hallaka Hausawa, mafarauta a Uromi da ke jihar Edo.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce dole ne hukumomi su dauki matakin gaggawa don ganin an yi adalci, tare da bayyana cewa ba wannan ne na farko da ake kashe Hausawa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.