Gwamna ko Sanata: Shehu Sani Ya Fadi Kujerar da Zai Tsaya Takara a 2027

Gwamna ko Sanata: Shehu Sani Ya Fadi Kujerar da Zai Tsaya Takara a 2027

  • Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi magana kan kujerar da zai nema a zaɓen shekarar 2027 mai zuwa
  • Shehu Sani ya bayyana aniyarsa ta sake neman kujerar sanatan Kaduna ta Tsakiya a zaɓen 2027
  • Tsohon sanatan ya bayyana cewa za su yi aiki tuƙuru domin tabbatar da cewa Gwamna Uba Sani ya sake komawa kan kujerarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya yi magana kan sake yin takara a 2027.

Sanata Shehu Sani ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takarar kujerar sanatan Kaduna ta Tsakiya a zaɓen 2027 mai zuwa.

Shehu Sani
Shehu Sani ya ce zai sake tsayawa takara Hoto: Shehu Sani
Asali: Twitter

Shehu Sani ya yi wannan furucin ne a ranar Lahadi yayin da yake gabatar da saƙon bikin ƙaramar Sallah a gidansa da ke Kaduna, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya fadi matsayarsa kan umarnin hana hawan Sallah a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shehu Sani ya kuma yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga Musulmi da su ci gaba da yin addu’a domin samun zaman lafiya da haɗin kai a Najeriya yayin bikin Sallah.

Shehu Sani zai sake neman kujerar sanata

"Duk wani ɗan siyasa da ke son tsayawa takara yana dogara ne ga yanayin siyasa wanda ya yi daidai da muƙamin da zai nema."
"Idan abubuwa suka zo daidai kuma lissafin siyasa ya tafi yadda ake so, zan tsaya takara musamman don kujerar Sanatan Kaduna ta Tsakiya."

- Sanata Shehu Sani

Ya ƙara da cewa, burinsa na tsayawa takara bai kai muhimmancin tabbatar da cewa an sake zaɓen Gwamna Uba Sani a wa’adi na biyu ba.

"A yanzu dai, abin da yafi zama muhimmanci a gare mu shi ne tabbatar da cewa gwamna mai ci, Uba Sani, ya sami damar yin tazarce. Za mu yi aiki tuƙuru da duk iyawarmu domin cimma wannan burin."

Kara karanta wannan

Faɗan giwaye: Ɗan majalisa na neman kassara Sanata Yari domin rage masa tasiri?

"Mun san cewa za a samu ƙalubale da adawa, amma mun shirya tsaf don fuskantar duk wata matsala."

- Sanata Shehu Sani

Shehu Sani ya yi Allah kan kisan ƴan Arewa

Hakazalika, ya yi Allah-wadai da kisan gilla da aka yi wa wasu mafarauta ƴan Arewa a jihar Edo, inda ya buƙaci hukumomin tsaro su gaggauta kamo waɗanda suka aikata wannan mummunan aikin.

“Idan ƴan ƙasa ba za su iya tafiya cikin ƴanci a faɗin ƙasar nan ba, to ba za mu iya cewa muna da ƙasa ɗaya ba."
"Idan kuma mutane suna ɗaukar doka a hannunsu ba tare da tsoron hukuma ba, hakan na nufin babu gwamnati ko wata hukuma mai iko."

- Sanata Shehu Sani

Shehu Sani
Shehu Sani zai sake tsayawa takara a 2027 Hoto: @ShehuSani
Asali: Twitter

Ya yi kira ga duk ƴan Najeriya da ke fatan ganin ƙasar nan ta gyaru, da su yi aiki don samun zaman lafiya da haɗin kai domin ci gaba da tabbatar da dimokuraɗiyya, duk da ƙalubalen da ake fuskanta.

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin Matawalle ya tabo batun dokar ta baci a Zamfara, ya ba Tinubu shawara

Hakazalika, Shehu Sani ya buƙaci gwamnati da ta mutunta haƙƙin ɗan Adam, musamman ƴancin rayuwa, domin wannan shi ne matakin farko na tabbatar da kwanciyar hankali da ci gaban ƙasa.

Shehu Sani ya faɗi dalilin komawa APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi ƙarin haske kan dalilin da ya sa ya koma jam'iyyar APC.

Shehu Sani ya bayyana cewa tun da farko saɓanin da suka samu da Nasir El-Rufai ne ya sanya ya fice daga jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng