'An ba Ni Cin Hancin Naira Biliyan 5 domin Tsige Fubara,' Ehie Ya Yi Zazzaga
- Edison Ehie ya ce an yi kokarin ba shi cin hanci na Naira biliyan 5 domin ya jagoranci tsige Gwamna Siminalayi Fubara
- Ya musanta cewa yana da hannu a rusa Majalisar Dokokin Jihar Rivers, yana mai cewa zai kai kara kan zargin da aka masa
- Rikicin siyasa na ci gaba da ruruwa a Rivers tun bayan sabani tsakanin Gwamna Fubara da tsohon gwamna, Nyesom Wike
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Rivers - Shugaban ma’aikatan gwamnatin Siminalayi Fubara, Edison Ehie ya bayyana cewa an yi kokarin ba shi cin hancin Naira biliyan 5 domin ya jagoranci tsige Fubara.
Edison Ehie ya taba zama kakakin tsagin majalisar Dokokin Rivers har zuwa watan Janairun 2024.

Asali: Facebook
Rahotanni sun nuna cewa ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ya yi a wani shiri na Channels Television.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce har yanzu yana da shaidar wannan tayin a cikin wayarsa, kuma ya riga ya buga takardun shaidar domin kare kansa daga duk wani yunkurin cutar da shi.
‘Ina da Shaida a Wayata’ - Edison Ehie
Jaridar the Cable ta wallafa cewa Ehie ya ce an yi masa tayin kudin ne a watan Oktoban 2023, lokacin da yake shugabantar masu rinjaye a majalisar dokokin Rivers.
“Ina da dukkan shaidu a cikin wayata. A farkon watan Oktoban 2023, an yi kokarin ba ni cin hancin Naira biliyan 5 domin in jagoranci tsige Gwamna Fubara,”
- Edison Ehie
Ya kara da cewa ya riga ya fitar da shaidar a rubuce kuma ya rarraba takardun don kare kansa daga duk wani shirin da ake da shi na cutar da shi.
Musa zargin rusa majalisar Rivers
Baya ga batun cin hanci, Edison Ehie ya musanta zargin da tsohon shugaban ma’aikatan Jihar Rivers, George Nwaeke, ya yi masa na cewa yana da hannu a rusa ginin majalisar dokokin jihar.
A wani taron manema labarai da Nwaeke ya yi a ranar Juma’a, ya zargi Ehie da cewa Gwamna Fubara ne ya ba shi umarnin rusa majalisar dokokin Rivers a ranar 30 ga Oktoba, 2023.

Asali: Instagram
Nwaeke ya ce ya shaida da idonsa lokacin da aka ba Ehie wata jaka cike da kudi a fadar gwamnati don aiwatar da wannan aiki, duk da cewa bai san adadin kudin da ke cikin jakar ba.
Sai dai a martaninsa, Ehie ya musanta wannan zargi kwata-kwata, yana mai cewa hakan wani yunkuri ne na bata masa suna a siyasa.
“Kamar sauran mutane, a safiyar ranar 30 ga Oktoba 2023 na ji labarin rusa majalisar Rivers. Ba ni da wata alaka da lamarin,”
- Edison Ehie
Ya kara da cewa ya riga ya umarci lauyoyinsa su shigar da kara kan Nwaeke saboda cin zarafi da bata suna, yana mai cewa ya kamata ya gabatar da shaidar da zai tabbatar da zargin da ya yi.

Kara karanta wannan
Kungiyar Izalah ta yi maganar kisan ƴan Arewa a Edo, ta fadi hanyar dakile lamarin
IYC ta bukaci a dawo da Fubara a Rivers
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar IYC ta bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dawo da gwamna Simi Fubara.
Kungiyar ta ce dakatar da gwamnan ya saba dokar kasa kuma hakan ba zai haifar da da mai ido a jihar da ke fama da rikicin siyasa ba.
Asali: Legit.ng