Tinubu zai Karbo Bashin $500m a Bankin Duniya, za a Raba Tallafi wa Jama'a

Tinubu zai Karbo Bashin $500m a Bankin Duniya, za a Raba Tallafi wa Jama'a

  • Bankin Duniya ya amince da bayar da bashin Dala miliyan 500 ga Najeriya don tallafa wa shirin inganta tattalin arziki
  • Kudin zai taimaka wajen samar da tallafi ga gidaje da kananan sana’o’i da ke fama da matsin tattalin arziki
  • Har ila yau, ana sa ran amincewa da karin wasu rancen guda biyu da suka shafi ilimi da ci gaban al’umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Bankin Duniya ya amince da bayar da rancen Dala miliyan 500 ga Najeriya a wani mataki na bunkasa tattalin arziki a kasar.

Wannan mataki yana cikin shirin CARE wanda ke da nufin samar da tallafi ga gidaje da kananan sana’o’i da ke fama da matsin tattalin arziki.

Najeriya
Gwamnatin Najeriya za ta karbi bashin $500m a bankin duniya. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

A cewar bayanai a shafin Bankin Duniya, amincewa da bashin da aka yi a ranar 28 ga Maris, 2025, mataki ne da zai taimaka wajen rage tasirin hauhawar farashi da sauran kalubalen tattali.

Kara karanta wannan

Atiku ya mayar da hankali kan tausaya wa talaka a sakon barka da sallah

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin karbar bashin $500m a bankin duniya

Shirin CARE zai tallafa wa gidaje da ‘yan kasuwa masu karamin karfi ta hanyar samar da kudin tallafi domin rage radadin matsin tattalin arziki.

Har ila yau, shirin zai mayar da hankali wajen inganta wadatar abinci da samar da damammakin tattalin arziki ga al’ummomin da ke fuskantar matsaloli sakamakon tabarbarewar tattali.

An ce shirin zai fi mayar da hankali kan inganta jin dadin rayuwa ta hanyar samar da kudin tallafi ga gidaje da kananan ‘yan kasuwa domin su samu damar farfadowa daga durkushewa.

Karin karbar bashi kan ilimi da lafiya

Baya ga rancen dala miliyan 500 da aka amince da shi, ana sa ran Bankin Duniya zai amince da wasu karin bashin guda biyu nan da karshen mako.

Daya daga cikin bashin zai mayar da hankali kan samar da ilimi mai inganci ga kowa a fadin Najeriya.

Kara karanta wannan

An farmaki ƴan Hisbah yayin hana ƙwallo a masallacin da ake tahajjud, sun samu raunuka

Jaridar Business Day ta wallafa cewa ana sa ran a ranar 31 ga Maris, 2025, Bankin Duniya zai kammala tattaunawa kan kudin tare da amincewa da su.

Tasirin bashin ga tattalin arzikin Najeriya

A yayin da Najeriya ke fama da hauhawar farashi da kuma wahalar rayuwa, ana ganin bashin zai taka rawa wajen samar da tallafi ga al’umma da kuma farfado da tattalin arziki daga tushe.

Hukumar da ke kula da shirin CARE ta bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wajen rage radadin wahalar da jama’a ke fuskanta, musamman ta hanyar bunkasa abinci.

Baya ga haka, ana sa ran bashin zai kuma bai wa ‘yan kasuwa jari domin farfadowa daga matsin tattalin arziki da suka shiga.

Najeriya
Gwamnatin Najeriya za ta karbi bashi a bankin duniya domin habaka tattali. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Yanzu dai ana jiran matakin karshe daga Bankin Duniya kan amincewa da karin kudin da za su taimaka wajen bunkasa ilimi da ci gaban al’umma a Najeriya.

Atiku ya bukaci a tallafa wa talaka

Kara karanta wannan

Bayan kona 'yan Arewa kurmus a Edo, an kashe mutane 10 da ke zaman makoki a Filato

A wani rahoton, kun ji cewa Atiku Abubakar ya yi kira ga shugabannin Najeriya da su tausaya wa talaka bayan azumin Ramadan.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce ya kamata talakawa su fara gani a kasa maimakon yadda ake ba su hakuri a kullum.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng