Atiku Ya Mayar da Hankali kan Tausaya wa Talaka a Sakon Barka da Sallah
- Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya ce azumin bana ya zo ne a lokacin da al’umma ke fama da matsananciyar wahala da yunwa
- A karkashin haka, ya bukaci shugabanni su dauki matakan rage radadin tattalin arziki bayan Ramadan domin inganta jin dadin al’umma
- Haka zalika, Atiku Abubakar ya yi kira da a ci gaba da ayyukan alheri da aka saba yi a Ramadan tare da yin addu’o’i domin cigaban kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Adamawa - Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya ce azumin Ramadan na bana ya zo a lokacin da ‘yan Najeriya ke fama da matsananciyar wahala da karancin abinci.
Atiku ya ce Ramadan ya saba karfafa wa Musulmi yin kyauta da taimakon mabukata, don haka yana da mahimmanci a tabbatar da cewa an cigaba da haka bayan azumi.

Asali: Facebook
A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, ya ce ya kamata gwamnatoci sun dauki matakan ci gaba da tallafa wa al’umma da rage radadin rayuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma bukaci shugabanni su yi koyi da koyarwar Manzon Allah (SAW) dangane da hakkin da ke kansu wajen inganta rayuwar jama’a.
Kiran gwamnati kan wahalar tattalin arziki
Atiku ya ce bai dace shugabanni su tsaya kawai suna kiran ‘yan kasa da su kara daurewa cikin halin kuncin tattalin arziki ba.
A cewarsa, ya fi dacewa su nuna tausayawa tare da daukar matakan rage radadin wahalar da ake ciki.
Ya jaddada cewa shugabanci wajibi ne, don haka dole ne shugabanni su kasance masu jin tsoron Allah wajen kula da rayuwar jama’a, ta hanyar samar da walwala da jin dadin al’umma.
Atiku ya bukaci gwamnati da ta mayar da hankali kan manufofi da tsare-tsare da za su taimaka wajen saukaka wa talakawa radadin hauhawar farashin kayayyaki.
Bukatar yin ayyukan alheri bayan Ramadan
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bukaci al’ummar Musulmi da su ci gaba da ayyukan alheri da suka yi a cikin watan Ramadan, ba wai su dakatar da su bayan kammala azumi ba.
Ya ce bukukuwan Idi na da muhimmanci wajen tunatar da mutane su kasance masu hakuri, tausayi, da sadaukarwa kamar yadda aka yi a lokacin Ramadan.
Atiku ya kuma bukaci ‘yan kasa da su ci gaba da yin addu’o’i don samun ci gaba a rayuwar su ta kashin kansu da kuma ci gaban kasa.

Asali: Facebook
Kira ga hadin kai da zaman lafiya
A karshe, Atiku Abubakar ya bukaci al’ummar Najeriya da su hada kai domin magance matsalolin da ke hana cigaban kasa.
Ya jaddada cewa hadin kai da zaman lafiya ne za su taimaka wajen ciyar da kasa gaba da samar da abubuwan more rayuwa.
An hana hawan sallah a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Kano ta hana hawan sallah da aka saba yi duk shekara.
Kakakin 'yan sandan jihar, Haruna Abdullahi Kiyawa ya ce an dauki matakin ne domin hana samuwar wani rikici a lokacin bikin sallah.
Asali: Legit.ng