Bayan Saudiyya, Sarkin Musulmi Ya Sanar da Ranar Karamar Sallah a Najeriya
- Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar ya fitar da sanarwa kan ganin watan Shawwal a Najeriya
- Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar ya bayyana an samu rahotannin ganin watan Shawwal 1446AH a sassa daban-daban na Najeriya
- Ya bayyana cewa gobe Lahadi, 30 ga watan Maris 2025, ita ce daidai da 1 ga watan Shawwal 1446AH
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar ya sanar da ganin jinjirin watan Shawwal a Najeriya.
Sarkin Musulmin ya bayyana ranar Lahadi a matsayin 1 ga watan Shawwal na shekarar 1446AH.

Asali: Facebook
Mai alfarma Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a wani jawabi na kai tsaye da ya yi wa ƴan Najeriya a daren ranar Asabar, 29 ga watan Maris 2025, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ga watan Shawwal a Najeriya

Kara karanta wannan
Rai baƙon duniya: Musulunci ya yi rashi bayan sanar da rasuwar malami a watan azumi
Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar ya bayyana cewa an samu rahotannin ganin watan a sassa daban-daban na Najeriya.
Sarkin Musulmin ya ce an samu rahotanni kan ganin sabon wata daga wasu sarakuna da shugabannin addini, kuma an tabbatar da sahihancinsu.
Ya yi kira ga al'ummar Musulmi da su ci gaba da yi wa shugabanni addu’a domin Allah Ya shiryar da su wajen sauke nauyin da ke kansu yadda ya kamata, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
Hakazalika, ya buƙace su da su ci gaba da zama lafiya da makwabtansu tare da yin addu’a don zaman lafiya da ci gaban ƙasa.
Sarkin Musulmi ya aika saƙo ga ƴan Najeriya
"Mun samu rahotanni daga shugabannin Musulmi da ƙungiyoyi daban-daban, kamar Shehun Borno, Sarakunan Dutse, Argungu, Maru, Daura, da Zazzau."
"Haka nan, mun kuma samu rahoto daga shugabannin JIBWIS waɗanda suka tabbatar da ganin sabon watan Shawwal 1446AH."
"Saboda haka, gobe 30 ga watan Maris 2025 ita ce 1 ga watan Shawwal 1446AH, kuma ita ce ranar Sallar Eid-el-Fitr."
"Muna kuma kira ga dukkan Musulmi, ko ina muke, da mu ci gaba da zama lafiya da junanmu, mu yi wa shugabanninmu addu’a."
"Kamar yadda muka ga watan Ramadan, kuma yanzu ya zo ƙarshe, muna roƙon Allah cikin rahamarsa da Ya ba mu damar ganin na shekaru da dama masu zuwa, domin mu ci gaba da bauta masa yadda ya dace."
"Allah Ya cika mana burikanmu, Ya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasarmu mai girma, Najeriya. Allah Ya sa shugabanninmu su ji tsoronsa a koda yaushe."
"Allah Ya ba mu ikon ci gaba da rayuwa cikin zaman lafiya da juna. Ina yi muku fatan alheri da zaman lafiya, kuma ina cewa Barka da Sallah ga dukkan ƴan Najeriya."
- Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar
Saudiyya ta sanar da ganin wata
A wani labarin kuma, kun ji cewa mahukunta a ƙasar Saudiyya sun sanar da ranar da za a gudanar da ƙaramar Sallah ta shekarar 1446AH.
Mahukuntan sun sanar da cewa za a gudanar da Sallar Idi (Eid el Fitr) a ranar Lahadi, 30 ga watan Maris 2025 wanda ya yi daidai da 1 ga watan Shawwal 1446AH.
Asali: Legit.ng