Shekara 73: Buhari Ya Aika Sako ga Tinubu, Ya Fadi Yadda Dangantakarsu Ta ke
- Tsohon shugaban ƙasan Najeriya, Muhammadu Buhari, ya aika da saƙo taya murnar zagayowar ranar haihuwa ga mai girma Bola Tinubu
- Muhammadu ya taya Bola Tinubu murnar cika shekara 73 a duniya tare da yi masa addu'ar Allah ya ƙara masa lafiya da tsawancin kwana.
- Tsohon shugaban ƙasar ya nuna muhimmancin yi wa shugabanni addu'o'i domin samun sauke nauyin da ke kansu yadda ya kamata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya taya mai girma Bola Ahmed Tinubu murnar cika shekara 73 a duniya.
Muhammadu Buhari ya taya shugaban ƙasan murnar ne a cikin wata waya da suka yi a ranar Juma'a.

Asali: Twitter
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaba Buhari, Garba Shehu, ya sanya a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Buhari ya faɗi dangantakarsa da Tinubu
Buhari ya jaddada danƙon zumuncin da ke tsakaninsa da shugaban ƙasan, inda ya taya shi murnar ƙara shekara ɗaya cikin shekarunsa na duniya.
A cikin wayar da suka yi a ranar Juma’a, tsohon shugaban kasa ya bayyana cewa shi da iyalinsa suna addu’a ga Tinubu domin ya samu tsawon rai, lafiya, da kuma samun nasara a jagorantar ƙasar nan da yake yi.
"Idan muna yi wa shugabanninmu addu’a, muna yi wa kanmu da kuma ƙasarmu addu’a ne. Wannan haƙƙi ne a kanmu da kuma ƙasar nan."
- Muhammadu Buhari
Tsohon shugaban ƙasar ya ce shi da iyalinsa za su ci gaba da tunawa da shugaba Tinubu da sauran shugabannin jam’iyyar saboda rawar da suka taka wajen kafa jam’iyyar APC.
Muhammadu Buhari ya yabawa Tinubu
Ya ce wannan gudunmawar ta ba shi damar zama shugaban ƙasa sau biyu, bayan rashin nasarar da ya yi a baya, da kuma taimakawa wajen samar da wata gwamnatin APC da Asiwaju Tinubu ke jagoranta.

Kara karanta wannan
"Hantar Tinubu ta kaɗa": An faɗi wanda ya dace Atiku, Obi da El Rufai su marawa baya a 2027

Asali: Facebook
"Babu shakka, tarihin ƙasar nan ba zai cika ba idan ba a ambaci kuma ba a yaba da irin rawar da Shugaba Tinubu ya taka ba."
"Ya taka rawa a matsayin ɗan kasuwa, jagoran jam’iyya, gwarzon ɗan fafutuka, mai gina jam’iyya, amini na ƙwarai, da kuma wanda ya saba yin nasarar lashe zaɓuka a tsarin dimokuradiyya. Ina alfahari da dangantakata da Asiwaju."
"Lokacin da ƴan Najeriya suka miƙa ragamar shugabanci ga APC a shekarar 2015, sun ba da dama domin a gina sabuwar Najeriya da za ta bai wa talakawa damarmaki don samun kyakkyawar makoma."
"Kuma ina farin ciki cewa wannan hangen nesa bai ɓace ba. Wannan nasara ce ga duk masu son ci gaban ƙasa nan."
- Muhammadu Buhari
Ya kuma yi amfani da wannan dama wajen yi wa shugaban lasa, iyalinsa, da daukacin al’ummar Najeriya fatan kammala azumin Ramadan cikin nasara da kuma murnar bikin Sallah.
Tinubu zai lashe Kano a 2027 - Akpabio
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya fara hango nasarar da Bola Tinubu zai samu a zaɓen 2027.
Godswill Akpabio ya bayyana cewa mai girma Shugaba Tinubu da jam'iyyar APC za su samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa a jihar Kano a 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng