Zakkatul Fitr: Hukunce Hukuncen Zakkar Fidda Kai a Addinin Musulunci
- Sheikh Jabir Maihula ya yi bayani dalla-dalla kan hukunce-hukuncen zakkar fidda kai (zakkatul fitr) a musulunci
- Malamin addinin musuluncin ya yi muhimman bayanai kan mutanen da ya kamata a ba zakkar idan an fitar da ita
- Dr. Jabir Maihula ya bayyana muhimmancin tare da tattare da zakkar da kuma mutanen da ake fitar ma wa da ita a gidaje
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Sheikh Jabir Maihula ya yi bayani kan zakkar fidda kai (zakatul fitr) da hukunce-hukuncenta a musulunci.
Malamin addinin musuluncin ya bayyana yadda ake fitar da ita da waɗanda ya kamata a ba idan an tashi fitarwa.

Asali: Facebook
Sheikh Jabir Maihula ya yi bayanin ne dalla-dalla a cikin wani bidiyo da @el_uthmaan ya sanya a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamin ya kawo nassoshi na hadisi waɗanda suka yi magana kan zakkar fidda kai da yadda ake fitar da ita a musulunci.

Kara karanta wannan
"Ba yau aka fara ba," Gwamnatin Kano ta yi zazzafan martani kan kisan ƴan Arewa a Edo
Zakkar fidda kai dai zakka ce wacce ake fitarwa bayan an kammala azumin watan Ramadan, watau idan an sha ruwa.
Su wa aka wajabtawa fitar da zakkar fidda kai?
Sheikh Jabir Maihula ya kawo hadisin manzon Allah (SWA) wanda ya yi bayanin mutanen da aka wajabtawa fitar da zakkar fidda kai.
"Annabi (SWA) ya wajabta zakkatul fitr a kan ɗa da bawa, babba da ƙarami na musulunci. Ya wajabta sa'i ake badawa na dabino, sa'i na sha'ir, ko sa'i na abinci watau abincin da aka shekara ana ci."
- Sheikh Jabir Maihula
Su wa ake ba zakkar a karshen azumi?
Malamin ya bayyana cewa malamai sun yi saɓani kan mutanen da suka cancanci a ba su zakkar fidda kai.
Ya ce wasu malaman na ganin cewa duk waɗanda aka ce a ba zakka guda takwas da ke cikin Suratul Taubah duk su za a ba. Yayin da wasu na ganin daga miskinai da faƙirai kawai za a ba.
Menene amfanin zakkar?
Malamin ya bayyana cewa kamar yadda ya inganta a hadisi, zakkar tana da amfani guda biyu.
Na farko shi ne tana tsarkake mai azumi daga yasassar magana da ƙananan maganganu da ya yi. Na biyu kuma abinci ce ga miskinai.
Ya ce ana ba miskinai ne domin a ranar Sallah ba a son ana ganin Musulmai suna bara.
Ya ake fitar da zakatul fitr?
Sheikh Jabir Maihula ya bayyana cewa kowane Musulmi zai fitar da sa'i ɗaya ko mudu guda huɗu, ya ce dukkaninsu ana cika su ne kafin a bayar.
A cewarsa idan ya zamana babu sa'i ko mudu, sai mutum matsakaici - wanda ba babba ba kuma ba ƙarami ba, sai ya miƙa hannayensa guda biyu ya cikasu, su ne za su ba da mudu guda ɗaya.

Asali: Facebook
Wane mutum yake fitar da ita?
Ya bayyana cewa mutumin da yake da abin da zai ci a ranar Idi,.wanda ya rage shi ne nisabin abin da za a fitar.
"Mai gida yana fitar ma kowa a cikin gidansa, kowa yana fitar ma duk wanda yake ciyarwa. Har jariri idan akwai in dai har an haifi jaririn kafin rana ta faɗi a ranar azumi na ƙarshe, to za a fitar masa."
- Sheikh Jabir Maihula
Hukuncin rama Sallar Idi
A wani labarin kuma, mun kawo muku abin da addinin musulunci ya tanada kan wanda ya makara ko ya rasa Sallar Idi a ranar Sallah.
Marigayi Sheikh Ahmad ya taɓa amsa tambaya kan hakan, ya kawo bayanai kan abin da shari'a ta tanada dangane da rasa Sallar Idi.
Asali: Legit.ng