Sanatocin Arewa Sun Haɗa Kai, Sun Taso da Ƙarfi kan Abin da Aka Yi wa Ƴan Arewa a Edo
- Snaatacin Arewacin Najeriya sun taso da karfinsu, sun yi Allah wadai da kisan matafiya a jihar Edo da babbar murya
- Shugaban kungiyar sanatocin Arewa, Sanata Abdul'aziz Yar'adua ya bukaci hukumomin tsaro su zaƙulo duk masu hannu a wannan ɗanyen aiki
- Ya yabawa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu bisa matakin da ya ɗauka na fara bincike, ya ce hakan ya nuna gwamnatin tarayya ba za ta lamunta ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Edo - Kungiyar Sanatocin Arewa ta bayyana damuwa da alhini game da kisan gilla da aka yi wa wasu matafiya da ke hanyar zuwa Kano, a garin Uromi, na jihar Edo.
A cewar kungiyar, wannan mummunan lamari ya faru ne a ranar Alhamis, 27 ga watan Maris, 2025, aka hallaka matafiyan bisa zargin cewa su ‘yan garkuwa da mutane ne.

Asali: Facebook
Shugaban ƙungiyar, Sanata Abdul'aziz Yari (APC, Katsina ta Tsakiya) ne ya bayyana hakan a madadin sanatocin Arewa, kamar yadda Channels tv ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka kashe Hausawa a jihar Edo
A sanarwar da ya sa wa hannu, Sanata Abdulaziz ya ce an yi wa mutanen da ke hanyarsu ta komawa gida kallon ‘yan fashi, lamarin da ya kai ga kashe su ta mummunar hanya.
Abdul'aziz ya ce:
“Mu na cike da bakin ciki da firgici kan wannan kisan gilla da aka yi wa wasu ‘yan Najeriya a garin Uromi, Jihar Edo.
"Wadannan mutane, wadanda ke kan hanyarsu ta komawa Arewa, an yi musu kisan gilla bayan da aka yi musu kallon Fulani masu garkuwa da mutane.”
Sanatocin Arewa sun yi Allah wadai da kisan
Sanatocin Arewan sun bayyana kisan a matsayin cin zarafi da take hakkin dan Adam, sun bukaci gwamnatin Edo ta gudanar bincike cikin gaggawa don gano wadanda suka aikata wannan aika-aika.

Kara karanta wannan
Barau ya yi martani kan kisan 'yan Arewa a Edo, ya fadi hanyar da zai samo musu adalci
“Mun yi Allah wadai da babbar murya kan wannan danyen aiki wanda ya sabawa dokokin kasa da hakkin dan Adam.
"Muna kira ga gwamnatin jihar Edo da ta gaggauta gudanar da bincike domin hukunta duk wadanda suka aikata wannan ta’asa.”
- In ji sanatocin Arewa.

Asali: Twitter
Sanatocin Arewa sun yabi Bola Tinubu
Sanatocin sun kuma jinjinawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan umarnin da ya bayar na gudanar da bincike domin kamo masu laifi, wanda ya nuna za a yi adalci da kare haƙƙin mamatan.
“Mun yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa umarnin da ya bayar ga ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro na gudanar da bincike cikin gaggawa.
"Wannan mataki ya nuna cewa gwamnati ba za ta lamunci irin wannan rashin adalci ba," in ji su.
A karshe, kungiyar Sanatocin Arewa ta bukaci a tabbatar da ‘yancin kowane dan Najeriya kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Kara karanta wannan
Kungiyar Izalah ta yi maganar kisan ƴan Arewa a Edo, ta fadi hanyar dakile lamarin
Ta kuma yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su hada kai don hana aukuwar irin wannan lamarin a nan gaba, kamar yadda Punch ta kawo.
Gwamnatin Kano ta yi Allah wadai
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Kano ta nuna matuƙar ɓacin ranta kan kisan gillar da aka yi wa wasu maharba a jihar Edo.
Ta ce wannan danyen aiki da ya lakume rayukan akalla mutum 16, ya zama abin takaici da dole ne hukumomin tsaro da na shari’a su dauki matakin gaggawa
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng