Lauya Ya Mika Bukatu 7 ga Bola Tinubu da Gwamna kan Kisan Hausawa a Edo
- An bukaci gwamnatoci su fitar da bayani kan yawan mutanen da aka kashe, jikkata ko yi wa asarar dukiya a Edo
- ‘Yan Arewa sun nemi kamawa da hukunta duk masu hannu a kisan gillar da aka yi wa Hausawa matafiya
- An bukaci kafa kwamitin bincike da samar da sabuwar doka domin hana sake faruwar irin wannan lamari nan gaba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Kungiyoyi da fitattun ‘yan Arewa sun bukaci gaggauta daukar matakan bincike da hukunta wadanda suka kashe Hausawa a Edo.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu matasa sun dauki doka a hannunsu, suka hallaka wasu matafiya da ake zargi da dauke da makamai ba tare da sahihin bincike ba.

Source: Facebook
A wata sanarwa da lauya mai kare hakkin dan Adam, Barista Abba Hikima, ya wallafa a Facebook, an bukaci daukar matakan da suka dace domin tabbatar da adalci.
Bukatar gaggauta bincike da hukunta masu laifi
Sanarwar ta bukaci gwamnati ta fitar da cikakken bayani kan adadin mutanen da aka kashe, jikkata ko yi wa asarar dukiya a jihar Edo.
A cewar sanarwar:
"Gwamnati na da alhakin tabbatar da adalci ta hanyar bincike da hukunta duk wadanda ke da hannu a wannan kisan gilla,"
Haka nan an bukaci kafa kotu ta musamman da za ta gudanar da shari’a cikin gaggawa domin kada lamarin ya shafe kamar yadda aka saba.

Source: Facebook
Bukatar biyan diyya da tabbatar da tsaro
Sanarwar ta bukaci gwamnati ta biya diyya ga iyalan wadanda aka kashe tare da basu hakuri a hukumance domin kwantar da hankulan jama’a.
A cewarta:
"Dole ne a biya iyalan mamatan diyya tare da basu hakuri a hukumance domin hana yaduwar tashin hankali a tsakanin al’umma."
Baya ga haka, an bukaci samar da karin jami’an tsaro a yankunan Kudu domin kare rayuka da dukiyoyin matafiya daga irin wannan farmaki a nan gaba.
Bukatar sabuwar doka da kwamitin bincike
Sanarwar ta bukaci a samar da sabuwar doka da za ta tsaurara hukunci kan masu daukar doka a hannunsu domin hana irin wannan kisan gilla nan gaba.
Haka nan an bukaci kafa kwamitin bincike na musamman da zai kunshi wakilan Arewa domin tabbatar da cewa ba a shashantar da lamarin ba.
A cewar sanarwar:
"Kafa kwamitin bincike zai tabbatar da cewa ba a bari wannan lamari ya wuce ba, kuma zai hana sake aukuwar irin hakan a nan gaba."
Bukatun 7 da Abba Hikima suka gabatar
Lauya mai kare hakkin dan Adam, Abba Hikima ya lissafa jerin bukatun da ake bukata Bola Tinubu da gwamnatin Edo su yi kan lamarin:
1. Gwamnati ta fitar da cikakken bayani kan mutanen da aka kashe, jikkata ko yi wa asarar dukiya a Edo.

Kara karanta wannan
"Ba yau aka fara ba," Gwamnatin Kano ta yi zazzafan martani kan kisan ƴan Arewa a Edo
2. A gaggauta kama da hukunta duk masu hannu a wannan kisan, musamman 'yan banga
3. A samar da kotu ta musamman don shari’ar wadanda suka aikata kisan gillar.
4. Gwamnati ta biya diyya ga iyalan wadanda aka kashe tare da basu hakuri a hukumance.
5. A kara samar da jami’an tsaro a yankunan kudu domin kare matafiya da direbobi.
6. A samar da sabuwar doka da za ta tsaurara hukunci kan masu daukar doka a hannu.
7. A kafa kwamitin bincike na musamman da zai kunshi wakilan Arewa domin tabbatar da an yi adalci.
An kama wadanda suka kashe Hausawa a Edo
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sanda ta kama wasu daga cikin wadanda suka kashe 'yan Arewa a jihar Edo.
Sufeton 'yan sanda ya tabbatar da cewa za a yi adalci wajen hukunta duk wanda aka samu da hannu a cikin aikata kisan gillar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

