"Abin Tausayi": An Ji Ainihin Yadda Aka Kashe Ƴan Arewa a Jihar Edo, Mutum 5 Suka Tsira

"Abin Tausayi": An Ji Ainihin Yadda Aka Kashe Ƴan Arewa a Jihar Edo, Mutum 5 Suka Tsira

  • Wani dattijo ɗan asalin jihar Kano, Ɗayyabu Yahaya ya yi bayanin yadda aka tare su a Uromi, aka kashe ƴan uwansa a Edo
  • Ɗayyabu na ɗaya daga cikin mafarautan da aka tare a Uromi, inda ake zagin mutanen garin sun kashe 16 daga cikinsu
  • Ya ce su 27 suka taso daga Fatakwal za su dawo Kano kuma ba su gamu da wata matsala ba sai da suka shigo jihar Edo

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - A jiya Juma'a ne aka samu labarin kisan wasu mafarauta ƴan Arewa da suka taso daga Fatakwal za su dawo gida domin yin shagalin sallah.

Sai dai daga cikin mutanen su 27, akalla mutum biyar ne suka tsira, wasu mutum biyu na kwance a asibiti, yayin da ake zargin an kashe mutane 20 a garin Uromi na jihar Edo.

Kara karanta wannan

Barau ya yi martani kan kisan 'yan Arewa a Edo, ya fadi hanyar da zai samo musu adalci

Yan sanda.
Daya daga cikin waɗanda suka tsira ya yi bayanin yadda aka kashe ƴan uwansa a Edo Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Menene ainihin abin da ya faru a Edo?

Ɗaya daga cikin wadanda suka tsira daga wannan lamari ya yi bayanin yadda aka kashe ƴan uwansa a wani bidiyo da Yahaya Abubakar ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dattijon da ya bayyana sunansa da Ɗayyabu Yahaya, ya fito ne daga ƙaramar hukumar Bunkure ta jihar Kano, ya ce sun taho ne da nufin zuwa gida su yi sallah.

Da yake ba da labarin haƙiƙanin abin da ya faru, mutumin wanda alamu suka nuna ya na cikin damuwa, ya ce:

"Tun da muka taso daga Fatakwal ba mu samu matsalar komai ba sai da muka zo Uromi, a nan ne ƴan bijilanti suka tare mu. Ni ina gaban mota, sun ce direba ya sauƙo amma bai sauka ba.
"Sai suka ce na sama su sauko, tun da suka fara saukowa suka fara dukansu, suka tara su wuri ɗaya, suka ci gaba da bugunsu a ka."

Kara karanta wannan

An fara kama mutanen da suka kashe 'yan Arewa a Edo

Da gaske an kama su da bindigogi?

Da aka tambaye shi kan bindigun da aka ce an kama su da su, mutumin ya bayyana cewa babu abin da aka samu sai tsunmokara da manjar da suka sayo.

"Eh sun bincike mu, ƴan bijilanti sun zo da wuƙakensu, suka rika buɗe kayanmu amma ba abin da suka samu daga tsunmokarai sai manja. Da suka ga bindigogin mu na maharba sai suka ce mu ƴan garkuwa ne.
"Taya ɗan garkuwa zai taho tare da kare tun daga Fatakwal zuwa Kano? Bindigogin duk na maharba ne kuma muna da takardu," in ji shi.
Taswirar Edo.
Yadda aka kashe mafarauta a Uromi Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ƴan Arewa nawa aka kashe a jihar Edo?

Dangane da adadin mutanen da aka kashe kuwa, Ɗayyabu ya ce su 27 ne suka taho a motar amma su biyar ne suka tsira da rayuwarsu.

"Mu 27 ne a motar, ban san mutum nawa aka kashe ba amma mu 5 muka rage a raye, an ce akwai mutum biyu a asibiti."

Kara karanta wannan

"Ba yau aka fara ba," Gwamnatin Kano ta yi zazzafan martani kan kisan ƴan Arewa a Edo

Pantami ya saukaka wa jami'an tsaro aiki

A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Isa Pantami ya yi Allah wadai da kisan matagiya a Edo, ya buƙaci hukumomi su kama dukan masu hannu a lamarin.

Tsohon ministan sadarwa ya jero hanyoyi 3 na fasaha da za a iya amfani da su wajen cafke waɗanda suka yi wannan aika-aika.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262