An Fara Kama Mutanen da Suka Kashe 'Yan Arewa a Edo
- Sufeto Janar na ‘yan sanda ya la’anci kisan wasu matafiya da aka yi a jihar Edo bayan jami'an tsaro sun kama mutane 14
- Rahotanni sun nuna cewa an umarci sashen bincike na FCID da ya dauki alhakin gudanar da cikakken bincike kan lamarin
- Rundunar 'yan sanda ta gargadi al’umma kan mallakar makamai ba bisa ka’ida ba tare da kira a kauce daukar doka a hannu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Adeolu Egbetokun, ya la’anci yadda wasu matasa a Edo suka dauki doka a hannu suka kashe wasu matafiya bisa zargin su da garkuwa da mutane.
Matafiyan da lamarin ya shafa sun bayyana kansu a matsayin mafarauta kuma su na kan hanyar Uromi-Obajana zuwa Kano a cikin wata mota a lokacin da aka tare su.

Kara karanta wannan
Kungiyar Izalah ta yi maganar kisan ƴan Arewa a Edo, ta fadi hanyar dakile lamarin

Asali: Facebook
Legit ta tattaro bayanin da IGP Kayode ya yi ne a cikin wani sako da rundunar 'yan sanda ta wallafa a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kama wadanda suka kashe 'yan Arewa a Edo
Bayan faruwar lamarin, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta baza jami’anta don dawo da doka da oda a yankin.
A yanzu haka, mutane 14 sun shiga hannu yayin da ake ci gaba da kokarin cafke sauran da suka tsere.
A cewar sanarwar da rundunar ta fitar:
"Muna ci gaba da kokarin kama duk wadanda suka aikata wannan aika-aika. ‘Yan sanda za su tabbatar da cewa an yi wa kowa adalci kuma an hukunta masu laifi.”
Sufeto Janar din ya ce za a hukunta duk wanda aka samu da hannu a wannan aika-aika domin tabbatar da cewa doka ta yi aikinta.
Edo: Matakin da 'yan sanda suka dauka
Sufeto Janar na ‘yan sanda ya umarci Mataimakin Sufeto Janar da ke kula da sashen binciken manyan laifuffuka na kasa (FCID), Sadiq Abubakar, da ya karbi ragamar binciken lamarin.
Ya ce binciken zai kasance cikakke, adali kuma ba tare da bata lokaci ba, domin tabbatar da cewa an hukunta wadanda suka aikata laifin.
A cewarsa:
"Ba za mu lamunci kisan gilla ko daukar doka a hannu ba. Kowa zai fuskanci hukunci idan aka same shi da laifi.”
Gargadin 'Yan sanda kan mallakar bindiga
Rundunar ‘yan sanda ta sake jaddada cewa mallakar bindiga ba bisa ka’ida ba babban laifi ne a Najeriya.
Ta gargadi duk wani da ke da makamai ba tare da izini ba da ya kai su ofishin ‘yan sanda mafi kusa don mika su ko kuma ya bi hanyoyin da doka ta tanada don samun lasisi.

Asali: Twitter
Rundunar ta kuma yi kira ga al’umma da su guji daukar doka a hannunsu, su kuma rika kai rahoto ga hukumomin da abin ya shafa idan sun ga wani abu da ke daure kai.
Yanzu haka, ana sa ido kan yadda binciken za su kammala, domin tabbatar da cewa an yi adalci ga wadanda lamarin ya shafa.
Maganar Pantami kan kisan Hausawa a Edo
A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Isa Ali Pantami ya yi magana kan kisan 'yan Arewa a jihar Edo da sunan cewa masu laifi ne.
Sheikh Pantami ya ce lamarin abin Allah wadai ne tare da kira ga jami'an tsaro su tabbbatar da cafke wadanda suka aikata laifin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng