Atiku Ya Bi Layin Kwankwaso game da Mummunan Kisan da Aka Yi Wa Ƴan Arewa a Edo
- Atiku Abubakar ya yi Allah wadai da kisan rashin imani da aka yi wa wasu mafarauta ƴan Arewa a garin Uromi da ke jihar Edo
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bukaci hukumomin tsaro su gudanar da bincike a bayyane kuma su tabbatar an hukunta masu laifi
- Wazirin Adamawa ya kuma mika sakon ta'aziyya ga iyalai da ƴan uwan waɗanda suka rasa rayukansu a wannan mummunan al'amarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi Allah wadai tare da jimamin kisan gillar da aka yi wa mafarauta ƴan Arewa a Jihar Edo.
Atiku ya yi kira ga hukumomin Najeriya su gudanar da cikakken bincike domin doka ta yi aiki a kan waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki.

Asali: Facebook
Wazirin Adamawa ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X yau Juma'a, 28 ga watan Maris, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin sanarwa da ya fitar, Atiku ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan da duka wadanda suka rasa ‘yan uwansu a wannan mummunan lamari.
Yadda aka kashe ƴan Arewa a Edo
Tun farko, Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa wasu matasa sun hallaka matafiya ƴan Arewa 16 yayin da suke hanyar zuwa Kano domin yin sallah a gida.
An tattaro cewa lamarin ya faru ne a garin Uromi da ke yankin ƙaramar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas a jihar Edo, yankin Kudu maso Kudancin Najeriya.
Jim kaɗan bayan haka, Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo ya ba da umarnin fara bincike kan lamarin, kuma ya roƙi al'umma su kwantar da hankula.
Da yake mayar da martani, Atiku Abubakar ya nuna bacin ransa kan wannan mummunan lamarin, ya kuma nemi a yi wa waɗanda aka kashe adalci.

Asali: Facebook
Atiku Abubakar ya buƙaci a yi bincike

Kara karanta wannan
Kisan 'rashin imani' da aka yi wa 'yan Arewa ya tada ƙura, Kwankwaso ya maida martani
"Na yi matukar jimami da alhinin rahotannin kisan gillar da aka yi wa wasu mafarauta ƴan Arewa a Jihar Edo. Ina mika ta'aziyyata ga iyalansu da duka masoyansu.
"Wannan mummunan lamari na bukatar cikakken bincike kuma a bayyane, adali kuma ba tare da son rai ba, domin a gano gaskiya kuma a tabbatar da cewa wadanda suka aikata laifin sun fuskanci hukunci.
"Kare rayukan jama'a shi ne abu na farko, kuma ina kira ga hukumomi da su dauki matakan gaggawa don hana sake aukuwar irin wannan lamari na daukar doka a hannu.
"Ba wai adalci kaɗai ake bukata ba, dole mutane su gane cewa an yi adalci kan wannan lamari domin yardar da suka yi wa jami'an tsaro ta dawo.
- In ji Atiku Abubakar.
Kwankwaso ya yi magana kan kisa ƴan Arewa
A baya, kun ji cewa madugun Kwankwasiya ya yi Allah wadai da mummunan kisan gillar da wasu mutanen gari suka yi wa ƴan Arewa a jihar Edo.
Rabiu Kwankwaso ya bukaci hukumomin tsaro da su yi cikakken bincike kan lamarin tare da tabbatar da an hukunta wadanda suka aikata wannan ta’asa.
Asali: Legit.ng