Tirkashi: Wasu Fastoci 2 da 'Yar Fasto Sun Fice daga Kiristanci, Sun Fadi Dalili

Tirkashi: Wasu Fastoci 2 da 'Yar Fasto Sun Fice daga Kiristanci, Sun Fadi Dalili

  • Tun daga karni na 15, Kiristanci ya zama babban addini a Najeriya, inda ke da manyan mazhabobi masu yawan mabiya.
  • Duk da cewa mutane da dama suna ci gaba da rungumar Kiristanci, wasu sun rasa imani bayan shekaru da dama na ibada da sadaukarwa.
  • A wannan labari, Legit.ng ta nazarci labaran wasu tsoffin Kiristoci uku da suka bayyana dalilin da ya sa suka bar addinin gaba ɗaya.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bayan shekaru da dama suna ibada da imani mai karfi ga Ubangiji, wasu ‘yan Najeriya sun yanke shawarar barin addinin Kiristanci bayan bincike da tunani mai zurfi.

Kamar yadda suka sanar a lokacin da suka rungumi Kiristanci, haka suka fito a kafafen sada zumunta suka sanar da ficewarsu daga addinin ba tare da damuwa da martanin mutane ba.

Kara karanta wannan

Sheikh Pantami ya jero hanyoyi 3 da za a kama waɗanda suka kashe yan Arewa a Edo

Tsofaffin Kiritoci da suka bar addinin Kirista sun fadi abin da ya sa suka bar addinin
Kiristoci uku sun fice daga addinin Kiristanci bayan shekaru a ciki. Hoto: Abraham Daniel, Genesis Eririoma, TikTok/@awakenwithshally
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattara bayanai kan wasu tsofaffin Kiristoci uku a Najeriya da suka bar addinin da dalilan da suka sa suka yanke wannan shawara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin wasu tsofaffin Kiristoci na barin addinin

1. Abraham Daniel, tsohon fasto

Bayan sama da shekaru goma yana mamba kuma fasto a cocin Dunamis ta Dr. Pastor Enenche, Abraham Daniel ya daina imani da Kiristanci, inda ya sanar da abokansa a Facebook cewa yanzu shi mutum ne mai kore wanzuwar Ubangiji.

A wata hira da Legit.ng, Abraham ya bayyana abubuwan da ya gano da suka sa ya yanke wannan shawara.

A cewarsa:

"A duk matakan rayuwata, na gano cewa akwai tambayoyin da na gagara samun amsarsu, babu lissafi ko hujjoji na kama hankali a akidar da nake bi.
"Na ga yadda mambobi ke yin addu’a da azumi, amma matsalolinsu sun gaza karewa. Na mallaki gidaje da motoci a matsayi na na fasto, amma kullum mabiya na cikin bukata suke.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa sun haɗa kai kan kisan Hausawa a Edo, sun shawarci al'umma

"A duk lokacin da aka kammala taron zarkake ruhin mutane, na kan ga fuskokin wadanda suka zo taron cike da takaici. Idan Allah na nan, me ya sa dole sai mun kare mu'ujizarsa?"

Abraham ya ce ya yi murabus daga cocin Dunamis tun a shekarar 2018. Duk da caccakar da yake fuskanta a intanet, wasu sun goyi bayansa tare da hada masa tallafin kudi.

2. Genesis Eririoma, tsohon fasto

A cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Genesis Eririoma ya bayyana dalilin da ya sa ya bar addinin Kiristanci.

A cewarsa, ya daina imani da bishara ne saboda ya fara shakkar gaskiyarta.

Genesis Eririoma ya ce:

"Ba wai na bar Kiristanci saboda takaici ko fushi ba. A'a, ma bar addinin ne a lokacin da nake gab da fara samun kudi daga gare shi.
"Na kashe dukiyata wajen taimakawa mutane da yada bisharar Yesu har sai da na gano cewa bisharar ba gaskiya ba ce, rudani ne kawai a ciki."

Kara karanta wannan

Kano: Abin da Reno Omokri ya ce bayan ƙone Hausawa a Edo, ya shawarci ƴan Arewa

Bayanan shafinsa na Facebook sun nuna cewa yanzu yana zaune a Abuja. Duk da bai bayyana takamaiman lokacin da ya bar Kiristanci ba, amma yana wallafa labarin rayuwarsa a tashar YouTube mai suna Africa Enlightenment Centre tun daga 2024.

3. Shalom, ‘yar fasto

Wata ‘yar fasto mai suna Shalom ta tayar da kura a intanet bayan ta bayyana abubuwan da ta fahimta da suka sa ta bar addinin Kiristanci.

A cikin wani rubutu da ta wallafa, wanda daga baya ta goge, ta ce ta gane cewa addinin Kiristanci, wani wankin kwakwalwa ne da ake hana mutum iko da kansa.

A cewarta:

"Lokacin da na fara tantama kan imani na da kalubalantar tunanin da aka gina min tun ina karama, sai na tsinci kaina a cikin tsananin mamaki da yanayi mai tsoratarwa.
"Na fuskanci matsananciyar rudani na tunani, amma daga baya na fahimci gaskiya. Addini wata hanya ce kawai aka kirkira don tilasta wa mutum mika wuya ga wasu."

Kara karanta wannan

An kona 'yan Arewa kurmus suna dawowa gida hutun sallah a jihar Edo

Matashiyar 'yar shekara 18 ta Musulunta

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wata budurwar, wacce aka fi sani da Blessing, ta sauya sunanta zuwa Khadijah bayan karɓar Musulunci.

Da muka tattara martanin jama'a a kan musuluntar Khadijah, an fahimci cewa yawancin mutanen suna yi mata maraba ne da shigowa addinin musulunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.