Kisan 'Rashin Imani' da Aka Yi Wa 'Yan Arewa Ya Tada Ƙura, Kwankwaso Ya Maida Martani
- Tsohon dan takarar shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna ɓacin ransa kan kisan gillar da aka yi wa ƴan Arewa a jihar Edo
- Kwankwaso ya bukaci hukumomi su gaggauta gudanar da bincike kuma su tabbata an hukunta duk wani mai hannu a ɗanyen aikin
- Wannan na zuwa ne bayan wasu matasa da ƴan sa-kai sun tare matafiya da ke hanyar zuwa Kano, suka masu kisan gilla tare da ƙone su ƙurmus
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Jagoran NNPP na kasa kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi tir da kisan gillar da aka yi wa ƴan Arewa a jihar Edo.
Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, ya bayyana damuwarsa kan kisan gillar da aka yi wa matafiya 16 suna hanyar zuwa Kano domin yin sallah.

Asali: Twitter
Kwankwaso ya yi martani kan mummunan lamarin ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X yau Juma'a, 28 ga watan Maris, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda matasa suka kashe ƴan Arewa
Legit Hausa ta kawo maku rahoton yadda ƴan sa-kai da matasa suka kashe matafiyan, kana suka ƙona su da tayoyi a garin Uromi, karamar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas.
Lamarin ya faru ne lokacin da ƴan sa-kai suka tare babbar motar da matafiyar ke ciki, suka kashe su sannan suka banka masu wuta.
An tattaro cewa jami'an tsaron sun samu mutanen ɗauke da bindigu irin na mafarauta, hakan ya sa suka yi zargin wai ƴan fashin daji ne ba tare da cikakken bincike ba.
Tuni dai Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo ya ba da umarnin gudanar da bincike domin cafke duk mai hannu a aikata wannan ɗanyen aiki.
Kwankwaso ya nuna ɓacin ransa kan lamarin
Kwankwaso ya bayyana cewa wannan lamari, wanda ya faru a ranar 28 ga watan Maris, 2025, babban abin bakin ciki ne da ke kara nuna munin ɗaukar doka a hannu.
Jagoran ɗarikar Kwankwasiyya ya ƙara da cewa cewa kowane dan kasa ya na da ‘yancin yin tafiye-tafiye cikin ‘yanci ba tare da fuskantar barazana ko tsangwama ba.

Asali: Facebook
Sanata Kwankwaso ya nemi a yi bincike
Saboda haka, tsohon gwamnan ya bukaci hukumomin tsaro da su yi cikakken bincike kan lamarin tare da tabbatar da cewa an hukunta wadanda suka aikata wannan ta’asa.
"Ina kira ga hukumomin da wannan abu ya shafa su gudanar da bincike kan abin da ya faru kuma su tabbatar da cewa duk mai hannu ya fuskanci hukunci."
- In ji Kwankwaso.
A karshe, ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, Gwamnatin Jihar Kano, da kuma sauran jihohin da abin ya shafa, tare da addu’ar Allah ya ji kan su da rahama.
Gwamnan Edo ya sa a fara bincike
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Monday Okpebholo ya ba da umarnin gudanar da bincike kan kisan gillan da aka yi wa matafiya a Uromi.
Gwamnan ya bukaci jama’a su zauna lafiya, yana mai tabbatar wa Hausawa da ke Uromi cewa jami’an tsaro sun dauki mataki domin kare rayukansu da dukiyoyinsu.
Asali: Legit.ng