Za a Ladabtar da Dalibar da Ta Yada Bidiyon da ake Yi wa Matar Tinubu Wulakanci
- Makarantar koyar da ungozoma ta jihar Delta ta aika wa daliba Osato Edobor da wasikar ladabtarwa
- An zargi dalibar da wallafa bidiyo ba tare da izini ba yayin ziyarar Uwargidan Shugaban Kasa, Oluremi Tinubu.
- Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce, inda wasu ke danganta abin da daliban suka yi da fushin jama’a kan matsin tattalin arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Delta - Hukumar makarantar koyar da ungozoma ta Delta ta dauki matakin ladabtarwa kan wata daliba mai suna Osato Edobor bisa zargin wallafa bidiyo ba tare da izini ba.
Dalibar mai suna Osato Edobor ta dauki bidiyon ne yayin ziyarar Uwargidan Shugaban Kasa, Oluremi Tinubu jihar Delta.

Asali: Twitter
Wata takarda da makarantar ta aika wa Edobor, wacce dan jaridar Arise News, Oseni Rufai, ya wallafa a shafinsa na X a ranar Juma’a, ta tabbatar da matakin da aka dauka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin takardar, shugaban makarantar, Evbodaghe Rita Ogonne, ta ce dalibar ta aikata abin da ya saba wa dokokin makaranta, don haka an bukaci kare kanta cikin sa’o’i 24.
An zargi daliba da karya dokar makaranta
An ce Edobor ta wallafa bidiyo ana rera waka a lokacin da ake tarbar Uwargidan Shugaban Kasa a Dome Event Centre da ke Asaba.
Taron dai na cikin shirin Renewed Hope Initiative Health Programme, inda aka raba kayan aiki ga ungozoma 10,000 a yankin Kudu maso Kudu.
Jaridar Punch ta wallafa cewa hukumar makarantar ta ce hakan karya doka ne da ke kunshe a kundin ladabtar da dalibai na makarantar, shafi na 21, doka 8.
Ce-ce-Ku-ce bayan wallafar bidiyon
Bayan wallafar bidiyon, jama’a da dama sun fara tofa albarkacin bakinsu, musamman ganin yadda wasu dalibai suka nuna kin amincewa da Uwargidan Shugaban Kasa.
Lokacin da mai gabatar da taron ya kira Remi Tinubu da uwar kowa, wasu daga cikin daliban sun mayar da martani da cewa "Ba uwar mu bace," suna kin karbar wannan matsayin da aka bata.
Wannan abu ya kara janyo ce-ce-ku-ce, inda mutane da dama suka danganta lamarin da fushin jama’a kan matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa a mulkin Shugaba Bola Tinubu.

Asali: Twitter
Gwamna da sarakuna sun girmama Remi
Duk da haka, a yayin taron, Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya yaba da kokarin Uwargidan Shugaban Kasa, yana mai cewa an samu ci gaba a fannin lafiya karkashin shirin RHI.
Haka kuma, Oluremi Tinubu ta gana da sarakunan gargajiya a majalisar sarakunan jihar, ciki har da Orodje na Okpe, Janar Felix Mujak Peruo (Mai Ritaya).
Ana ci gaba da jira a ga irin matakin da makaranatar za ta dauka kan dalibar da aka tuhuma, da kuma yadda wannan lamari zai shafi fahimtar juna tsakanin gwamnati da ‘yan Najeriya.
Gwamnati ya yi wa daliba afuwa
Rahotanni da suka fito daga baya sun nuna cewa gwamnatin jihar ta yi afuwa wa dalibar da ta yada bidiyon.
Kwamishinan lafiya na jihar ya bukaci makarantar ta janye tuhumar da ta yi wa dalibar kamar yadda gwamnatin Edo ta wallafa a X.
Akpabio ya ce APC za ta kwace Kano a 2027
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio ya yi magana kan shirin da APC ta ke yi na karbar mulki a Kano a zaben 2027.
Sanata Godswill Akpabio ya ce su na da tabbacin cewa APC za ta kwace mulkin jihar Kano a hannun NNPP lura da yadda suke da manyan 'yan jam'iyya a jihar.
Asali: Legit.ng