Ramadan: Wike Ya Tattaro Kungiyoyin Addini a Abuja, Ya Raba Buhunan Shinkafa 10, 000
- Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya raba buhunan shinkafa 10,000 ga kungiyoyin addini da makarantu mutane masu bukata ta musamman
- Wike, ta bakin shugaban ma’aikatansa, Chidi Amadi, ya bukaci shugabannin addini su tabbatar da adalci wajen rabon tallafin ga mabukata
- Shugabannin addini, sun gode wa ministan bisa wannan tallafi, inda suka ce zai rage radadin mutane a wannan wata na Ramadan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Ministan babban birnin tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya raba buhunan shinkafa 10,000 ga kungiyoyin addini da makarantu alfarmar watan Ramadan.
Wike, wanda shugaban ma’aikatansa, Chidi Amadi, ya wakilta a wurin taron a Gwagwalada, ya jaddada muhimmancin ba al'umma tallafi, musamman a watan azumin Ramadan.

Asali: Facebook
Wike ya tattara kungiyoyin addinai a Abuja
A cewar rahoton Punch, Amadi ya ce wannan tallafin ya nuna jajircewar Wike wajen tallafawa al’ummomin addini da masu bukata ta musamman a Abuja.

Kara karanta wannan
Jerin kura kurai 5 da musulmi ke yi a ranar ƙaramar sallah da yadda za a kauce masu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amadi ya ce ministan babban birnin tarayyar ya bukaci shugabannin addini da su tabbatar da adalci wajen rarraba kayan abincin.
“Ramadan wata ne na musamman a rayuwar ‘yan uwanmu Musulmi. Wata ne da ke da muhimmanci matuka a addinin Islama.
“Ana yin azumi, addu’a da bayar da sadaka a wannan lokaci. Saboda haka, Mai girma minista ya ga dacewar tallafawa Musulmi ta hanyar bayar da tallafi."
- Chidi Amadi.
Wike ya raba tallafin buhunan shinkafa 10,000
Tribune ta rahoto Chidi Amadi ya shaidawa mahalarta taron cewa:
“Ya kuma tanadi buhunan shinkafa 10,000 domin rabawa shugabannin addini, kungiyoyin addini da sauran rukunin jama’a.
“Ina kira ga shugabannin addini da kungiyoyi da su tabbatar da cewa an raba kayan ga wadanda suka dace.
"Wannan lokaci ne da ya dace mu tallafa wa mabukata da marasa galihu. Wannan shinkafa, buhu 10,000 za ta taimaka wajen isar da tallafi ga mutane da dama."
Shugaban makarantar makafi da bebaye, Alhaji Abdulrazzaq Ademola, ya gode wa minista bisa wannan tallafi, inda ya ce hakan zai rage radadin tsadar abinci, musamman ga marasa galihu.
“Muna matukar godiya da wannan kyauta. Mai girma minista ya nuna kishin kasa da tausayi. Wannan tallafi ya zo a lokacin da abinci ke kara tsada, lallai mabukata za su amfana."
- Alhaji Abdulrazzaq.
Limami ya yi wa Nyesom Wike addu'a
Babban limamin fadar ministan Abuja, Imam Lawal Mustapha, wanda ya karbi kayan a madadin shugabannin addini, ya gode bisa wannan kyauta, tare da kira ga shugabanni su rika tallafawa al’ummarsu.
“Wannan kyauta alama ce ta jagoranci na kwarai. A iya saninmu, alheri ba ya faduwa kasa banza. Muna addu’a Allah ya kara wa minista nasara da kariya.
"Shugabanni su rika tallafawa jama’a, domin irin wannan shiri na taimako shi ne babban abin da ke nuna tausayin shugaba ga al'ummarsa."

Kara karanta wannan
"Ba ni da hannu," Sheikh Sulaimon ya fashe da kuka a tafsirin Ramadan, ya rantse da Alƙur'ani
- Imam Lawal.
Alhaji Aminu Bayero ya gana da Wike
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Mai Martaba Alhaji Aminu Ado Bayero ya hadu da ministan Abuja, Nyesom Wike, a wata ganawa kafin bikin yaye daliban jami'ar Calabar.
Ba a bayyana batutuwan da suka tattauna ba, amma an hango su suna magana. Amma an rahoto cewa jami'ar ta karrama Wike da wasu manyan mutane a kasar nan.
Asali: Legit.ng