Ana Wata ga Wata: Natasha Ta Karbi N500m a Hannun Akpabio? An Ji Gaskiyar Zance
- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta fito ta yi martani kan zargin ta karɓi N500m a hannun shugaban majalisar dattawa
- Natasha ta bayyana cewa ko kaɗan ba ta taɓa karɓar N500m ko wasu kuɗi a hannun Sanata Godswill Akpabio ba
- Ta bayyana jita-jitar a matsayin tsantsagwaron ƙarya, ta buƙaci hukumomin tsaro su yi bincike domin zaƙulo masu yaɗa ta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ta yi magana kan zargin ta karɓi Naira miliyan 500 daga hannun shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.
Sanata Natasha wacce aka dakatar ta ƙaryata iƙirarin cewa ta karɓi kuɗaɗen daga hannun shugaban majalisar dattawa.

Asali: Facebook
Natasha ta musanta zargin ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, 26 ga watan Maris 2025, cewar rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Natasha tace kan karɓar N500m?
Sanatar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta bayyana wannan iƙirarin a matsayin tsagwaronta da aka ƙirƙira don yaudarar jama’a da ɓata mata suna.
Natasha ta musanta karɓar kuɗaɗen, har ta jaddada cewa babu wani abu makamancin hakan da ya faru.
"Bari na fayyace cewa, ban taɓa karɓar Naira miliyan 500 ko kowane irin kuɗi daga hannun Sanata Akpabio ba."
"Ban taɓa yin wata magana da ke nuni da hakan ba. Wannan ƙarya ce da aka ƙirƙira da gangan domin haifar da cece-kuce."
- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan
Sanatar ta nuna damuwa kan yadda jita-jita da labaran ƙarya ke yawaita, musamman waɗanda ake ƙirƙira don dalilai na siyasa, tare da kira ga jama’a da su yi watsi da wannan iƙirari.
Ta yi gargaɗin cewa yaɗa ƙarya don cimma wata manufa ta siyasa, babbar barazana ce ga dimokuraɗiyyar ƙasar nan.

Asali: Twitter
"Abin takaici ne yadda wasu mutane ke ƙirƙirar irin wannan ƙarya ba tare da wani shakku ba. Ina kira ga ƴan Najeriya da su tabbatar da sahihancin kowane labari kafin su yarda da shi ko su yaɗa shi."

Kara karanta wannan
Natasha: Fada ya barke a majalisa, an yi kaca kaca tsakanin sanata da tsohuwar minista
- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan
Sanata Natasha ta buƙaci a kawo hujja
Sanata Natasha ta kuma ƙalubalanci waɗanda ke yaɗa wannan jita-jitar da su gabatar da wata hujja mai gamsarwa da ke tabbatar da iƙirarinsu.
"Irin waɗannan ƙarya ba abin da za a amince da ita ba ne. Na fi maida hankali kan hidimtawa mutanena da gaskiya da riƙon amana."
- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan
Sanatar ta kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su binciki asalin wannan labari na ƙarya tare da ɗaukar matakin da ya dace kan waɗanda suka ɗauki nauyinsa.
Shirin yi wa Natasha kiranye ya je INEC
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), ta bayyana kuskuren da masu yunƙurin yi wa Sanata Natasha Akpoti kiranye suka yi.
INEC ta bayyana cewa masu shigar da ƙorafin neman yi wa sanatar kiranye, ba su bayar da adireshinsu ba yadda ya kamata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng