Natasha: Fada Ya Barke a Majalisa, an Yi Kaca Kaca Tsakanin Sanata da Tsohuwar Minista

Natasha: Fada Ya Barke a Majalisa, an Yi Kaca Kaca Tsakanin Sanata da Tsohuwar Minista

  • Abubuwa sun rincaɓe inda aka yi kamar za a ba hammata iska a majalisar dattawa a ranar Talata, 25 ga watan Maris 2025
  • Lamarin ya auku ne a yayin da kwamitin majalisar dattawa kan ɗa'a da karɓar ƙorafe-ƙorafe ya fara zamansa a birnin Abuja
  • A yayin zaman, cacar baki ta kaure a tsakanin Sanata Onyekachi Nwaebonyi da tsohuwar ministar ilmi, Obi Ezekwesili
  • An fara jin ta-cewar jama'a kan ƙorafin da Sanata Natasha Akpoti ta shigar, Nwaebonyi ya ce Obi ta nemi ya rufe baki
  • Cacar bakin ta yi ƙamari inda har ta kai ga zage-zage da gayawa juna kalamai masu kaushi a tsakanin manyan mutanen

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - An samu ɓarkewar hayaniya a majalisar dattawa a ranar Talata, 25 ga watan Maris 2025.

Lamarin ya auku ne a yayin da kwamitin majalisar dattawa kan ɗa'a da karɓar ƙorafe-ƙorafe ya fara zamansa kan ƙorafin da Sanata Natasha Akpoti ta shigar.

Kara karanta wannan

Yadda Atiku, Peter Obi da El Rufai za su zaɓi wanda zai gwabza da Tinubu a 2027

Hayaniya ta barke a majalisar dattawa
An yi hayaniya a majalisar dattawa Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Rigima ta ɓarke a majalisar dattawa

A wani bidiyo da tashar News Central Tv ta sanya a shafin X, an nuna Sanata Onyekachi Nwebonyi na jihar Ebonyi da tsohuwar ministar Ilimi, Obi Ezekwesili suna cacar baki mai zafi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin bidiyon an ga manyan mutanen biyu suna gayawa juna maganganu cikin kalmomin zagi da cin fuska.

Kwamitin dai ya fara gudanar da bincike ne kan zargin cin zarafi ta hanyar lalata da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ta shigar kan Godswill Akpabio.

A yayin zaman, abubuwa sun rincaɓe inda manyan mutanen biyu suka yi cacar baki mai zafi a tsakaninsu.

Ana iya kallon bidiyon a ƙasa:

Natasha ta yi zarge-zarge kan Akpabio

Idan ba a manta ba dai, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta zargi shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da ci mata zarafi ta hanyar yunƙurin yin lalata da ita.

Zargin ya biyo bayan cece-kuce kan sauya mata kujerar zama da shugaban majalisar dattawan ya yi.

Kara karanta wannan

"Ta kai ƙorafi LPDC," Natasha ta sake kinkimo rigima, ta zargi Sanata da 'rashin ɗa'a'

Daga bisani, an dakatar da ita daga majalisar har na tsawon watanni shida bisa zargin rashin ɗa'a.

Akpoti-Uduaghan ta yi magana a taron ƙungiyar IPU a ranar 11 ga Maris kan dakatarwar da aka yi mata, inda ta bayyana cewa an yi hakan ne saboda ta zargi Akpabio da yunƙurin ci mata zarafi.

Bayan haka, ta yi jerin hirarraki da kafofin yaɗa labarai na ƙasashen wajen kan zargin da take yi wa Akpabio.

The Cable ta rahoto Sanata Onyekachi Nwaebonyi ya na cewa ya fusata ne saboda 'yar siyasar ta nemi ya yi gum da bakinsa.

Karanta wasu labaran kan Natasha, Akpabio

Lauyan Natasha ya yi sabon zargi

A wani labarin kuma, kun ji cewa lauyan da ke kare Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Victor Giwa, ya zargi gwamnatin jihar Kogi.

Kara karanta wannan

Sanatan Bauchi ya ba mutane kunya da azumi, bidiyosa yana rabon kuɗi ya shiga intanet

Victor Giwa ya yi zargin cewa gwamnatin jihar Kogi ce ta ɗauki nauyin yunƙurin raba Sanafa Natasha da kujerarta ta majalisar dattawa.

Ya yi zargin cewa gwamntin na ɗaukar nauyin shirin yi wa sanatar kiranye ne, saboda ta kasance ƴar jam'iyyar adawa ta PDP.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng