An Hango Alkalin da Ya Jika wa Fubara Aiki a Rivers Zaune da Wike, Kotu Ta Yi Bayani
- Kotun Koli ta magantu kan zargin da ake yi cewa Emmanuel Agim ya halarci taron karramawar jami’ar UNICAL tare da Ministan Abuja, Nyesom Wike
- Sanarwar da kotun ta fitar ta bayyana cewa Agim ya halarci taron ne a matsayin wanda aka karrama, ba domin rakiyar wani jami’in gwamnati ba
- Kotun ta ce an karrama Mai Shari’a Agim ne saboda rawar da ya taka a fannin shari’a, ba tare da wata alaka da shari’ar rikicin siyasa a Ribas ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kotun Koli ta bayyana cewa zargin da ake yi cewa Mai Shari’a Emmanuel Agim ya rakar Ministan Abuja, Nyesom Wike, zuwa taron karramawar jami’ar UNICAL ba gaskiya ba ne.
Wannan martani ya biyo bayan wani hoton da ya bazu a kafafen sada zumunta, wanda ya nuna Agim yana zaune kusa da Wike a wurin taron.

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Daraktan Yada Labarain Kotun Koli, Festus Akande ne ya fitar da sanarwar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin sanarwar da kotun ta fitar, an bayyana cewa Agim ya halarci taron ne a matsayin wanda aka karrama, ba tare da wata alaka ta siyasa ba.
Kotun Koli ta karyata rade-radin da ake yi
A ranar Litinin, Kotun Koli ta fitar da sanarwa, inda ta karyata cewa Mai Shari’a Agim ya halarci taro a Calabar tare da Wike.
Kotun ta bayyana cewa Agim ya samu karramawa daga jami’ar UNICAL, inda aka ba shi digirin girmamawa a fannin shari’a saboda irin gudunmawar da ya bayar.
A cewar sanarwar, Agim ya kasance daya daga cikin fitattun malaman shari’a da suka yi fice wajen kare adalci da bin doka.
Dalilin da ya sa Agim ya je taron UNICAL
Punch ta wallafa cewa kotun koli ta bayyana cewa Mai Shari’a Agim ya nemi izini domin halartar taron karramawar da aka shirya a jami’ar UNICAL.
A da, yana cikin alkalan da za su halarci jana’izar Mai Shari’a Stanley Alagoa a Bayelsa, amma sai ya nemi izini domin zuwa taron karramawar a UNICAL.
Sanarwar ta jaddada cewa halartar taron da Agim ya yi ba shi da wata alaka da rakiyar wani jami’in gwamnati ko siyasa.

Asali: Facebook
Kotun Koli ta gargadi jama’a kan jita jita
Kotun ta gargadi jama’a da ‘yan jarida da su daina yada labaran da ba su da tushe ko makama, domin hakan yana iya kawo rudani a cikin al’umma.
A cewar sanarwar, irin wadannan jita-jita na iya rage amana da mutuncin bangaren shari’a, wanda yake da matukar muhimmanci ga ci gaban dimokuradiyya.
Kotun ta bukaci jama’a da kafafen yada labarai da su rika tantance gaskiyar labari daga madogara masu inganci kafin su yada shi.
Shugaban ma'aikatan Rivers a yi murabus
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban ma'aikatan jihar Rivers ya ajiye aiki mako daya bayan dakatar da gwamna Siminalayi Fubara.
Shugaban riko na jihar da Bola Tinubu ya nada ne ya bayyana haka a wata sanarwa tare da bayyana cewa ya nada sabon sakataren gwamnati.
Asali: Legit.ng