Sanatan Bauchi Ya ba Mutane Kunya da Azumi, Bidiyosa Yana Rabon Kuɗi Ya Shiga Intanet

Sanatan Bauchi Ya ba Mutane Kunya da Azumi, Bidiyosa Yana Rabon Kuɗi Ya Shiga Intanet

  • Sanata Abdul Ningi na Bauchi ta Tsakiya na shan suka daga ƴan Najeriya bayan an gano shi a wani bidiyo yana raba takardar kuɗi ₦1,000 ga jama’arsa
  • Wani mai suna Ayekooto ne ya wallafa bidiyon, ya soki ɗan Gwamnan Bauchi da tsohon Gwamnan Jigawa, Sule Lamido, waɗanda suka taba Seyi Tinubu
  • A baya Sanata Ningi ya ja hankalin jama’a lokacin da ya zama sanata na farko da aka dakatar ƙarƙashin shugabancin Shugaban Majalisa, Godswill Akpabio

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi - Sanatan Bauchi ta Tsakiya, Abdul Ningi ya ja hankalin ƴan Najeriya da aka gan shi a kan titi yana ba ƴan acaɓa da sauran mutanen mazaɓarsa kyautar N1,000 kacal.

Abdul Ningi ya fara jan hankalin al'ummar ƙasar ne lokacin da zama sanata na farko da Majalisar Dattawa ta 10 karkashin Godswill Akpabio ta dakatar na tsawon watanni uku.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Jerin gwamnonin da suka goyi bayan Tinubu a dakatar da Fubara

Abdul Ningi.
An caccaki sanatan Bauchi kan bidiyon da aka ganshi yana rabawa jama'a N1,000 Hoto: Abdul Ningi
Asali: Twitter

Sanata Abdul Ningi ya rabawa jama'a N1,000

Wani mai suna Ayekooto ne ya wallafa bidiyon Sanata Ningi a shafin X, inda aka gan shi ya na ba kowane mutum ya haɗu da shi a titin mazaɓarsa kyautar N1,000.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya caccaki ɗan gwamnan Bauchi da tsohon gwamnan jihar Jigawa da suka soki ɗan shugaban kasa, Seyi Tinubu kan raba tallafin abincin da yake yi a Ramadan.

Ayekooto ya soki mutanen bisa yadda suka fito suka soki rabon abincin Seyi Tinubu amma suka yi gum da bakinsu game da batun rabon N1,000 da Sanata Ningi ya yi.

An soki ɗan gwamna da Sule Lamido

Ya ce:

"A jihar Bauchi, ɗan gwamna ya fito ya ce ya kamata Seyi Tinubu ya daina shirya buɗa baki da matasan jihar, haka nan Sule Lamiɗo ya ce abin kunya ne shirya buɗa bakin da Seyi ke yi.

Kara karanta wannan

"Tinubu ya saba da tsarin jari hujja," NNPP ta haramta dokar ta ɓacin Ribas

"Yanzu kuma sai ga Sanata Ningi na PDP a jihar Bauchi, ya na koya wa ɗan shugaban ƙasa yadda zai taimaka wa mutane."
Abdul Ningi.
Yan Najeriya sun yi magana kan rabon N1,000 da aka ga sanatam Bauchi na yi a mazaɓarsa Hoto: @Sen_AbdulNingi
Asali: Twitter

Ƴan Najeriya sun maida martani

Tun bayan bayyanar wannan bidiyo na Sanata Ningi, mutane suka yi masa ruwan martani a kafafen sada zumunta, mafi yawa sun caccaki abin da ɗan Majalisar ya yi.

King Emeka ya ce:

"A zuciyarsa ya na ganin wani abin arziƙi yake yi wa jama'a, irinsu ne mutanen da suke son ganin al'umma a cikin talauci domin su ji daɗin hakan.

Abba Askar ya ce:

"Idan ba ku jin Hausa, mutumin da ke sanye farin yadi a kusa da sanatan cewa ya ke yi duk duniya babu sanata irin wannan, ba ma a Najeriya kaɗai ba saboda N1,000."

Okiti-Ogan ya ce:

""Duk waɗannan ‘yan Arewa da ke sukar Seyi Tinubu saboda kyautarsa ga talakawa mugaye ne, marasa tausayi kuma suna da mugun tunani. Ɗan Gwamnan Bauchi ya soki Seyi ne saboda ya na yin abin da Sanata Ningi ya kasa."

Kara karanta wannan

Dambarwar masarauta: Gwamnatin Abba ta aika sako ga 'makiya Kano'

Za a ɗauki matasa aiki a Bauchi

A wani labarin kun ji cewa Gwamnatin Bauchi ta gama shirin ɗaukar haziƙan matasa akalla 10,000 aiki a faɗin kananan hukumomin jihar.

Shugaban Ma’aikatan Jihar Bauchi (HoS), Barista Mohammed Sani Umar, ya ce hakan zai taimaka wajen ɗage aikin yi da inganta ayyukan gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262