Daga Karshe Sanata Natasha Ta Nemi Afuwar Majalisar Dattawa? Ta Fito Ta Fede Gaskiya
- Wasu rahotanni da aka yaɗa sun nuna Natasha Akpoti-Uduaghan ta fito ta nemi afuwar majalisa kan dakatarwar da aka yi mata
- Sai dai, Sanatar ta bayyana cewa ko kaɗan babu ƙamshin gaskiya a rahotannin, domin ba ta nemi afuwar majalisar dattawa ba
- Sanatar Kogin ta bayyana cewa har yanzu ta na nan kan bakarta kuma ba za ta daina fafutukar ganin mata sun samu ƴanci ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kogi - Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi magana kan rahotannin da ke cewa ta nemi afuwar majalisar dattawa kan dakatarwar da aka yi mata.
Sanata Natasha wacce ke wakiltar Kogi ta Tsakiya ta ƙaryata rahotannin da ke cewa ta nemi afuwar majalisar dattawa kan batun da ya kai ga dakatar da ita.

Asali: Facebook
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa Sanata Natasha ta fitar a ranar Litinin, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane martani Sanata Natasha ta yi?
Sanata Natasha ta bayyana waɗannan rahotanni a matsayin ƙarya da yaudara, tana mai jaddada cewa har yanzu tana nan daram kan matsayarta.
"Rahotannin da ke cewa na nemi afuwar majalisar dattawa ko kuma na janye matsaya ta ba gaskiya ba ne."
"Ina nan kan bakata, kuma ban ba da wata afuwa ga majalisar dattawa ko wani ba dangane da wannan batu."
- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan
Ta soki waɗanda ke yaɗa waɗannan rahotanni na ƙarya, ta zarge su da ƙoƙarin karkatar da gaskiya da kuma yaudarar jama’a, rahoton jaridar The Cable ya tabbatar.
Sanatar, wacce aka dakatar bayan wani saɓani da shugabannin majalisar dattawa, ta ce har yanzu ta na tsaye kan kare haƙƙin mutanen da take wakilta.
Haka nan, ta yi zargin cewa wasu mutane na ƙoƙarin amfani da bayanan ƙarya don rinjayar ra’ayin jama’a.
"Ina kira ga jama’a da su yi watsi da waɗannan jita-jita da rahotanni, domin ba su ne matsaya ta ba. Burina shi ne tsayawa kan gaskiya, adalci, da kuma kare mutanen da na ke wakilta."
- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan
Ta kuma bayyana damuwa kan abin da ta kira yunƙurin da ake na hana ta yin magana a cikin majalisar dattawa.

Asali: Facebook
Natasha ta ce a yi watsi da rahotannin neman afuwa
"Wannan ba wai kawai ni ake hari ba, wannan batu ne da ya shafi mutuncin dimokuraɗiyya. Ba za a tsoratar da ni ko a tilasta ni na janye matsaya ta ba ta hanyar ƙirƙirar labaran ƙarya."
- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan
Ta buƙaci ƴan Najeriya da su yi taka-tsantsan da bayanai marasa inganci, ta na mai cewa duk wata sanarwa daga gare ta za ta fito ne kawai daga shafukanta na asali.
"Ina matuƙar godiya ga mutanena bisa goyon baya da haɗin kai da suke ba ni. Ina ba ku tabbacin cewa zan ci gaba da yaƙi don tabbatar da gaskiya da adalci."
- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan
Natasha ta caccaki Sanata Sunday Karimi
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta caccaki Sanata Sunday Karimi bayan ya kare matakin dakatarwar da aka yi mata a majalisa.
Sanata Natasha ta ce ya kamata hukumar NDLEA ta riƙa yi wa sanatoci gwajin miyagun ƙwayoyi domin kaucewa yin sokana a yayin gudanar da ayyukansu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng