Ba a Gama da Akpabio ba, Natasha Ta Sake Tsokano Fada da Wani Sanata
- Sabuwar ɓaraka ta kunno kai tsakanin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da Sanata Sunday Karimi mai wakiltar Kogi ta Yamma
- Sanata Sunday Karimi ya kare dakatarwar da aka yi wa Natasha, inda ya bayyana cewa abokiyar aikinsa ta jawo abin kunya ga jihar Kogi
- Sai dai, a martanin da ta yi, ta buƙaci NDLEA da ta riƙa yin gwajin miyagun ƙwayoyi ga sanatoci saboda gujewa yin ɓaramɓarama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kogi - Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan wacce aka dakatar da Sanata Sunday Karimi, mai wakiltar Yankin Kogi Yamma, sun yi musayar yawu a ranar Lahadi.
Hakan ya faru ne bayan Sunday Karimi na APC ya kare dakatarwar da aka yi wa Natasha daga majalisar dattawa, ya na mai cewa abin da ya faru wanda ya kai ga dakatar da ita abin kunya ne.

Kara karanta wannan
Daga karshe Sanata Natasha ta nemi afuwar majalisar dattawa? Ta fito ta fede gaskiya

Asali: Facebook
Sai dai a martanin da Natasha ta yi, ta ce kalaman Karimi sun tabbatar da bukatar gudanar da gwajin miyagun ƙwayoyi ga sanatoci, cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatan Kogi ya caccaki Natasha
A cikin sanarwar da ya fitar, Karimi ya bayyana cewa abin da Sanata Natasha ta aikata ya tabbatar da gaskiyar tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, wanda tun farko ya nuna fargaba game da shigowarta majalisar dattawa.
Ya bayyana takaicinsa kan yadda ta yi watsi da shawarwarin da ya ba ta don a warware matsalar.
Karimi ya nuna takaicin cewa Natasha Akpoti-Uduaghan ta jawowa jihar Kogi abin kunya ta hanyar barin saɓaninta da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya kai ga dakatarwa.
A cewarsa, tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, ya rigaya ya hango wannan matsala tun farko, inda ya bayyana cewa halayenta ba su da tabbas.
"Duk shawarwarin da muka ba ta ba ta saurara ba. Saboda haka, ba abin mamaki ba ne cewa Yahaya Bello ya hango irin hakan."
"Sanata Natasha ba wai kawai ta kunyata jiharmu ba ne, ta jawo ana yi mana wani irin kallo a faɗin ƙasar nan."
- Sanata Sunday Karimi
Wane martani Sanata Natasha ta yi?
A martaninta kan sukar da ya yi mata, Sanata Natasha ta buƙaci hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) ta riƙa gudanar da gwajin miyagun ƙwayoyi a kan sanatoci lokaci zuwa lokaci.
Ta yi martanin ne yayin da take magana da jaridar The Punch ta bakin mai taimaka mata kan harkokin watsa labarai, Israel Arogbonlo.
Sanata Natasha ta jaddada cewa ya zama wajibi NDLEA ta riƙa duba lafiyar ƙwaƙwalwar sanatoci don gujewa yin abin kunya wajen gudanar da ayyukansu.
"NDLEA na buƙatar gudanar da gwajin miyagun ƙwayoyi lokaci zuwa lokaci kan sanatoci. Wannan tsarin zai ceci majalisa daga yanke shawara marasa kan gado."
- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan
A cewarta, wannan ra’ayin ba sabon abu ba ne, domin tuni shugaban NDLEA, Buba Marwa, ya goyi bayan a riƙa yi wa ƴan siyasa gwajin miyagun ƙwayoyi a matsayin wani ɓangare na tantancesu kafin su yi takara.
Natasha da majalisar dattawa
Sanata Natasha ta ci gaba da bayyana cewa dakatarwar da aka yi mata wata hanya ce ta tauye mata hakki da murya a majalisar dattawa.
Ta ce irin wannan matakin ba wai kawai cin zarafi ne ba, har ma yana haifar da illa ga dimokuradiyya.
A cewarta, idan ba a kawo sauyi ba, to sauran ‘yan majalisa, musamman mata, na iya fuskantar irin wannan matsin lamba a nan gaba.
A gefe guda, wasu ‘yan majalisa da ke goyon bayan Natasha sun nuna rashin amincewarsu da kalaman Karimi.
Wasu daga cikinsu sun ce maimakon ya mayar da hankali kan rikicin siyasar Kogi, ya fi dacewa ya yi kokarin ganin an samu fahimta da sulhu a majalisar dattawa.
Hakazalika, wasu ‘yan siyasa daga Kogi sun bayyana cewa, tun farko, Natasha ta fuskanci matsin lamba daga wasu jiga-jigan siyasa a jihar, wadanda ke ganin shigowarta majalisar barazana ce gare su.
A cewarsu, wannan ne dalilin da ya sa ake amfani da duk wata hanya don dakile tasirinta.
A halin da ake ciki, magoya bayan Natasha sun bayyana cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen kare zabinsu, tare da yin kira ga shugabannin siyasa su mutunta ra’ayin jama’a.
Magoya bayan Natasha sun yi zanga-zanga
A wani labarin kuma, kun ji cewa magoya bayan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan sun gudanar da zanga-zanga domin adawa da shirin kiranye da ake yi mata.
Mutanen waɗanda suka fito daga mazaɓar Kogi ta Tsakiya sun yi zargin cewa masu shirin yi wa Natasha kiranye, kuɗaɗe suka amsa daga hannun ƴan siyasa.
Salisu Ibrahim ya fadada wannan labarin ta hanyar kara bayani kan rikicin Natasha da majalisa.
Asali: Legit.ng