Wani abin Fashewa Ya Tarwatse a Cibiyar Haƙo Mai a Rivers bayan Dakatar da Fubara

Wani abin Fashewa Ya Tarwatse a Cibiyar Haƙo Mai a Rivers bayan Dakatar da Fubara

  • Sabuwar fashewa ta auku a cibiyar hakar mai ta Soku, jihar Rivers, kasa da mako guda bayan fashewar bututun Trans Niger Pipeline
  • Kungiyar YEAC-Nigeria ta bukaci a gudanar da bincike kan fashewar, tana mai cewa har yanzu ba a san ko farmakin 'yan ta'adda ba ne
  • Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a Rivers, inda ya dakatar da majalisa da gwamna bisa gazawar kare kadarorin mai da rikicin siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Rivers - Kasa da mako guda bayan fashewar bututun Trans Niger Pipeline a Bodo, wani abun fashewa ya fashe a cibiyar hakar mai ta Soku a jihar Rivers.

Wannan sabuwar fashewar ta faru ne a karamar hukumar Akuku Toru, lamarin da ya jawo tantama kan tsaron bututun mai da karuwar hare-hare kan wuraren hakar mai.

Kara karanta wannan

Nasarori 3 da Nyesom Wike ya samu a cikin kwanaki 3 a siyasar jam'iyyar PDP

Kungiyar YEAC-Ngeria ta yi magana da abin fashewa ya sake tarwatsewa a Rivers
YEAC-Ngeria ta bayar da bayani kan tashin wani abin fashewa a cibiyar hako mai a Rivers. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Rivers: Abin fashewa ya tashi a cibiyar hako mai

Kungiyar matasa da kare muhalli ta YEAC-Nigeria ta tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Lahadi, tana mai dogaro da rahotannin masu sa ido da ke fadin yankin Neja Delta, inji rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata sanarwa da daraktan kungiyar, Dr. Fyneface Dumnamene Fyneface, ya sanya wa hannu, an bayyana girman wannan sabuwar fashewar da illar da za ta iya haifarwa.

"An ji karar fashewa tare da tashin wata gagarumar wuta a sararin sama daga yankin cibiyar hakar mai. Wutar na ci har zuwa lokacin da ake bada wannan rahoto," in ji sanarwar.

Kamfanin Nigeria Liquefied Natural Gas (NLNG) Limited ne ke kula da cibiyar hakar man ta Soku.

Sai dai har yanzu ba a san hakikanin musabbabin fashewar ba, ko matsalar kayan aiki ce, ko kuma wani hari ne daga 'yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda mutane 10 suka mutu, motoci 18 suka kone kurmus a kan gadar Abuja

Tinubu ya ayyana dokar ta baci a Rivers

Wannan shi ne karo na uku da aka samu tashin bam a kadarorin mai a jihar Rivers cikin mako guda. Fashewar farko ta auku a Ogoni, sai kuma ta biyu da ta faru a Oga/Egbema/Ndoni.

A cikin jawabin da ya gabatar a ranar 18 ga Maris, Shugaba Bola Tinubu ya lissafa fashewar da ta faru a Oga, a cikin dalilan ayyana dokar ta-baci na tsawon watanni shida a jihar Rivers.

Daga cikin matakan dokar ta-bacin, Shugaba Tinubu ya dakatar da majalisar dokokin jihar Rivers, mataimakin gwamna, da kuma Gwamna Siminalayi Fubara, bisa zargin gazawa wajen kare wuraren hakar mai.

Hakan ya biyo bayan barazanar wasu matasa da aka gani a wani bidiyo suna gargadin kada a tsige Fubara daga mukaminsa.

An nemi a binciki dalilin fashewar cibiyar mai

Kungiyar YEAC-Nigeria ta bukaci a gaggauta gudanar da bincike kan fashewar da ta faru a Soku.

Kara karanta wannan

"Ka da a ɗora mun laifi": Gwamna Fubara ya cire tsoro, ya ƙaryata kalaman Tinubu

Ta bukaci hukumar tantance hatsarin mai da daukar matakin gaggawa (NOSDRA) da ta gudanar da binciken hadin gwiwa (JIV) domin gano hakikanin dalilin fashewar.

Kungiyar ta jaddada cewa dole ne a hukunta duk wanda aka samu da laifi bisa tanadin dokar masana’antar man fetur ta PIA, 2021.

Dr. Fyneface ya bayyana cewa, dole ne a dauki matakin da ya dace domin kare lafiyar al’umma da kuma tabbatar da adalci ga wadanda abin ya shafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.