Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Yi Wa Jami'an Tsaro Ƙwanton Bauna, an Samu Asarar Rayuka
- An shiga jimami a jihar Zamfara bayan ƴan bindiga sun kai wani harin ta'addanci kan ƴan sa-kai masu ƙoƙarin samarnda tsaro
- Ƴan bindigan sun hallaka ƴan sa-kai mutum tara bayan sun yi musu wani kwanton ɓauna a ƙaramar hukumar Anka ta jihar
- Harin kwanton ɓaunan dai ya auku ne bayan ƴan sa-kan sun dawo daga wani farmaki da suka kai kan miyagu a cikin daji
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Aƙalla ƴan sa-kai tara, waɗanda aka fi sani da Askarawa, suka rasa rayukansu a wani hari da ƴan bindiga suka kai musu a jihar Zamfara.
Ƴan bindigan sun kai musu harin kwanton ɓauna ne a ranar Asabar a ƙaramar hukumar Anka, yayin da suke komawa gida bayan sun samu nasara a wani farmakin haɗin gwiwa da jami’an tsaro.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun kai hari a Abuja, sun yi awon gaba da babbar soja da wasu mutane

Asali: Original
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan bindiga sun kashe ƴan sa-kai
Majiyoyi sun bayyana cewa yan sa-kan sun fafata da ƴan bindiga masu ɗauke da muggan makamai a cikin daji tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro, inda suka samu babbar nasara a kan ƴan ta’addan.
Sai dai yayin da suke kan hanyarsu ta komawa, wata tawagar ƴan bindiga sun yi musu kwanton-bauna, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar da dama daga cikinsu.
Rundunar tsaron Askarawan Zamfara dai Gwamna Dauda Lawal ne ya ƙirƙiro ta domin ƙarfafa ƙoƙarin da sauran hukumomin tsaro ke yi a faɗin jihar.
Mutanen gari da shugabannin al’umma sun nuna matuƙar baƙin ciki da alhini kan wannan mummunan hari, inda suka miƙa ta’aziyyarsu ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.
Sun jinjinawa jarumta da sadaukarwar da ƴan sa-kan suka yi domin tallafawa yaƙi da rashin tsaro a jihar.
Ƴan bindiga na ci gaba da barazana a Zamfara
Wannan harin ya ƙara jaddada yadda ƴan bindiga ke ci gaba da zama barazana ga zaman lafiya da tsaron jama’a a yankin.
Duk da irin nasarorin da jami’an tsaro ke samu tare da hadin gwiwar ƴan sa-kai, ƴan ta’adda na cigaba da kai hare-hare masu muni a wasu yankuna.
Al’ummar yankin sun buƙaci gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙara ɗaukar matakan daƙile ayyukan ƴan bindiga, tare da ƙara bai wa rundunar Askarawan Zamfara kayan aiki da goyon baya domin su samu damar kare jama’a da yankunansu.
Ƴan bindiga sun sace mutane a Abuja
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai hari a cikin yankin Mpape da ke birnin tarayya Abuja.
Ƴan bindigan a yayin harin sun yi awon gaba da wata babbar sojan ruwa mai muƙamin Laftanal tare da wasu mutum biyu.
Bayan sace mutanen, ƴan bindigan sun buƙaci a ba su kuɗin fansa N100m kafin su sake su domin su shaƙi iskar ƴanci.
Asali: Legit.ng