Abu Ya Girma: SERAP Ta Maka Tinubu a Kotu kan dakatar da Fubara, Ta Jero Bukatunta
- Ƙungiyar SERAP ta ɗauki matakin shari'a kan dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi
- SERAP ta maka Shugaba Tinubu ƙara a gaban kotu inda take ƙalubalantar matakin da ya ɗauka
- Ta buƙaci kotun da ta soke dakatarwar da aka yi wa zaɓaɓɓun shugabanni domin a cewarta hakan ya saɓa da kundin tsarin mulkin Najeriya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙungiyar SERAP ta shigar da ƙara kan Shugaba Bola Tinubu saboda dakatarwar da ya yi wa Gwamna Siminalayi Fubara da ƴan majalisar dokokin jihar Rivers.
Ƙungiyar SERAP ta bayyana dakatarwar da Tinubu ya yi musu yayin da yake amfani da ikon da yake da shi na ayyana dokar ta ɓaci, a matsayin wacce ta saɓa ƙa'ida.

Asali: Twitter
SERAP ta kai ƙarar Tinubu a kotu

Kara karanta wannan
"Na yi mamaki": 'Dan majalisa ya magantu kan karbar cin hanci don dokar ta baci a Rivers
Ƙungiyar SERAP ta sanar da shigar da ƙarar ne a shafinta na X a ranar Lahadi, 23 ga watan Maris 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Waɗanda suka shigar da ƙarar sun haɗa da Yirabari Israel Nulog, Nengim Ikpoemugh Royal, da Gracious Eyoh–Sifumbukho, waɗanda dukkansu mambobi ne na SERAP Volunteers’ Lawyers Network (SVLN) a jihar Rivers.
Dukkanin masu shigar da ƙarar sun cancanci kaɗa ƙuri’a kuma sun kaɗa ƙuri’arsu a babban zaɓen 2023.
Mutanen da aka ambata a cikin ƙarar a matsayin waɗanda ake ƙara sun haɗa da Antoni Janar na tarayya kuma ministan shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), da Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya).
Wane buƙatu SERAP ke nema?
A cikin ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/558/2025, wacce aka shigar a babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Juma’a da ta gabata, masu shigar da ƙarar suna neman:
Umurnin soke dakatarwar da aka yi wa shugabannin da aka zaɓa ta hanyar dimokuradiyya a jihar Rivers ta hannun Shugaba Tinubu yayin ayyana dokar ta-baci a jihar.

Kara karanta wannan
Tsagin NNPP ya kwanto wa Kwankwaso da mabiyansa ruwa, jam'iyya ta tura wasiƙa ga INEC
Umurnin soke naɗa Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya) a matsayin shugaban riko na jihar Ribas.
Umurnin hana wanda ake ƙara na uku daga ci gaba da aiki ko yin wani aiki a matsayin shugaban riƙo na jihar Rivers, bisa ga naɗin da wanda ake ƙara na farko ya yi masa a ranar 18 ga watan Maris, 2025.
Umurnin hana dukkan waɗanda ake ƙara, ciki har da wakilansu ko duk wani mutum da ke aiki a madadinsu, daga ɗaukar gwamna, mataimakin gwamna, da ƴan majalisar dokoki jihar Rivers a matsayin waɗanda aka dakatar.
Masu shigar da ƙarar suna kuma neman:
Sanarwa ta hukuma da ke bayyana cewa, bisa ga sashi na 1(2) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 (wanda aka gyara), ba za a iya tafiyar da Najeriya ko wani ɓangare na ƙasar ba, sai bisa ga tanadin kundin tsarin mulki.
Ba a sanya ranar da za a fara sauraron ƙarar ba.
SERAP ta samu yabo
Idris Adam ya yaba da matakin da ƙungiyar SERAP ta yi na garzayawa kotu domin ƙalubalantar matakin Shugaba Bola Tinubu na sanya dokar ta ɓaci a Rivers.
"Abin da SERAP ta yi ya dace domin matakin da shugaban ƙasan ya ɗauka ya jawo cece-kuce. Yana da kyau a samu waɗanda za su riƙa ƙalubalantar ɓangaren zartaswa idan suka yanke wani hukunci."
"Sai dai, na san SERAP ta sha kai ƙararraki a kotu, amma ɓan taɓa ganin wanda ta yi nasara ba."
- Idris Adam
Gwamnonin PDP za su kai Tinubu kotu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnonin jam'iyyar PDP sun nuna rashin amincewarsu da matakin da Shugaba Bola Tinubu ya ɗauka na dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa za su ƙalubalanci dakatarwar da aka yi wa takwaransu na jihar Rivers a gaban kotu.
Asali: Legit.ng