Rikicin Ribas: An Ƙara Samun Bayanai kan Dalilin Shugaba Tinubu na Dakatar da Gwamna

Rikicin Ribas: An Ƙara Samun Bayanai kan Dalilin Shugaba Tinubu na Dakatar da Gwamna

  • Kakakin APC na ƙasa, Felix Morka ya bayyana cewa Bola Tinubu ya dakatar da Simi Fubara ne saboda yadda yake karya doka a jihar Ribas
  • Morka ya musanta jita-jitar cewa matakin da shugaban kasa ya ɗauka ya kara dagula rikicin siyasar Ribas, ya ce Tinubu ya yi abin da ya dace
  • Wannan dai na zuwa ke a lokacin da ake ta ce-ce-ku-ce kan dokatar ta ɓacin da gwamnatin tarayya ta ƙaƙaba a Ribas saboda rikicin siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Mai magana da yawun jam’iyyar APC, Felix Morka ya zargi dakataccen gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara da yi wa doka hawan kawara a mulkinsa.

Morka ya bayyana cewa Gwamna Siminalayi Fubara ya mulki Ribas ba tare da bin doka ba idan ba kafin Shugaban Kasa Bola Tinubu ya tsoma baki a rikicin siyasar jihar ba.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun faɗi damuwarsu kan dokar ta ɓaci a Ribas, sun ambaci Kano

Bola Tinubu da Fubara.
Kakakin ya caccaki yadda Fubara ya tafiyar mulki a jihar Ribas Hoto:@OfficialABAT
Asali: Twitter

Matakan da Bola Tinubu ya ɗauka a Ribas

A ranar Talata, shugaba Tinubu ya dakatar da Gwamna Fubara, mataimakinsa, da mambobin majalisar dokokin jihar Ribas, kamar yadda The Cable ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kasa Tinubu ya ɗauki matakin ne bayan shafe watanni ana fama da tashin hankali na siyasa.

Haka kuma, shugaban ƙasa ya ayyana dokar ta-baci tare da naɗa Ibok-Ete Ibas, tsohon babban hafsan rundunar sojin ruwa, a matsayin mai kula da harkokin jihar na wucin gadi.

Kakakin jam'iyyar APC ya jero dalilan Tinubu

Da yake magana a shirin Prime Time na tashar Arise TV, Morka ya zargi Gwamna Fubara da take ka’idodin dimokuraɗiyya.

"Ba wai kawai rusa majalisar dokoki kaɗai ya yi ba, ya hana su zama kwata-kwata. Ya watsa su, kamar ba su wanzu ba. Ya hana su albashinsu da duk wani kudi da ya kamata majalisa ta samu."

Felix Morka ya kuma zargi Fubara da kafa majalisar dokoki ta wucin gadi da ‘yan tsiraru, maimakon amincewa da majalisar da aka zaɓa bisa doka.

Kara karanta wannan

Aiki zai dawo sabo: Gwamnoni 12 za su maka Tinubu a kotu kan Fubara

"Ya ci gaba da mulki ba tare da bin doka ba na tsawon fiye da watanni 14," in ji shi.

Matakin Tinubu ya dagula rikicin Ribas?

Kakakin APC na ƙasa ya karyata raɗe-raɗin da ke cewa matakin da Tinubu ya dauka ya kara dagule lamarin, yana mai cewa rikicin ya samo asali ne daga ayyukan Fubara.

"Tun kafin shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci, akwai matsalolin karya doka da oda a jihar Ribas.
"Wannan matsalolin kirkiro su aka yi kuma aka ƙara rura wutar, wanda ya jefa jihar Ribas cikin ruɗani kuma duk da sa hannun Fubara.

- In ji Morka.

Felix Morka.
Felix Morka ya goyi bayan matakin da Bola Tinubu ya ɗauka a Ribas Hoto: Felix Morka
Asali: UGC

Felix Morka ya jaddada cewa shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci tare da dakatar da Gwamna Fubara ne domin ceto jihar Ribas don tabbatar da doka da oda.

Jonathan ya soki matakin dakatar da Fubara

A wani labarin, kun ji cewa Goodluck Jonathan ya soki dakatar da gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa da ƴan majalisar dokokin jihar Ribas da Bola Tinubu ya yi.

Ya nuna cewa yana da mahimmanci a lura cewa mutuncin ƙasa da yawan hannun jarin da ke shigowa na da alaƙa da matakan da ɓangarorin gwamnati suka ɗauka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262