ALGON: Dalilin Gwamnatin Tinubu na Kasa Fara Tura Kudi Kai Tsaye ga Kananan Hukumomi

ALGON: Dalilin Gwamnatin Tinubu na Kasa Fara Tura Kudi Kai Tsaye ga Kananan Hukumomi

  • Ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi ta Najeriya (ALGON) ta fito ta yi ƙarin haske kan rashin fara samun kuɗi kai tsaye daga gwamnati
  • Shugaban kwamitin amintattu na ALGON, Odunayo Alagbere, ya bayyana cewa har yanzu akwai tsare-tsaren da ba a kai ga kammalawa ba
  • Ya yabawa gwamnatin tarayya kan ƙoƙarin da take yi wajen ganin ƙananan hukumomi sun samu ƴancin cin gashin kansu
  • Odunayo Alagbere ya nuna cewa turawa ƙananan hukumomin kuɗinsu kai tsaye, zai taimaka wajen fatattakar talauci a ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi ta Najeriya (ALGON), ta yi magana kan dalilin gwamnatin tarayya na kasa fara turawa ƙananan hukumomi kuɗadensu kai tsaye.

Ƙungiyar ALGON ta ce har yanzu ba a fara tura kuɗaɗen ba ne saboda wasu matakan da har yanzu ba a kammala su ba.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gwabza da 'yan ta'addan Lakurawa cikin azumi, an samu asarar rayuƙa

Gwamnatin Tarayya ba ta fara tura kudi kai ga kananan hukumomi ba
Gwamnatin tarayya ta kusa fara tura kudade kai tsaye ga kananan hukumomi Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Shugaban kwamitin amintattun ALGON, Odunayo Alegbere, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a Abuja bayan wata ganawa da ƙungiyar ta yi, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ta ba ƙananan hukumomi umarni

Ya bayyana cewa an umarci ƙananan hukumomi da su buɗe asusu a babban bankin Najeriya (CBN) domin sauƙaƙa aiwatar da tsarin turo kuɗaɗen kai tsaye.

Duk da cewa har yanzu ba a kammala tsarin ba, Alegbere ya yabawa gwamnatin tarayya kan ci gaban da aka samu, yana mai cewa hukuncin Kotun Koli kan ƴancin cin gashin kan ƙananan hukumomi babbar nasara ce.

Ya bayyana cewa gwamnati tana ƙoƙarin aiwatar da wannan hukunci, wanda ya haɗa da ƴancin gudanarwa da ƴancin sarrafa kuɗaɗe ga ƙananan hukumomi, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar da zancen.

Alegbere ya tabbatar da cewa bayar da kuɗaɗe kai tsaye ga ƙananan hukumomi zai taimaka wajen rage talauci, domin hakan zai ba ƙananan hukumomi damar riƙe kuɗaɗensu da gudanar da ayyukan ci gaba.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta yi wa gwamnatin jihar Kano barazana da dokar ta ɓaci

Ya kuma soki tsarin da ake amfani da shi a yanzu, inda gwamnonin jihohi ke shirya zaɓen ƙananan hukumomi, ya na mai cewa tsarin ya fi kama da naɗa shugabanni fiye da zaɓen dimokuraɗiyya na gaskiya.

'Tura kuɗaɗen zai rage talauci' - ALGON

A cewarsa, ya na da kyakkyawan fata cewa gyaran kundin tsarin mulki da majalisar tarayya ke yi zai warware wannan matsala.

“Muna godiya ga shugaban ƙasa, kuma ko da yake ba mu kai ga cimma burinmu ba tukuna, muna samun ci gaba sannu a hankali."

- Odunayo Alagbere

A ƙarshe, ya sake nanata cewa tura kuɗaɗe kai tsaye ga ƙananan hukumomi zai taka muhimmiyar rawa wajen rage talauci a ƙasa.

Gwamnonin jihohi sun fara lallaɓa Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnonin Najeriya sun fara ƙoƙarin kawo cikas ga yunƙurin fara turawa ƙananan hukumomi kuɗaɗensu kai tsaye.

Gwamnonin sun fara lallaɓa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan a yi jinkirin fara tura kuɗaden ga ƙananan hukumomi.

Sun nuna cewa akwai ɗimbin bashi a kan ƙananan hukumomin wanda ya kamata a ce sun biya kafin a fara tura musu kudaɗen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng