"Me Yasa ba Ka Sa a Legas ba?" An Tunkari Tinubu da Tambaya kan Dokar ta Ɓaci

"Me Yasa ba Ka Sa a Legas ba?" An Tunkari Tinubu da Tambaya kan Dokar ta Ɓaci

  • Farfesa Pat Utomi ya ƙalubalanci Bola Ahmed Tinubu kan ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Ribas ba tare da yin hakan a jihar Legas ba
  • Masanin tattalin arziki yace babu wani dalili da zai sa a kafa dokar ta ɓaci a jihar Ribas, yana mai cewa babu adalci a matakin Tinubu
  • Farfesan ya kuma soki amincewa da wannan mataki da Majalisar Dattawa da Tarayya suka yi, ya ce sun ci amanar ƴan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Fitaccen masanin tattalin arziki, Pat Utomi, ya yi fatali da matakin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ayyana dokar ta-baci a Jihar Rivers.

Farfesa Pat Utomi ya bayyana cewa babu wata hujja da ke nuna tilas sai an ɗauki matakin ayyana dokar ta ɓaci.

Bola Tinubu, Pat Utomi.
Fat Utomi ya caccaki matakin sanya dokar ta ɓaci a jihar Ribas Hoto: @OfficialABAT, Pat Utomi
Asali: Twitter

Pat Utomi ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels tv ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Tinubu ya jawo wa kansa, dattawan Ribas sun faɗi matsayarsu kan dakatar da gwamna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matakan da Bola Tinubu ya ɗauka a Ribas

Vanguard tace tun farko dai shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a Ribas bisa dalilin da suka haɗa da fasa bututun mai da rikicin siyasar da ya ƙi ƙarewa.

A cikin wani jawabin da ya yi ga ƴan ƙasa a ranar Talata, 18 ga Maris, 2024, shugaba Tinubu ya ce ba zai zuba ido yana kallo ana ɓarnata kayayyakin al'umma ba.

Bugu da ƙari, shugaban ƙasar ya naɗa tsohon babban hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Ibokette Ibas (mai ritaya), a matsayin mai kula da harkokin jihar Ribas.

Ya yi haka ne bayan dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu, da kuma dukkan ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.

Utomi ya caccaki shugaban kasa Tinubu

Da yake tsokaci kan wannan lamarin, Farfesa Utomi ya caccaki wannan mataki, yana mai cewa rikicin siyasa da ke faruwa a Rivers bai kai a ayyana dokar ta-baci ba.

Kara karanta wannan

Majalisar Wakilai ta ɗauki zafi kan buƙatar Tinubu na ayyana dokar ta ɓaci a Ribas

A cewarsa, har lokacin da ‘yan bindiga ke tayar da bututun mai a jihar a zamanin da, ba a taba ayyana dokar ta-baci ba.

Ya kuma kalubalanci shugaba Tinubu kan rashin ayyana dokar ta-baci a Jihar Legas lokacin da rikici ya ɓarke tsakanin Shugaban Majalisar Dokoki, Mudashiru Obasa, da wasu ‘yan majalisar.

Oat Utomi.
Pat Utomi ya caccaki Bola Tinubu kan ƙaƙaba dokar ta ɓaci a Ribas Hoto: Prof. Pat Utomi
Asali: Twitter

Me ya sa Tinubu bai sa dokar a Legas ba?

“Ina da tambaya, menene matsalar jihar Ribas da ya sa dole sai an ayyana dokar ta-baci? A lokacin da bututun mai ke fashewa kamar gurguru a Rivers, an taba yin dokar ta-baci?
“Me ya sa bai ayyana dokar ta-baci a Legas ba lokacin da majalisar jihar ke fama da rikici? Me ya sa sai Ribas? Ya kamata a yi adalci, daidaito da gaskiya a mulki, amma babu alamar hakan.
"Abin takaici ne yadda ake kokarin lalata dimokuradiyyar da muka yi wahala wajen samowa."

- Pat Utomi.

Bugu da ƙari, Farfesa Utomi ya soki Majalisar Ƙasa bisa amincewa da ayyana dokar ta-bacin, yana mai cewa hakan cin fuska ne ga ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Rivers: Atiku ya sauya salo, ya roƙi ƴan Najeriya bayan Tinubu ya sanya dokar ta ɓaci

Dattawan Ribas sun yi Allah wadai

A wani labarin, kun ji cewa dattawan jihar Ribas sun nuna ɓacin ransu kan ayyana dokar ta ɓaci da shugaban kasa ya yi.

Kungiyar dattawan ta ce matakin da shugaban ƙasa ya ɗauka babu adalci a cikinsa kuma ya ci karo da kundin tsarin mulkin ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262