Jama'a Sun Barke da Azababben Faɗa a Watan Azumi, An Kashe Tsohon Mai Mulki
- Rikici ya sake ɓarkewa tsakanin mutanen kauyukan Ifon da Ilobu a Osun, an kashe tsohon kansila da wasu mutane da ba a tantance ba
- An tattaro cewa mutanen garuruwan biyu sun fara kai wa juna hare-hare da ƙona gidaje tun daga 15 har 20 ga watan Maris, 2025
- Gwamna Ademola Adeleke ya umarci a tura ƙarin jami'an tsaro domin shawo kan lamarin da kuma binciko masu tada fitina a jihar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Osun - Tsohon ɗan majalisar ƙaramar hukuma watau kansila daga Ifon Orolu a Jihar Osun, mai suna Azeez, ya rasa ransa a rikicin iyaka tsakanin kauyukan Ifon da Ilobu.
Har yanzu ba a bayyana cikakken bayanin yadda aka kashe tsohon kansilan ba a wannan rikici da ya sake ɓarkewa tsakanin mutanen kauyukan biyu a jihar Osun.

Kara karanta wannan
Wike ya sake samun nasara, Kotun Koli ta yi hukunci kan rikicin sakataren PDP na ƙasa

Asali: Original
Punch ta ce mazaunin Ifon, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda tsoron hare-hare, ya ce an tabbatar da rasuwar Azeez a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Osun da ke Osogbo a safiyar Juma’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Faɗa ya kaure tsakanin kauyuka 2 a Osun
Bayan haka, an ruwaito cewa an kona gidaje da dama a lokacin artabun da ya ɓarke tsakanin al’ummomin biyu.
Mai taimaka wa Olufon na Ifon, Yusuf Adekunle, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya zargi al’ummar Ilobu da daukar nauyin harin, rahoton Leadership.
Sai dai Otun Jagun na Ilobu, Adegoke Ogunsola, ya karyata zargin, yana mai cewa mutanen Ifon ne suka fara kai hari kan mazauna Ilobu, suka raunata mutane da dama.
Mutanen garuruwan sun fara zargin juna
Adekunle ya kara da cewa:
“Marigayin shi ne Hon. Azeez, tsohon kansila. Mutanen Ilobu sun yi kokarin kai mana hare-hare, kuma mun kai rahoto ga jami’an tsaro a lokuta da dama.
"Tun daga ranar 13 zuwa 20 ga wannan wata, mun rubuta koke zuwa ga gwamna da hukumomin tsaro. A daren jiya da misalin karfe 11:00, sai muka fara jin harbe-harbe. Suka fara kona gidajen jama'armu.
A nasa bangaren, Ogunsola ya ce ‘yan ta’adda daga Ifon ne suka kai hari kan mazauna Ilobu, suka far wa mutane a gonakinsu.
Ya bayyana cewa:
"A gaskiya su ne suka fara kai hari tun kimanin kwana biyar da suka wuce, wato tun ranar Litinin. Suka far wa mutanenmu a gonaki a Gbere Onireke da Opapa.
"Sun kai wa wani Baale mai suna Liasu Ishola hari a ranar Talata, suka yi kokarin sace shi daga gidansa, amma sai ya kira jama’a don taimako, manoma da masu gini suka kubutar da shi daga hannun maharan.

Asali: Facebook
Wane matakin gwamnan Osun ya ɗauka?
A yayin da rikicin ke ci gaba da kamari, Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya bada umarnin tura dakarun tsaro domin dawo da zaman lafiya tsakanin Ifon da Ilobu.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Olawale Rasheed, ya fitar, Adeleke ya bukaci rundunar tsaro ta hadin gwiwa da ta shigo tsakani domin dakile rikicin.
Gwamnan ya yi Allah-wadai da siyasantar da rikicin, ya bukaci jami’an tsaro su bi diddigin masu tada rikicin tare da gurfanar da su gaban kotu.
An kashe mutum 6 a rikicin Osun
A wani labarin, kun ji cewa akalla mutane shida suka mutu a jihar Osun da rikici ya ɓarke bayan kotu ta mayar da ciyamomon APC kan kujerunsu.
Gwamna Ademola Adeleke ya zargi ministan tattalin arzikin ruwa, Gboyega Oyetola da tayar da fita tare da haɗin guiwar hukumomin tsaro.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng