Dokar Ta Baci a Ribas: Ana Zargin Shugaba Tinubu da 'Juyin Mulki'
- Babban lauya kan kundin tsarin mulkin kasa, Mike Ozekhome (SAN), ya yi suka kan yadda gwamnati ta ayyana dokar ta-baci a Ribas
- Ozekhome (SAN) ya bayyana dakatar da gwamna Siminalayi Fubara da ‘yan majalisar jihar a matsayin 'juyin mulki' na farar hula
- Masanin shari'ar ya bayyana cewa dakatar da gwamnati a jihar Ribas ya sabawa sashe na 305 na kundin tsarin mulki na shekarar 1999
- Dokar ta baci da dakatar da zababbiyar gwamnati ya jawo ce-ce-ku-ce da martani daga manya a bangarori daban-daban na Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos - Babban lauya kan kundin tsarin mulkin kasa, Mike Ozekhome (SAN), ya yi suka kan ayyana dokar ta-baci a jihar Ribas.
Lauyan ya bayyana dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa da wasu ‘yan majalisar jihar a matsayin 'juyin mulki' na farar hula.

Asali: Facebook
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a Ribas tare da naɗa tsohon Hafsan sojan ruwa, Vice Admiral Ibok-Ette Ibas mai ritaya ya kuda harkokin jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lauya ya caccaki shugaba Bola Tinubu
Nigerian Tribune ta wallafa cewa Ozekhome ya ce dakatar da gwamnati ta hanyar cire gwamna, da dukkanin ‘yan majalisar jihar ya saba wa kundin tsarin mulkin kasa.
Ya kuma jaddada cewa rarraba kudin jihar daga asusun tarayya zuwa shugaban riko na jihar ya saba wa hukuncin kotun koli.
Ribas: An fadi dokar da Tinubu ya karya
Ozekhome SAN ya yi bayani cewa kundin tsarin mulkin 1999 da aka yi wa kwakwarima ya bayyana karara cewa sashe na 305 ne kawai ke bai wa Shugaban kasa ikon ayyana dokar ta-baci.
Ya ce dokar ba ta ba da damar cire ko dakatar da gwamna ko sauran wakilan da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya ba.
Babban lauyan ya jaddada cewa sashe na 11(4) na kundin tsarin mulkin kasar ya hana ma majalisar dokoki ta kasa ikon tsige gwamna a lokacin dokar ta-baci.

Asali: Instagram
Ozekhome ya ce:
"Ba za a amince da rushe hukumomin da aka zaba ba tare da nada wanda zai karbi kudin jihar Ribas da suka zo daga asusun tarayya, lamarin da ya saba wa sashe na 162 na kundin tsarin mulki da kuma hukuncin kotun koli da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce yana mutunta wa."
An gargadi Tinubu kan batun Ribas
A baya, mun wallafa cewa tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya fusata da matakin da shugaba Bola Tinubu ya dauka na dakatar da zababbun jami’an gwamnati a Jihar Ribas.
El-Rufa’i ya ce matakin na Tinubu na sabawa kundin tsarin mulki, ya bayyana cewa dakatar da gwamna da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya wani barazana ce ga dimukuradiyya.
Tsohon gwamnan ya ce dokar Najeriya ba ta bai wa Shugaban kasa ikon cire zababbun jami’ai a matakin jiha ba, domin wannan na rage karfin tsarin dimokuradiyya da aka gina a kasar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng