El Rufai Ya Sake Bankado Babban Lamari, Ya Zargi Gwamna Uba da 'Satar' Kuɗin Kaduna

El Rufai Ya Sake Bankado Babban Lamari, Ya Zargi Gwamna Uba da 'Satar' Kuɗin Kaduna

  • Mallam Nasiru El-Rufai ya ɗauko batun yadda kuɗin kananan hukumomin Kaduna ke ɓata a mulkin Sanata Uba Sani
  • Tsohon gwamnan ya yi zargin cewa Uba Sani na canza kuɗin kananan hukumomi zuwa Dalar Amurka, ya sayi kadarori da su
  • El-Rufai ya ce yana da cikakkun bayanan yadda ake karkatar da kudin Kaduna da ma sunayen masu hulɗa da ƴan canji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya zargi magajinsa, Sanata Uba Sani, da karkatar da kuɗin kananan hukumomi.

El-Rufai ya zargi Gwamna Uba Sani da amfani da kuɗin ƙananan hukumomi wajen sayen kadarori a ƙasashen Seychelles, Afirka ta Kudu, da Birtaniya.

El-Rufai da Uba Sani.
El-Rufai ya zargi Uba Sani da karkatar da kuɗin kananan hukumomi a jihar Kaduna Hoto: Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan ya jefi Malam Uba Sani da wannan zargi ne a wata hira da ya yi da gidan radiyo Freedom na Kaduna wanda aka wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya rama miyagun maganganu da El Rufa'i ya fada masa a baya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

El-Rufai ya taso Gwamna Uba Sani a gaba

Nasir El-Rufai, wanda kwanan nan ya sauya sheƙa daga APC zuwa SDP, ya ce gwamnan na canza kuɗin kananan hukumomi zuwa dala don sayen kadarori a ƙasashen waje.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa lokacin mulkinsa bai taba karɓar ko sisin kwabo daga kuɗin kananan hukumomi ba.

“Lokacin da nake gwamna, ba na tabawa kananan hukumomi kuɗinsu. Idan an cire kudaden SUBEB, kiwon lafiyar matakin farko, da wasu muhimman abubuwa, ana ba su sauran kudinsu gaba ɗaya.”

'Uba Sani ke wawure kudin kananan hukumomi'

El-Rufai ya yi zargin cewa gwamnatin Uba Sani tana wawure kuɗin kananan hukumomi kuma hukumomin yaƙi da cin hanci na ƙasa sun gaza ɗaukar mataki.

Ya ce a halin yanzu babu wata ƙaramar hukuma a Kaduna da ke karɓar fiye da Naira miliyan 50 a wata saboda an riƙa an wawure dukiyarsu.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan kasuwa sun yi zanga-zanga, sun tuna da yadda El-Rufa'i ya jawo masu matsala

"Yanzu haka maganar da nake da ku, babu ƙaramar hukumar da ke samun Naira miliyan 50 a wata. Da zaran an turo kason ƙananan hukumomi suke karkatar da su.
"Su canza su zuwa Dala, sannan su yi amfani da su wajen sayen kadarori a ƙasashe irinsu Seychelles, Afirka ta Kudu, Landan da wasu wurare.

- In ji El-Rufai.

A baya dai ya yi zargin cewa, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, shi ne ya shirya wannan aiki saboda burin zama shugaban kasa, zargin da ya musa.

Malam El-Rufai ya ƙara da cewa yana da bayanan yadda ake kwashe kuɗin, da kuma sunayen masu hulɗa da ‘yan canjin da ke juya kuɗin.

El-Rufai ya musanta karɓar cin hanci

Tsohon gwamnan ya ƙaryata duk wani zargi da ake masa na karɓar cin hanci daga ƴan kwangila a lokacin mulkinsa.

"Idan wani ɗan kwangila ya taba ba ni cin hanci, ya fito ya bayyana. Lokacin da hukumar ICPC ta gayyaci ƴan kwagilarmu, duk sun ce ba su taba haɗuwa da ni ba.”

Kara karanta wannan

Zargin El Rufai: Gwamna Uba Sani ya yi martani, ya fadi abin da ya sa a gaba

A ƙarshe, Nasir El-Rufai ya zargi Gwamna Uba Sani da karɓar kason 40% daga duk wata kwangila da zai bayar a jihar Kaduna.

"Uba yana ɗaukar takardun kwangila ya tafi Abuja, ya miƙa wa ƴan kwangila su ba shi kaso 40%, sun yi tunanin haka muka tafiyar da gwamnati, amma sun yi kuskure," in ji shi.

El-Rufai ya caccaki ƴan sandan Kaduna

A wani rahoton, kun ji cewa Mallam Nasir El-Rufai ya fusata da garƙame tsohon kwamishinansa a Kaduna, ya zargi ƴan sanda da zama yaran Uba Sani.

Tsohon gwamnan ya kuma yi zargin cewa ƴan sanda sun sace tsohon kwamishinan ne saboda kawai ya fice daga APC zuwa jam'iyyar SDP mai alamar doki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel