Fata Na Gari: Masana Sun Gano Hanyar da Za a Bi Man Fetur Ya Koma N500 Nan Kusa

Fata Na Gari: Masana Sun Gano Hanyar da Za a Bi Man Fetur Ya Koma N500 Nan Kusa

  • Masana na hangowa ‘yan Najeriya wani tagomashi yayin da manyan masu harkar man fetur ke yakin karya farashi a kasar
  • Ana sa ran man fetur zai iya sauka har zuwa N500 nan ba da jimawa idan aka samu dama guda biyu a fannin tattalin arziki
  • A halin yanzu, matatar man Dangote na ci gaba da karya farashin man fetur, wanda ke tilastawa NNPC yin hakan a gidajen man ta

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Najeriya - A yayin da ake ci gaba da fafatawa kan farashin man fetur tsakanin Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC) da Matatar Dangote, ‘yan kasuwa sun fara rage yawan sayen fetur saboda tsoron asarar kudade masu yawa.

Yakin karya farashin ya fara ne a watan Nuwamba 2024 lokacin da Matatar Dangote ta rage farashin fetur daga N990 zuwa N970 a kowace lita.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Dangote ya tsallake Najeriya, ya shigo da ɗanyen mai daga ƙasar waje

Daga bisani, kamfanin ya kara rage farashin zuwa N899 domin saukaka wa 'yan Najeriya yayin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.

Man fetur zai iya sauka zuwa N500 nan kusa
Akwai yiwuwar mai ya sauka nan kusa zuwa N500 | hOTO: Bloomberg/Contributor
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NNPC ta karya farashi bayan Dangote

NNPC ma ta bi sahu ta hanyar rage farashinta, kamar yadda Kungiyar Masu Gidajen Man Fetur ta Najeriya (PETROAN) ta tabbatar.

A ranar 1 ga Fabrairu, 2025, Matatar Dangote mai karfin tace ganga 650,000 a kowace rana ta rage farashin fetur zuwa N890. Sai daga baya ta sake ragewa zuwa N825.

A ranar 3 ga Maris, 2025, wasu tashoshin sayar da man NNPC sun sanar da rage farashin zuwa N860, daidai da sabon farashin Dangote.

Asarar da 'yan kasuwa ke fuskanta

Masana sun bayyana cewa wannan sauyin farashi ya amfanar da ‘yan Najeriya, amma ya haddasa asarar kusan N2.5 biliyan a kowace rana, wanda ke iya kaiwa N75 biliyan a kowane wata ga ‘yan kasuwa da masu shigo da fetur.

PETROAN ta nemi hukumomi su tsara yadda za a daidaita farashin man fetur sau biyu a shekara, don hana irin wannan matsala.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Shugaban Amurka, Trump ya samu izinin kakaba takunkumi ga Najeriya

Mataimakin Shugaban Kungiyar ‘Yan Kasuwar Man Fetur ta Najeriya (IPMAN), Hammed Fashola, ya ce wannan yakin rage farashi yana haifar da asara mai yawa ga ‘yan kasuwa.

Mafitar da IPMAN ta daukarwa kanta

Ya bayyana cewa rage yawan sayen fetur shine kawai mafita domin gujewa asara idan farashin ya sake sauka.

Matatar Dangote ta sake rage farashinta daga N825 zuwa N815, bayan faduwar kudin shigo da fetur zuwa N774.82 a kowace lita.

Kungiyar Manyan Masu Sayar da Man Fetur (MEMAN) ta bayyana cewa farashin shigo da man fetur ya sauka daga N927.48 a ranar 21 ga Fabrairu, 2025, zuwa N774.82.

Hakan na faruwa ne sakamakon saukar farashin danyen mai a duniya, inda farashin Brent crude ya sauka zuwa $70 kowace ganga, yayin da US Western Intermediate (WTI) ya sauka zuwa $66.70.

Ta yiwuwa farashin fetur ya kai N500

Fashola ya yi hasashen cewa farashin fetur na iya sauka zuwa N500 a kowace lita idan farashin danyen mai ya sauka zuwa $40 kowace ganga kuma darajar Naira ta karu ƙasa da N1,000 kan dala.

Kara karanta wannan

Sauƙi ya samu: Dangote ya ƙara sauke farashin man fetur daga N825

Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta ce adadin shigo da man fetur ya kai na N15.42 tiriliyan a shekarar 2024, wanda ke nuna karuwar kashi 105%.

Masana sun nuna damuwa kan wannan yanayi duk da karuwar ƙarfin tace mai a Najeriya.

Mataimakin Shugaban IPMAN ya ce shigo da man fetur zai karya tsarin handame kasuwa guda kuma zai rage farashin kayayyaki a bangaren man fetur.

Najeriya ta fi Saudiyya kashe kudin hako mai

A wani labarin, kun ji yadda aka hango cewa, kasar Saudiyya bata kai Najeriya kashe kudi ba wajen hako danyen mai.

Wannan ya samo asali ne daga yanayin kayan aikin da Saudiyya ke da shi da kuma yadda Najeriya ke fuskantar kalubale.

A bangare guda, hukumomin Najeriya sun bayyana damuwa kan yadda za su sayar da man fetur a kasuwannin duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

iiq_pixel