Gwamna Ya Tausayawa Ma'aikata, Ya Masu Garaɓasa a Wurin Aiki saboda Azumin Ramadan
- Gwamnan Kebbi, Nasir Idris ya amince da rage awannin aiki ga ma'aikata domin su samu lokacin ibada da neman kusanci da Allah a Ramadan
- Daga nan zuwa karshen azumin bana, ma'aikata za su fara aiki daga ƙarfe 8:00 na safe zuwa 1:00 na rana a ranakun Litinin zuwa Alhamis
- Ma'aikatan gwamnatin Kebbi za su koma tashi daga aiki karfe 12:00 na rana a kowace Juma'a, wannan garabasa za ta kare a karshen Ramadan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kebbi - Gwamnan Kebbi, Nasir Idris, ya rage lokutan aiki ga ma’aikatan jihar domin sauƙaƙa musu su samu damar ibada a watan azumin Ramadan.
Wannan mataki yana daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na bai wa ma’aikata damar gudanar da ayyukan su cikin sauƙi tare da samun isasshen lokaci don yin ibada.

Asali: Facebook
Kwamishinan ma’aikata, fansho da bayar da horo, Auwal Manu Dogondaji, ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Birnin Kebbi a madadin gwamnan, rahoton Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kebbi: Lokutan aiki a watan Ramadan
Ya ce daga yanzu, ma’aikata za su fara aiki daga karfe 8:00 na safe zuwa 1:00 na rana daga Litinin zuwa Alhamis, yayin da a ranar Juma’a za su yi aiki daga karfe 8:00 na safe zuwa 12:00 na rana.
Auwal Dogondaji ya ce wannan mataki ya dace da Ramadan, inda Musulmi ke bukatar samun lokacin zuwa wurin tafsiri, sallah da sauran ayyukan ibada.
"Gwamnati ta fahimci yadda ma'aikata ke bukatar lokacin yin ibada a Ramadan, don haka wannan mataki zai ba ma’aikata damar yin aiki tare da yin ibada cikin sauƙi," in ji shi.
Ya ƙara da cewa wannan sauyin lokaci na aiki zai ci gaba har zuwa ƙarshen watan Ramadan, daga nan ma’aikata za su koma tsarin aikin da aka saba.
Gwamnatin Kebbi ta buƙaci addu'a
Kwamishinan ya bukaci ma’aikatan da su yi amfani da wannan damar wajen ƙara kusanci da Allah ta hanyar ibada, addu’o’i da taimakon marasa ƙarfi.
Ya kuma bukaci al’ummar Kebbi su yi addu’a domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar da Najeriya baki ɗaya.
Wannan mataki ya samu karɓuwa daga ma’aikatan, musamman Musulmi, wadanda suka bayyana jin daɗinsu da irin wannan sauƙin da gwamnati ta ba su.
Wasu daga cikin ma'aikatan sun bayyana cewa matakin zai rage gajiya da wahalar aiki, tare da ba su damar gudanar da azumi cikin kwanciyar hankali.
A ƙarshe, Auwal Dogondaji ya jaddada cewa gwamnatin Kebbi za ta ci gaba da ɗaukar matakan da za su taimaka wa jama'a wajen samun kyakkyawan yanayi na rayuwa, musamman a lokutan ibada.
"Allah ya saka wa mai girma gwamna da alheri, ya duba mana kuma na san ma'aikata za su ji daɗin hakan a wannan wala mai albarka," in ji wani ma'aikacin gwamnatin Kebbi.
Mutumin wanda ya bayyana sunansa da Kabir Alhassan ya yabi Gwanna Nasir yayin da yake tattaunawa da wakilin Legit Hausa ta wayar tarho.
A cewarsa, Ramadan wata ne da je bukatar mutum ya ajiye abubuwa da dama ya koma ga Allah, ya ayi addu'ar Allah ya haɗa kowa da alkairan wannan wata.
Gwamna ya rage lokacin aiki a Jigawa
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Jigawa ya rage wa ma’aikatan gwamnati lokutan aiki domin saukaka musu yayin azumin watan Ramadan.
Shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar, Muhammad Kandira Dagaceri, ya bayyana cewa rage lokutan aiki zai fara aiki nan take.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng