Sanata Natasha Ta Dauki Sabon Mataki kan Zargin Lalata da Take Yi Wa Akpabio

Sanata Natasha Ta Dauki Sabon Mataki kan Zargin Lalata da Take Yi Wa Akpabio

  • Sanata Natasha Akpoti ta tsaya kan bakanta a zargin da take yi wa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, kan ci mata zarafi
  • Natasha Akpoti wacce ke wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta sake gabatar da ƙorafi kan Godswill Akpabio a zaman majalisar na ranar Alhamis
  • Sake gabatar da ƙorafin na zuwa ne bayan an yi watsi da wanda ta miƙa a ranar Laraba, saboda ya saɓa ƙa'idar majalisar tarayya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Sanata mai wakiltar mazaɓar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta sake miƙa ƙorafi kan Godswill Akpabio.

Sanata Natasha ta sake gabatar da ƙorafin ne kan zargin cin zarafin da take yi ga shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.

Natasha ta shigar da korafi kan Akpabio
Sanata Natasha ta sake shigar da korafi kan Godswill Akpabio Hoto: @NGRSenate
Asali: Twitter

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa shugabar kwamitin majalisar dattawa kan mazauna ƙasashen waje da ƙungiyoyi masu zaman kansu, ta sake miƙa ƙorafin ne a zaman majalisar na ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Zargin lalata: Akpabio ya tono abin da ya faru a daren auren Sanata Natasha

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Natasha ta sake miƙa ƙorafi kan Akpabio

Sanata Natasha ta sake miƙa ƙorafin ne bayan da aka yi watsi da ƙorafinta na farko da ta gabatarwa kwamitin ladabtarwa, ɗa'a da ƙorafe-ƙorafe na majalisar dattawa.

Yayin gabatar da ƙorafin, Sanata Natasha ta bayyana cewa al’ummar mazaɓarta ne suka shigar da shi, ƙarƙashin jagorancin wani mai suna Zubairu Yakubu.

Bayan gabatarwar, shugaban majalisar Dattawa Akpabio ya tambayi ko akwai wani ƙalubale na shari’a da zai hana karɓar ƙorafin, sai Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta ce babu wata matsala.

Daga nan ne shugaban majalisar ya umurce ta da ta gabatar da ƙorafin a hukumance.

Daga nan an miƙa ƙorafin zuwa ga kwamitin ladabtarwa ƙarƙashin jagorancin Sanata Neda Imasuen, inda aka umarce su da bayar da rahoto a cikin makonni huɗu.

Ƙorafin Natasha kan Akpabio ya tayar da ƙura

Idan ba a manta ba dai Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta gabatar da ƙorafi kan zargin cin zarafi da ta yi a kan Akpabio a zaman majalisa na ranar Laraba, lamarin da ya janyo cece-kuce.

Kara karanta wannan

Zargin Shugaban Majalisa da neman lalata da matar aure ya riƙide, an samu wasiƙa daga Kogi

Babban mai tsawatarwa na majalisar dattawa, Sanata Mohammed Monguno (APC, Arewa ta Borno), ya nuna cewa ƙorafin bai biyo ta hanyar da ta dace ba.

Ya bayyana cewa majalisar ba za ta iya sauraro ko tura ƙorafin ga kwamitin ladabtarwa ba, domin kuwa yana da nasaba da shari’a da ke gudana tsakanin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da matar shugaban majalisa, Ekaette Akpabio.

Sanata Monguno ya ƙara da cewa ba za a iya duba ƙorafin ba, Saboda Sanata Natasha ce da kanta ta sanya hannu a kai.

Saboda haka, kwamitin ladabtarwa na majalisar dattawa ya yi watsi da ƙorafin.

Wannan sabon ƙorafin ya ƙara dagula al'amura tsakanin Sanata Natasha da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.

Majalisar dattawa za ta hukunta Sanata Natasha

A wani labarin kuma, kun ji cewa kwamitin majalisar dattawa na ladabtarwa da ɗa'a ya ba da shawarar a hukunta Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kan zargin da take yi wa Godswill Akpabio.

Kara karanta wannan

Natasha: 'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga zanga, sun harba barkonon tsohuwa

Kwamitin ƙarƙashin jagorancin Sanatan Nada Imaseun ya ba da shawarar majalisar ta dakatar da Natasha har na tsawon watanni shida.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng