Gwamna Ya Daina Ɓoye Ɓoye, Ya Jero Mutanen da Ke Jefa Matasa Harkar Ƴan Bindiga
- Gwamna Charles Soludo na jihar Anambra ya gano yadda bokaye da malaman tsibbu ke yaudarar matasa suna shiga harkokin laifi
- Soludo ya ce gwamnatinsa ta ɗauki matakan shawo kan wannan matsala kuma tuni ta fara bincike kan bokaye da irin waɗannan malamai
- Cikin laifukan da bokayen ke yaudarar matasa su fara har da safarar miyagun kwayoyi da shiga kungiyoyin ƴan bindiga da garkuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Anambra - Gwamnan Jihar Anambra, Charles Soludo, ya caccaki bokaye da malaman tsibbu da ke yaudarar matasa da alkawarin kariya ta sihiri wajen aikata laifuka.
Gwamna Soludo ya ce bokaye ke yaudarar matasa su jefa su cikin aikata miyagun laifuka irin su safarar miyagun kwayoyi, damfarar yanar gizo da garkuwa da mutane.

Source: Facebook
Farfesa Soludo ya fallasa wannan sirrin ne a wata hira da manema labarai a Awka, babban birnin jihar Anambra, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Zargin lalata: Sanata Natasha na tsaka mai wuya, Hadimin Osinbajo ya tona shirin majalisa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda bokaye ke yaudarar matasa
Soludo ya bayyana cewa bokaye na yin mummunan tasiri a rayuwar matasa, suke ba su tabbacin cewa za su tsira daga doka ta hanyar amfani da asiri da layu.
Ya ce hakan ya jefa dubban matasan Najeriya cikin mawuyacin hali, yayin da da-dama ke fuskantar dauri a gidajen yari na kasashen waje.
Gwamna Soludo ya ce:
“Ana yi wa matasa asirin Oke-Ite don yaudararsu cewa za su iya wuce wuraren bincike ba tare da an gano su da miyagun kwayoyi ba.
"Amma da zarar an kama su, sai su kare a gidan yari. Idan hakan ya kasa, sai su juya zuwa damfara ta yanar gizo, idan hakan ma bai yi nasara ba, sai su fada harkar ƴan bindiga/garkuwa da mutane domin samun kudi cikin sauki."
Wasu matakai Gwamna Soludo ya ɗauka
Gwamna Soludo ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta fara ɗaukar matakan tsaftace Anambra daga irin wadannan miyagun ayyuka na bokaye da malaman tsibbu.
Ya ce a halin yanzu an fara gudanar da bincike kan bokaye da wasu malamai fiye da 30 da ake zargi da hannu a aikata miyagun laifuka.
Ya kara da cewa, tun bayan fara wannan bincike, da dama daga cikin bokayen sun tsere daga jihar, yayin da wasu ke fargabar cewa sihirinsu zai daina aiki saboda kama shugabanninsu.
Gwamnatin Anambra ta fara gano abubuwa
Gwamnan ya ce an kwato tukwane da dama na Oke-Ite kuma za a yi musu gwajin binciken kimiyya.
Ya ce idan aka gano cewa akwai jinin dan Adam a cikin wadannan tukwane, masu su za su fuskanci hukunci mai tsanani.

Source: Facebook
Soludo ya jaddada cewa burinsa shi ne ya mayar da Anambra cibiyar kasuwanci da masana’antu, inda mutane za su iya rayuwa cikin kwanciyar hankali.
Ya bukaci kowa, ba tare da la’akari da kabila ko addini ba, da ya hada hannu da gwamnatinsa don tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jihar.
Gwamnatin Anambra ta rusa otal
Ku na da labarin cewa gwamnatin jihar Anambra karkashin Gwamna Soludo ta rusa wani otel wanda aka bayyana a matsayin maboyar masu garkuwa da mutane.
Rahotanni sun nuna cewa an gano kaburbura sama da 30 da aka tsara a wani sashe na ginin, tare da wajen tsafi da ake amfani da shi wajen aikata miyagun ayyuka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

