Zargin Neman Lalata Ya Ƙara Girma, Sanata Natasha Ta Gabatar da Takarda a Majalisa

Zargin Neman Lalata Ya Ƙara Girma, Sanata Natasha Ta Gabatar da Takarda a Majalisa

  • A ƙarshe Natasha Akpoti-Uduaghan ta miƙa ƙorafinta a hukumance kan zargin shugaban Majalisar Dattawa da neman lalata da ita
  • Sanata Natasha ta halarci zaman Majalisar yau Laraba tare da mijinta, kuma ta miƙa takardar ƙorafinta domin yin abin da ya dace
  • Wannan batu dai ya tayar da ƙura, tuni mutane suka nemi Akpabio ya yi murabus domin gudanar da bincike na gaskiya da adalci

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Sanata mai wakiltar yankin Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta gabatar da ƙorafinta a hukumance a gaban Majalisar Dattawa.

Sanata Natasha ta miƙa takardar ƙorafi ne kan zargin cin zarafi da neman lalata da ita da take yi wa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio.

Natasha da Akpabio.
Sanata Natasha ta mika korafi ga Majalisar Dattawa kan zargin da take wa Akpabio Hoto: @NGRSenate
Asali: Twitter

A zaman majalisar na ranar Laraba, 5 ga watan Maris, 2025, Sanata Akpoti-Uduaghan ta miƙa ƙorafinta ƙarƙashin dokar Majalisa ta 40, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Daga ƙarshe, an ji ta bakin shugaban Majalisa kan zargin neman lalata da Sanata Natasha

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Natasha ta bayyana cewa ta riga ta yi magana a wani shirin talabijin na Arise News kan batun cin zarafi da take zargin Akpabio da aikatawa ta hanyar neman lalata da ita.

Sanata Natasha ta miƙa ƙorafi ga Majalisa

A yayin da yake jagorantar zaman, Sanata Akpabio ya bai wa Sanata Natasha damar gabatar da ƙorafinta a gaban majalisar dattawan kuma ta yi hakan nan take.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godwills Akpabio wanda ake zargi da aikata laifin, shi ne ya jagoranci zaman majalisar na yau Laraba a Abuja, Channels tv ta kawo.

Wannan al'amari dai ya tayar da ƙura a siyasar Najeriya tun da Sanata Natasha ta fito fili ta yi ikirarin cewa Akpabio ya neme ta da lalata amma a cewarta ba ta amince ba.

An nemi Akpabio ya yi murabus

Manyan mutane da ƴan siyasa a kasar nan sun tofa albarkacin bakinsu kan wannan zargi, inda wasu ke ganin ya kamata a gudanar da bincike mai zurfi.

Kara karanta wannan

Natasha: 'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga zanga, sun harba barkonon tsohuwa

Wasu kuma na ganin ya kamata Akpabio ya yi murabus daga shugabancin Majalisar Dattawa domin ba da damar bincike cikin gaskiya da adalci.

Tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki na ɗaya daga cikin waɗanda ke ganin ya kamata Akpabio ya ajiye muƙaminsa.

Godwill Akpabio.
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya karɓi korafin Natasha Hoto: @NGRSenate
Asali: Facebook

Da take martani kan zargin, Majalisar Dattawa ta ce ba za ta binciki Akpabio ba saboda har yanzu babu wanda ya shigar da ƙorafe a gabanta a hukumance.

Hakan ya a sa a zaman yau Laraba, Natasha wacce ta halarci zama tare da mijinta ta miƙa takardar korafi kuma shugaban Majalisar ya amsa da kansa nan take.

Wane mataki majalisar za ta ɗauka?

Idan har majalisar ta amince da gudanar da bincike, wannan na iya zama babban lamari da ka iya shafar mutuncin Akpabio da matsayinsa a siyasance.

Duk da haka, har yanzu babu wata takamaiman hujja da aka bayyana a bainar jama’a da ke tabbatar da sahihancin zargin.

Kara karanta wannan

Neman lalata: Majalisa ta yi watsi da bukatar Natasha kan zargin Akpabio

Zanga-zanga ta ɓarke a Majalisa

A ɗazu, mun kawo maku cewa magoya bayan Sanata Natasha sun ɓarke da zanga-zangar lumana a zauren Majalisar Dattawa.

Masu zanga-zangar da suka haɗa da mata da maza sun buƙaci shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya yi murabus daga muƙaminsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262